Sakonnin Masu Karatu (2016) (17)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

102

Assalamu alaikum, yaya aka ji da kokari? Ni ma a taimaka mini da bayani kan Tsibirin Bamuda da yadda zan yi anfani da password wajen kare wasu aiyukana daga miyagu. Nagode.  Muhammad Bala: muhammadbala456@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Ka duba akwatin Imel dinka, na aika maka abin da ya sawwaka.  Allah amfanar damu baki daya, amin.


Assalamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kana Lafiya. Don Allah ina so ka fada mini shekarun “Farfesa Tim Bernes-Lee” Wato Baban Internet. Muhammad Izzuddin: izzuddin0814@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Shekarun “Baban Intanet” dai a halin yanzu sun kai 61.  Domin an haife shi ne a ranar 8 ga watan Yuni, shekarar 1955.  Da fatan ka gamsu.


Assalama alaikum, don Allah Baban Sadik, ina so in san su wa ke da alhakin mallakar fasahar Intanet?  Sannan, sai sun ba da umarni ne ake bude shafin yanar sadarwa (website)?   Shin, idan sun ga dama suna iya rufe maka shafin yanar sadarwarka ne bisa wani dalili, kuma suna karbar haraji ne a gurin masu shafukar yanar sadarwa?  Allah yasa ka fuskanci tambayata, ya kuma baka ikon amsa min.  Na gode. Allah ya kara basira amin. Musa Ibrahim Gala: musaibrahimgala1@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Babu wata kasa da ta mallaki Intanet gaba dayansa a halin yanzu.  Duk da cewa fasahar ta samo asali ne daga kasar Amurka, amma a halin yanzu ta yadu ko ina a duniya.  Babu wata kasa da za ta iya kulle ta gaba daya ta hana kowa amfana da ita.  Amma kowace kasa na iya hana wani bangare na Intanet daga isa na’urorin mutanen kasar.  Misali, kasar Saudiyya ta killace wasu shafuka na Intanet da suka danganci kasar Isra’ila, da dukkan shafukan batsa; ko da ka nemo wadannan shafuka a kasar baza ka same su ba.  Wannan shi ake kira “Cyber Censorship.”

Na biyu, ba wata kasa dake bayar da umarni kafin a bude wani shafin yanar sadarwa.  Daga kwaryar dakinka kana iya zama ka gina shafinka na Intanet, in har za ka iya, sannan ka biya kudin hidimar adana maka shi ga kamfanonin da ke wannan aiki, tare da yin rajistar suna ko adireshin gidan yanar, duk ba matsala.  Babu wata kasa da sai an nemi izninta ake iya wadannan abubuwa.

Dangane da rufe maka shafi, ya danganci kamfanin dake adana maka shafinka.  Misali, akwai wasu shafuka masu dauke da bayanan da kasar Amurka ta haramta yada su, wannan yasa hukumar kasa ta rufe shafukan, ta hanyar tirsasa kamfanin da ke lura wa masu shafin da bayanansu, wato: “Web Hosting Company” kenan.  Wannan ya faru ne saboda kamfanin da ke dauke da shafin yana kasar Amurka ne.  Amma da ace kamfanin na kasar Rasha ne, sai dai kasar Amurka ta toshe adireshin shafin kadai, amma ba za ta iya hana wadanda ke wasu kasashen isa ga shafin ba.

Dangane da batun biyan haraji, babu wata kasa da ake biyanta haraji don bude shafin Intanet.  Sai dai harajin cinikayya da kamfanoni ke biyan hukumomi, wannan kuma bai takaitu gare su kadai ba.  Kudaden da za ka rika biya su ne kudin rajista na adireshin shafinka, da kuma kudin lura maka da shafi, wanda ta sanadiyyar haka ne ake iya neman shafinka a Intanet har a samu isa gare shi.  Wadannan kudaden kuma za ka rika biyan kamfanin dake maka hidimar ne, ba wata kasa ba.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Salamu Alaikum, Baban Sadik, ya aiki?  Da fatan kana cikin koshin lafia, Allah yasa haka amin.   Don Allah Baban Sadik wai mutum zai iya saukar da babbar manhajar “Linux” akan babbar manhajar “Window”?  Kuma zai iya amfani da wannan babbar manhaja a kan kowace irin kwamfuta, ko kuma akwai kwamfutar da baza ta iya dauka ba?  Mungode da ka bamu damar aiko maka da tambayoyinmu kuma kana amsa mana, Allah ya karama daukaka da basira. Shamsuddeen Kabir: shamsudeenkabir92@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Tabbas idan kana bukata za ka iya saukar da babbar manhajar kwamfuta nau’in Linux, har ma ka dora wa kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Windows.  Wannan abu ne mai yiwuwa, kuma shi ake kira: “Dual Booting” a ilimin kwamfuta na zamani.  Sai dai kuma, dole ne ka tanada wa babbar manhajar Linixu din wuri na musamman, ba wai a bangaren da babbar manhajar Windows take ita ma nan za ka jibga ta ba.  Hakan bazai yiwu ba.  Misali, idan kwamfutarka mai dauke da babbar manhajar Windows na dauke da mizanin da ya kai 500GB, kana iya yanke kamar 150GB ka dora babbar manhajar Linux a kai.  Wannan tsari na yanko wani bangaren babbar ma’adanar kwamfuta shi ake kira: “Partitioning.”  Don haka, idan kwamfutarka ba ta da isasshen ma’adana, to, yin haka zai kuntata mata.  Don haka, sai ka yi la’kari da yanayin girman mizanin kwamfutar taka tukun.

