Sakonnin Masu Karatu (2019) (17)

Tasirin Turakun Sabis Ga Lafiyar Jama'a

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 25 ga watan Oktoba, 2019.

53

Assalamu alaikum babban malamina Baban Sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya kuma Allah yasa anyi sallah lafiya, amin.  Shin da gaske ne kafa turakun sabis (GSM Mast) kusa da jama’a yana illa ga lafiyar xan adam? Musamman ma Radiation. Daga Saminu Artillery Yelwa Shendam Jihar Filato, 08032436477, Imail: saminuartillery1@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Saminu Artillery.  Wannan tambaya taka mun sha amsa tambayoyi makamantanta ko ma irinta, a baya – musamman a shekarun 2013 da 2016.  Malam Ali Fancy yayi irin wannan tambaya a 2013, sai Malam Nasiru Kainuwa Hadeja da yayi tambaya kan tabbacin ko sinadaran da wayoyi salula ke fitarwa yayi amsa kira na haddasa cutar sankara (Cancer), a shekarar 2016.  Wadannan tambayoyi duk na amsa su ta hanyar bincike mai zurfi kuma a takaice.  Ga amsa tambayar da na bayar kan tasirin turakun sabis na kamfanonin wayar salula nan:

Wadannan cibiyoyi masu taimaka wa kamfanonin sadarwa yada tsarin sadarwar kamfanin wayarsu sun kasu kashi biyu ne; akwai na farko, wadda ke janyo tsarin sadarwar, wadda ke yada maganadisun sadarwar rediyo, wato “Rabio Waves.”  Wannan nau’i shi ne wanda aka ce yana taimakawa wajen yada cutar sankara (Cancer), saboda maganadisun lankarki na rediyo da yake bazawa a muhallin da yake, wato “Electromagnetic Radiation.”  Ire-iren wadannan galibi ba a dirke su a cikin unguwa ko gari ko maraya, sai dai a bayan gari, ko a saman tsaunuka, kusa da unguwa ko gari ko mahallin da ake so su samu wannan tsarin sadarwa na wayar salula. Wannan yasa ba a ajiye shi a kusa da jama’a.  Kuma aikin hukumar sadarwar kowace kasa ne ta rika lura da inda kamfanonin sadarwar wayar salula ke ajiye ire-iren wadannan cibiyoyi. Shi yasa ma yana daga cikin ka’ida, dole sai da wani jami’in Hukumar Sadarwa ta Kasa (kamar National Communication Commission, a Najeriya misali) kafin a dirke cibiyar a ko ina ne.

Na biyun kuma shi ne wanda aikinsa bai wuce yadawa ko baza wannan tsarin sadarwa, don hana shi cushewa a vangare daya. A wasu lokuta a unguwa ko gari, za ka ga wani vangare ya fi wani vangaren garin daidaituwan tsarin sadarwa. Idan haka ta kasance, alama ce da ke nuna cewa akwai matsalar cushewar tsarin sadarwa a wani vangaren garin ko unguwar.  Irin wannan cibiyar sadarwar ita ce za ka gani a girke a unguwanni misali.  Shi wannan, a cewar masana, ba ya haddasa wata matsala ga lafiyar mazauna wannan wuri.  Domin aikinsa shi ne yadawa ko baza tsarin sadarwar, ba wai ya janyo shi ta amfani da sinadaran maganadisun lantarki ba.  Shi yasa suke kiransa “Cell Signal Booster.”  Da fatan ka gamsu.

Dangane da abin da ya shafi alakar dake tsakanin sinadaran maganadisun lantarki da wayar salula ke fitarwa yayin amsa kira, ga amsar da na bayar nan kasa:

- Adv -

Wannan zance an sha maimaita shi, haka ma jama’a sun sha mini tambaya kan wannan al’amari shekaru kusan biyar da suka gabata, kuma amsar da nake basu dai ita ce zan baka: cewa har yanzu babu wani ingantaccen bincike na kimiyya, kuma amintacce, wanda ke nuna yawan amfani da wayar salula na haddasa cutar sankara, wato “Cancer” kenan.  Wannan jita-jita ce da kuma dari-dari da wasu ke yi sanadiyyar sinadaran maganadisun lanatarkin sadarwa (Radio Frequency Electromagnetic Radiation) dake fita daga wayar a yayin da mai waya yake yin waya.  Galibin masu yada wannan jita-jita ko yawan damuwa da wannan lamari na kafa hujja ne da wannan sinadari, wanda suka ce bincike ya nuna cewa zai iya haddasa wannan cuta.  Damuwar ta karu sosai cikin shekarar 2011, sadda Hukumar Bincike kan Cutar Sankara ta Duniya (International Agency for Research on Cancer) ta nuna cewa akwai alamun nan gaba wannan sinadari na iya haddasa wannan cuta.

