Sakonnin Masu Karatu (2019) (15)

Yadda Ake Gyaran Shafin Facebook

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 11 ga watan Oktoba, 2019.

70

Assalamu Alaikum Baban Sadik, Ina fatan kana lafiya. Ina son zama daga cikin mabiyan shafinka na Dandalin Facebook ne, amma ban san sunar shafin ba. Shi yasa nake son ko za ka taimaka min da sunan, saboda in yi ”Like” don amfana da abubuwa masu amfani. Na gode. Sunana Sa’idu Abubakar daga jihar Nasarawa: 09080080326

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Sa’id. Shafina dake dandalin Facebook, wanda na buxe shi musamman don fadakar da masu karatu, ana iya samunsa a wannan adireshin ne: www.facebook.com/taskarbabansadik. Da zarar ka shigar da wannan adireshin, za ka samu shafin, amma baza ka iya karanta dukkan bayanan ba ka shigar da suna (username) da kalmar sirrinka (password) na Facebook. Idan ba ka da rajista da Facebook, sai kayi rajistar sabon shafi. In kuma shigar da adireshin zai maka wahala, idan kana da shafi a Facebook sai ka nemi: “Taskar Baban Sadik”, nan take za a buxo maka shafuka masu makamancin sunan, za ka ga nawa shafin xauke da hotona da kuma maqaloli masu alaqa da fannin kimiyya da fasahar sadarwa. Daga nan sai ka riski shafin ka matsa alamar “Like” don a rika sanar da kai a duk sadda na sabunta bayanan dake shafin.

Muna murna da zuwanka. Allah sa mu amfana baki xaya da juna. Na gode.
Assalamu alaikum Baban Sadik, matsalata game da shafin Facebook dina ne; idan na shigar da kalmar sirri sai ya nuna min sunan wani. Idan na sake nemo shafin, to, sai naga duk abokaina babu ko xaya. Wace hanya zan bi domin hana masu yin kutse a shafin facebook dina? Daga Ahmed Garba Zubarau, Auyo, Jigawa. 09070608002

Wa alaikumus salam, barka da Malam Ahmad. Wannan ke nuna cewa shafin ya samu matsala kenan. Ta yiwu wani ya kwace shafin ne, tunda har idan ka hau ba ka ganin sunanka sai sunan wani, kuma shafinka ne. Abin da zan iya fahimta dai a taqaice, shi ne, wani ya kwace shafinka. Hanya mafi sauki ita ce ka kai koke ga hukumar Facebook don su taimaka maka cikin sauki. Wannan wani abu ne da suka saba yi. Domin ko nace zan maka bayani filla kan yadda zaka dawo da shafi ba lale bane ka fahimta ciki. Ka shiga wannan adireshin: https://m.facebook.com/hacked.

- Adv -

Da zarar ka hau shafin, za ka ga shudiyar alama mai take: “My Account is Compromised”. Idan ka matsa, za a buqaci wasu bayanai daga gareka. Dole ka basu bayanai na gaskiya, kuma tabbatattu. Da su za suyi amfani wajen karvo maka shafinka. Da fatan ka gamsu, kuma ina maka fatan alheri. Allah sa a dace, amin.

Salamun alaikum Baban Sadik, ya fama da mu? Allah Yayi tukuici da Firdausi, amin. Tambayata ita ce: don Allah ko akwai matsala idan kullum ina sa wayata caji a kwamfiyuta? Daga Al-Ameen Zariya. 07035586603

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Al-Ameen. A iya sanina babu wata matsala don ka sanya wayarka caji ta hanyar amfani da wayar caji a kwamfuta. Domin yana daga cikin abin da aka kintsa a cikin wayar salula, ya zama ana iya amfani da wutar makamashin lantarkin jikin kwamfuta don yin cajin batirinta. Na sanar kuma zan kara sanarwa, cewa duk asalin makamashin lantarkin da za ka yi amfani dashi wajen cajin wayar salula, dole ne ya zama mizanin karfinsa ya dara na mizanin batirin wayar. Na yi dogon bayanai a tambayar da wani dan uwa yayi kan tasirin cajin waya da na’urar “Power Bank”, watanni uku da suka shude. Za ka iya samun wannan bayani cikakke a wannan adireshi dake Taskar Baban Sadik: https://babansadik.com/saqonnin-masu-karatu-2019-11/.
Dangane da haka, idan kayi la’akari da mizanin ma’adanar lantarkin kwamfuta da na wayar salula, ko kusa na kwamfuta ya fi girma. Illa kawai ka sani, shi caji ta amfani da kwamfuta kan dauki lokaci kafin cajin ya cika, idan ka kwatanta da lokacin da asalin na’urar caji kan dauka kafin ya cike batirin waya. Wannan kuma ba wani abu bane, saboda a kwamfuta akwai abubuwa da dama dake amfani da makamashinta; ba wai kai tsaye wutar ke isa baitirin wayarka ba. Sabanin na na’urar caji da aka killace musamman don daukowa da loda makamashin lantarkin daga asalinsa zuwa cikin batirin wayarka.
Wannan shi ne dan tsokacin da zan iya yi a halin yanzu. Da fatan ka gamsu. Allah sa a dace, amin.

Salamun alaikum Baban Sadik, Allah Ya ja kwana mu ci gaba da kwankwadar karatu. Don Allah a taimakemu da lambar da akan turawa don kulle taskar banki cikin gaggawa. Barayin waya sukan ciri kuxi ta asusun mutum na banki, su sa kati a layin wayar da suka sata, sai mutum ya je ciran kuxinsa, sai ya gane ashe sun kwashe. Al-Ameen Zariya: 07035586603

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Al-Ameen. Akwai lambobi da kowane banki ke bayarwa ga kwastomominsa. Duk saqo idan banki ya aiko maka sanadiyyar cire kuxi ko sanya kuxi a taskarka ta banki, a kasa za ka ga sanarwa daga bankin cewa idan kana da matsala ka kira wata lamba ta musamman. Idan kuma bacewa ko sace maka katin ATM dinka aka yi, ga lamba ka kira don toshe katin kafin a sace maka kuxaxen dake ciki.
Hanya mafi sauki shi ne, kayi iya kokarinka wajen kare dukkan bayanan taskarka na banki don kada wani ya sace su. Wannan ita ce hanya mafi sauki. Hausawa kan ce: “Riga-kafi ya fi magani”. Don haka, duk bankin da kake da taska dasu, yana da kyau ka san lambar da ake iya tuntubarsu idan matsala ta auku. Wannan ita ce hanya mafi sauki. Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.