Kwamfutar da ba ta da isasshen ma’adana a babbar ma’adanarta (Hard Drive), da wacce ba ta isasshen ma’adanar wucin-gadi (RAM), da wacce kuma kwazon sarrafa umarninta mai rauni ne (wato: Processor), duk ya kamata a guje wa dora musu kaya mai yawa.  Domin yin hakan na iya hana su gudanar da ayyuka yadda ya kamata.  Kai kanka baza ka ji dadin amfani da ita a wannan yanayi.  Wannan kadan ne daga cikin abin da zan iya cewa a halin yanzu.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu Alaikum Baban Sadik don Allah ka min karin bayani a kan yadda ake kirkirar maudu’i a shafin twitter wato “hashtag#”, kuma ta yaya mutum zai iya gane wanda ya kirkiri maudu’in? Sannan ta yaya ake tantance shafukan sada zumanta irin su Facebook da Twitter, wato verified?  Nagode.  Daga Bello Isiyaku: ishiyakubello@gmail.com 

Wa alaikumu s salam Malam Bello, barka dai.  Kirkirar hashtag ba wani abu bane mai wahala.  Idan kana da wani sako dake dauke da wata manufa da kake son yadawa nan take a Twitter misali, sai ka rubuta sakon, sannan ka tsara kalmomi ko haruffan da kake son su wakilci wannan sako, ko dai a farkon sakon, ko kuma a karshen sakon.  Ga misali: “Wajibi ne kowa ya dage wajen tarbiyyar ‘ya’yansa.  Bamu yarda da sakakkiyar ‘yanci ga yara da nufin gata ba. #TarbiyyaWajibi”.  Ka ga sakon da na rubuta mai dauke da manufata, kan tarbiyya ne, da nuna inkari ga masu baiwa ‘ya’yansu sakakkiyar ‘yanci a rayuwarsu da sunan gata.  Amma a dunkule, ina nuna dole ne iyaye su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu.  Shi yasa na sanya taken hashtag dina: #TarbiyyaWajibi.

Kana iya rubuta sakon da kowane harshe cikin harsunan duniya da ka nakalta.  Amma dole ne ya zama wadanda kake son su fahimci sakon suna jin harshen.  Da zarar ka rubuta ka aika, duk wadanda suke abota da kai za su gani.  Da zarar su ma sun dauki sakon (“retweet,” kamar “share” kenan a Facebook), zai kai ga abokansu, su ma daga can idan suka dauka, haka abin zai ta yaduwa.

Dangane da tambayarka ta biyu kuma, gane asalin wanda ya kulla hashtag abu ne mai wahala ainun.  Domin masu dandalin Tweeter basu samar da wani tsari na musamman da za a iya amfani da ita, ta hanyar tambaya (Search) ko nemo wanda ya assasa hashtag din ba, a farkon lamari.  Sai dai nan gaba in shafin bai rufe ba, ta yiwu cikin tsare-tsaren da suke samarwa lokaci zuwa lokaci, za su tsara wata hanya don yin hakan.

Tambayarka ta karshe kan batun tantance shafin mai shafi a Facebook, wato: “Verified Pages,” tsari ne da masu shafin Facebook ke aiwatar dashi, don nuna ingancin shafin da mai shafin.  Ma’ana, idan ka shiga shafin wani gwarzo ko wani kamfanin kasuwanci a Facebook, kaci karo da wata alama shudiya da maki fari a kanta, wannan na nuna cewa wannan shafi ne ingantacce, ba na bogi ba.  Sun samar da wannan tsari don tabbatar da natsuwa a zukatan masu son aiwatar da saye da sayarwa a dandalin Facebook ta hanyar shafukan kasuwanci dake da rajista a dandalin.  Ganin cewa shafukan bogi sun yawaita sosai, idan ba haka suka yi ba, to, kamfanonin dake basu tallace-tallace zasu ragu, ko ma a rasa gaba daya.  Domin jama’a baza su amintu da abin da suke tallatawa ba, tunda babu tabbacin ingancin shafin.

Samun hukumar Facebook su tantance shafinka a matsayin shafi ingantacce (Verified Page) abu ne mai sauki.  Sai dai ba kowace nahiya daga cikin nahiyoyin duniya suka tanada wa wannan tsari ba.  Mu a nan Afirka ba mu cikin wadanda za su iya neman hukumar Facebook su tantance mana shafukanmu.  Don haka ma ko kaje shafin da ake aika wannan bukata baza ka ga alamar da za ka yi amfani da ita wajen aika bukatarka ba.  Sun yi haka ne ganin cewa kamfanoni da shahararrun mutanen dake da shafuka dasu galibi suna kasashe mawadata ne.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.