Don samun karin tabbaci, na tuntubi shafin Hukumar dake Lura da Yaduwar Cutar Sankara a kasar Birtaniya, wato: “Cancer Research, UK”.  A cikin bayanan da ta sabunta a shafinta dake: www.cancerresearchuk.org, a ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar 2016, ta nuna cewa wannan zance har yanzu babu kamshin gaskiya a cikinsa.  Domin dukkan binciken da aka gabatar a baya masu nuna wata alaka da wannan cuta basu cika sharuddan binciken kimiyya nagartacce da za a iya gina hukunci a kansa ba.  Hukumar tace hatta rahoton da hukumar binciken cutar sankara ta duniya ta fitar a shekarar 2011 bai da nagartar da za a iya dogaro dashi.  Wanda shi yasa ma hukumar ita kanta tace ta sanya wayar salula ne cikin jerin na’urorin da take “lura dasu” don ganin ko wannan sinadari na iya tasiri wajen haddasa wannan cuta.  In kuwa haka ne, ashe babu cikakken tabbaci kenan.

Ba wannan wayar salula kadai ba, hatta na’urar yada siginar Intanet, wato: “WiFi”, da na’urar wutar lantarki na zamani, wato: “Digital Meter,” ana tuhumar suna iya zama sanadi.  Sai dai a shekarar 2012 an sake gudanar da wani bincike wanda ya tabbatar da cewa babu sila, ko alaka na sisin kwabo tsakanin sinadarin da wadannan na’urori ke fitarwa da wannan cuta.  Wannan har wa yau shi ne bayanin da Cibiyar Lura da Cutar Sankara ta kasar Amurka, wato: “National Cancer Institute” ta fitar a shafinta.  Babban dalili shi ne, wannan sinadari da wayoyin salula da sauran na’urorin sadarwa ke fitarwa ba ya furzar da sinadarin ayon (ion), ba wannan kadai ba, babu sinadarin ayon ma tare dashi.  Amma sinadarin maganadisun lantarkin sadarwa mai fitar da sinadarin ayon (ion) ne ke haddasa cutar sankara.  Don haka, tunda wannan sinadari ba ya dauke da ayon a cikinsa, kenan ba shi bane ke haddasa wannan cuta.

Hukumar Lura da Cutar Sankara ta kasar Birtaniya taci gaba da cewa, ya zuwa yanzu dai babu wani abin dogaro dake tabbatar da wannan zargi, sai ma akasinsa.  Domin, a cewarta, in da gaske ne wannan sinadari na sanadin kamuwa da cutar sankara, a kalla an kwashe shekaru kusan 30 ana amfani da wannan na’urar sadarwa ta wayar salula a kasar Ingila, misali, amma tsawon wannan lokaci, yawan masu cutar sankara bai karu ba.  Da a ce wannan na’ura na haddasa wannan cuta, da ya kamata a ce a duk shekara ana samun karuwar masu kamuwa da cutar fiye da kima, musamman ta la’akari da yawan masu mu’amala da wayar salula a kasar baki daya.  Amma hakan bai kasance.   Ba ma a kasar ba kadai, a duk fadin duniya har yanzu ba a samu wani mutum guda daya da ya taba kamuwa da cutar sankara sanadiyyar yawan amfani da wayar salula ba.

A qarshe dai, abin da hukumar ta karkare bayani dashi dai shi ne, idan ma wannan sinadari na haddasa wannan cuta, to, ta yiwu sai bayan lokaci mai tsawon gaske, wanda babu wani bincike na kimiyyar zamanin yau da zai iya hasashen tsawon lokacin da za a iya kamuwa da cutar sanadiyyar amfani da wannan na’ura.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.