Sakonnin Masu Karatu (2019) (16)

Siffar Duniya: Daga Kasar Amurka Zuwa Jafan

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 18 ga watan Oktoba, 2019.

61

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya kai da iyalanaka. Wannan karon shi ne na biyu da na rubuto maka wasika. Na rubuto maka wannan wasikar ne domin na jinjina maka kan yadda kayi gyare-gyare a shafinka na Taskar Baban Sadik. Gaskiya ya qayatar da ni sosai. Sai dai kuma a yanzu na samu bambanci; a baya idan ina karanta shafin zan iya karance shafin duka, amma yanzu gaskiya rubutun ya yi yawa ta hannun dama. Ma’ana rubutun ya yi wa wayata tsawo ba na ganinsu duka. Amma wataqila ina tunanin matsalar wayata ne. Daga Sunusi, Unashi Danko, Wasagu LG, Kebbi State: 07054106655

Wa alaikumus salam Malam Sunusi, ina godiya da gaisuwa. Lallai kamar yadda ka fada ne, matsalar daga wayarka ne. Idan ka hau shafin da wayar salula, za ka ga jerin sakonnin da na sabunta a farko, daya-bayan-daya. Wannan na biye da wannan. Daga kasa kuma za ka ga sauran fannoni da na jera. Idan ka matsa taken Maqala, za ta budo dauke da takaitattun bayanai. A kasan bayanin kuma za ka ga wani maballi (Button) launin ja, an rubuta: “Continue Reading”. Idan ka latsa, nan take sauran bayanan za su bayyana, su cike shafin gaba daya, ba wai a hannun dama ba kamar yadda kake gani a wayarka. Hakan zai baka damar karanta dukkan maqalar daga farko har qarshe. A kasan maqalar ma zaka ci karo da hotunan wasu maqaloli masu alaka da wacce ka gama karantawa. Sannan akwai mashigi da zai riskar dakai zuwa ga maqalar dake gaba ko bayan wacce ka gama karantawa. Duk wannan na samar dasu ne don sawwake ma mai karatu tsarin mu’amala da shafin ne.

Don haka, idan kana ganin sabanin yadda nayi bayani a sama, to, yana da kyau ka bibiyi wayarka. In kana da wata wayar da kake iya hawa Intanet da ita, ka gwada hawa shafin da ita, don gane bambancin dake tsakaninsu. Hakan shi zai taimaka maka wajen gano daga ina ne matsalar take. Da fatan ka gamsu. Allah sa a dace, amin.

Assalamu Alaikum Baban Sadik, ina da tambaya: don Allah ayi mini bayanin abin da Allah ya sanar da kai game da gaskiyar wai Amurkawa ko kuma sauran jama’ar yankin irin su Kanada in za su tafi kasa Japan wai ta yamma za su yi tafiyar – maimakon gabas. Wai saboda duniyar kamar qwallo take. Inji masu ikirarin haka. Na gode. Malam Dalhatu Aminiya.

- Adv -

Wa alaikumus salam, Malam Dalhatu barka ka dai. Da farko dai, bayani kan siffar duniya mun gama dashi tun a jerin maqalolin da muka gabatar shekaru 8 da suka gabata masu take: “Kimiyyar Kur’ani da na Zamani: A Ina Aka Hadu?”, kuma mun bayyana hakikanin gaskiyar wannan lamari na cewa, ita duniya a shimfide take kamar tabarma ko a cure take kamar qwallo.

Tambaya ta biyu kan cewa Amurkawa da mutanen kasar Kanada kan bi yammacin duniya ne don hadewa da kasar Jafan, don kusancinsu da ita idan aka gewayo ta yammaci, hakan gaskiya ne ta wani vangare, kuma ba gaskiya bane idan aka bi ta wani vangare. Da farko dai ban da masaniya kan cewa lallai Amurka kan koma ta yammaci don KARAsawa kasar Jafan; haka ma ‘yan kasar Kanada. Na biyu, don sauqin fahimtar wannan bayanai, yana da kyau mu fahimci cewa kasar Amurka, ta la’akari da mu dake Najeriya, tana yammacin duniya ne. Ita ce kasa ta qarshe dake yammacin duniyarmu ta yau. Domin jiharta mai suna Alaska, ita ce jiha ta qarshe dake yammacin duniya; daga ita sai ruwa kawai. Haka ma kasar Kanada take, bigire daya suke da kasar Amurka, bayanta babu komai sai ruwa. Ita kuma kasar Jafan tana gabashin duniya ne, can quryar gabas. Ita ma daga ita sai ruwa kawai.

Kuma tunda duniyar a mulmule take kamar qwallo, wannan yasa idan ka dubi alaqar dake tsakanin quryar gabas da quryar yammaci, sai ka ga ashe zasu iya haxewa daga baya. Kamar dai Karin maganar Bahaushe ne da yake cewa: “Inna ta zaga Baba ya zaga…”
Ta la’akari da bayanin da ya gabata kan bigiren kasar Amurka da Kanada a vangare daya, da bigiren kasar Jafan da wani vangaren kasar Rasha ma, a daya vangaren, sai kaga cewa abu ne mai sauki kuma mai yiwuwa ka iya isa kasar kasar Jafan idan ka zagayo daga kasar Amurka ko Kanada. Haka ma idan kana son isa kasar Amurka da Kanada daga kasar Jafan; zai fi sauqi da saurin zuwa idan ka zagaya ta baya. Ya zama yanke kenan, wato: “Short Cut”.
To amma kuma, kamar yadda na fada a farko, ba ni da tabbacin faruwar haka a aikace.

Saboda na farko dai galibin tafiye tafiye tsakanin wadannan kasashe kan faru ne ta hanyar jirgin sama. Ko ta hanyar jirgin ruwa, wanda kuma ke xaukowa daga kasar Amurka ne ta tekun Atlantika, a kutso ta vangaren Afirka da Asiya, sannan a dire a kasar Jafan. Haka wasu kan bi jiragen ruwa zuwa kasashen Turai (Europe), daga nan su bi jiragen kasa don watayawa tsakanin kasashe da buxe ido ko don kasuwanci. Amma zagayawa daga bayan kasar Amurka da Kanada zuwa kasar Jafan, ta baya, abu ne da ban da masaniya a kai. Ko dai saboda ba a yi a aikace, ko kuma hakan bai shahara ba. Domin bigiren dake tsakanin wadannan kasashe teku ne mai zurfi, kuma nan ne vangaren da yafi kowane vangare sanyi daga cikin tekunan duniya. Domin galibin shi qanKARA ne. Wannan na iya zama dalilin da zai sa a kasa kutsawa ciki don yin tafiya makamancin wannan.

Wannan shi ne taqaitaccen bayanin da zan iya yi kan wannan al’amari. Da fatan ka gamsu. Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.