Fasahar “Digital Currency”: Manyan Matsalolin Cryptocurrency (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a. 28 ga watan Mayu, 2021.

321

Manyan Matsalolin “Cryptocurrency” (1)

Akwai matsaloli masu dimbin yawa da masana suka haddade dangane da samarwa, da aiwatar da cinikayya da nau’in kudin zamani na Intanet da ake kira: “Cryptocurrency”.  Wadannan masana kuwa sun hada da Malaman addini, musamman na musulunci, da masana hada-hadar kudade na zamani, da masana tattalin arzikin kasa, da masana a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani, da kuma masana a fannin tsaron kasa.  Daga cikin shahararrun matsalolin kudaden zamani na Intanet dai akwai su kamar haka:

Jahilci – Mafi Girman Hadari

Mafi girman hadarin dake tattare da kudaden zamani na Intanet shi ne jahiltar yadda tsarin hada-hadarsa ke gudana.  Shi yasa, abu na farko da ya kamata mu sani musamman a kasashe masu tasowa shi ne, wannan nau’i na kudi da ake yayinsa a yanzu, yana da hadarin gaske idan ka jahilci yadda tsarinsa, da kintsinsa, da hakikaninsa suke, a aikace.  Wannan ya faru ne saboda fasaha ce sabuwa da bata shige shekaru 11 ba ana amfani da ita.  Amma duk inda kabi a galibin manyan biranenmu a Najeriya, kaga gayu sunyi gungu ana tattaunawa, ko ana ta latse latse a wayar salula, galibi za ka samu ana hada-hadar wannan kudi ne.  Abin dake daukan hankalin mutane shi ne farashinta, da yadda take haurawa a kowane minti ko sa’a, wanda wannan ke haifar da riba mai tsoka.  To amma kuma, a ka’idar fannin hada-hadar kudi da zuba jari, duk haja ko jarin dake da riba mai yawa kuma yake saurin hauhawa da saukowa, ya fi hadari, kuma hasarar dake cikinsa daidai yake da ribar da ake tsammani ko samu.  In kuwa haka ne, ashe wajibi ne ga duk wanda zai shiga wannan harka ya zama ya shige shi ne da ilimi, ba da romon ka ba.  Ko don ganin wasu na cin riba kawai shi ma ya fada ciki.  Domin idan aka tashi hasara, sai an sha mamaki.

Haramtattun Hanyoyin Mu’amala

- Adv -

Abin da yake asali dangane da samuwar wannan fasaha shi ne, wadanda suka samar da ita dai ba hukumomi bane, a a, mutane ne daidaiku masu zaman kansu, kuma masu ra’ayin tawaye ga tsarin gudanar da al’amura na al’adar rayuwar yau.  Wadannan mutane dai masana ne kuma kwararru a harkar gina manhajar kwamfuta.  Sun samar da fasahar Bitcoin ne, musamman, don neman hanyar bat-da-sawu, da neman ‘yanci, da sirri wajen gudanar da wasu al’amuransu na rayuwa.  Shi yasa ma, da aka fara hako nau’in kudin Bitcoin, an fara amfani dashi ne a bakar kasuwar Intanet da ake kira “Darknet”, ko “Internet Black Market”.  Wannan mahalli fa, wuri ne da galibin masu hada-hada a cikinsa ‘yan kwaya ne, da karuwai, da manyan barayin Intanet, da masu sayar da haramtattun makamai ta karkashin kasa, da sauran ayyukan assha.  Kuma har yanzu galibin cinikayyar da ake yi a wannan kasuwa ta “Darknet”, duk da wadannan nau’ukan kudade ake gudanar dasu.  Domin babu wata hukuma da za ta iya ganewa.   Sannan kana iya bude lalitarka kai tsaye da wani suna daban, ba hotonka, ba adireshin gidanka, sannan babu wata alama ko sheda da za ta iya tabbatar da kasar da kake, ka gudanar da cinikayya cikin ruwan sanyi ba matsala.

Bayan haka, a yanzu galibin barayin gwamnati musamman a kasashe masu tasowa irin namu, suna amfani da wannan hanya na hada-hadar kudi wajen aikawa da kudaden da suka sata daga taskar gwamnati ko wadanda aka killace don hidimar jama’arsu, zuwa kasashen waje, inda za a mayar dasu zuwa kwandalolin Bitcoin cikin sauki, sannan daga baya a sayar su zama daloli, a kuma sake shigowa dasu cikin kasar a wani yanayi daban, ko a sayi wasu kayayyaki masu tsada na kasuwanci a wata kasar, sannan a shigo da kayayyakin a bude shago ko kasuwa a zuba ana sayarwa.  Wannan shi ake kira: “Money Laundering”.  Kai idan ka gani sai ka dauka halattacciyar dukiya ce.  Nan kuwa kara ce da kiyashi; dibar marar sani.

Har wa yau, manyan kungiyoyin hada-hadar miyagun kwayoyi dake duniya, musamman nahiyoyin Kudanci da Arewacin Amurka da Turai, suna amfani da wannan hanya su ma wajen aikawa da karban kudaden haramtattun hajojin da suke tallatawa.  Idan aka sayi hajojin, wanda galibi suke sayar dasu ta hanyar kafofin sada zumunta irin su Instagram, sai a aiko musu kudin a kimar Bitcoin, su canza don samunsu cikin daloli ko nau’in kudin da suke bukata.

Wadannan dalilan ne suka sa babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci dukkan bankunan kasuwanci da su rufe duk wata taskar ajiya da ake iya amfani da ita wajen hada-hada da cinikayyar kudaden zamani na Intanet.

Hasarar Bayanai da Dukiya

Kasancewar magudanar fasahar kudaden zamani na Intanet wata manhaja ce ta musamman mai dauke da tsaro da kariyar bayanai, yasa mutane suka aminta da wannan hanya fiye da tsarin hada-hadar kudade na al’ada da hukumomi da kamfanoni suka samar a zahirin rayuwa.  Wannan magudana, wato: “Blockchain”, manhaja ce da aka gina cikin mafi makurar tsaro da sirri da kariyar bayanai.  Da zarar ka yi rajistar lalitarka ta ajiya, wato: “Digital Wallet”, akwai kalmomin sirri da ake kira: “Private Key” da manhajar ke baka.  Kai kadai kasan wadannan kalmomi na sirri; hatta maginin manhajar bai sansu ba.  Da zarar ka bukaci aikawa da kudade, wannan magudana za ta yi amfani da wadannan kalmomin sirrin ne wajen tantanceka, sannan ta aika wa wanda kake nufi.  Inda matsalar take shi ne, da zarar ka mance ko ka batar da wadannan kalmomi na sirri, shikenan; ba za ka iya sake shiga lalitarka ba.  Kuma duk abin da ka mallaka a ciki, komai yawansu, sun tafi kenan.  Haka za su ci gaba da zama a ciki illa maa shaa Allah.  Babu wanda zai iya kaiwa gare su.  Sanadiyyar wannan matsala dai dimbin mutane sun rasa kwandalolinsu na biliyoyin daloli, saboda mance Kalmar sirrinsu da suka yi.  Sabanin tsarin hada-hadar kudade na zahirin rayuwa, inda bankinka zai iya canza maka Kalmar sirrinka don baka damar isa ga taskarka cikin sauki.  Karkashin wannan tsari, kai ne alkalin kanka.  Wannan na cikin manyan matsalolin tsarin kudaden zamani na Intanent.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.