Sakonnin Masu Karatu (2017) (16)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

70

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Don Allah ina so ka tura min kasidar da kayi ta shekarar da ta wuce akan yadda ake loda manhajar Whatsapp akan kwamfuta nau’in Laptop.  Ga Imel dina: tasiuismaeelrimaye@gmail.com.  Ka huta lafiya.  – Tasiu Ismail Rimaye

Wa alaikumus salam Malam Tasiu, barka dai.  Wancan tsari da kake ishara gare shi yanzu ya zama tsohon yayi.  Kamfanin Whatsapp ya bullo da hanyar amfani da manhajar Whatsapp a kan kwamfuta cikin sauki.  Idan kana da Laptop za ka iya amfani da wannan tsari ba tare da matsala ba.

Abu na farko shi ne ya zama kana da manhajar Whatsapp a kan wayarka ta salula.  Daga nan sai ka kunna “data”.  Ka kuma kunna Laptop dinka, ka jona mata Intanet, sai kaje shafin Whatsapp dake dauke da nau’in Whatsapp na kwamfuta a wannan shafi: http://web.whatsapp.com.  Nan take za a budo maka shafi, dauke da wani bakin tambari mai farin ratsi a jikinsa.  Wannan tambari shi ake kira: “QR Code”.  Daya ne daga cikin hanyoyin aiwatar da sadarwa tsakanin na’urorin sadarwa mai cike da tsaron bayanai. 

Daga nan sai ka dauki wayarka ta salula, ka hawa manhajar Whatsapp.  Kana budowa sai ka latsa wasu dige-dige guda uku a jere dake saman fuskar manhajar daga sama a bangaren dama.  Daga bayanan da zasu bayyana, za ka ga: “Whatsapp Web.”  Da zarar ka matsa, na’urar daukan hoton wayarka (kyamara) za ta budo.  Sai ka haska wannan na’ura kai tsaye a daidai inda wancan tambari na “QR Code” yake a shafin Whatsapp da ka budo a Laptop ko kwamfutarka.  Da zarar ka haska iya daidai mahallin da tambarin yake, nan take shafin zai juye, sai kawai ka ga Manhajar Whatsapp irin wanda ke wayarka, kai tsaye.

Kana iya gudanar da hirarraki da aikawa da sakonni na hotuna da bidiyo da sauti kamar yadda kake yi a wayarka.  Bambancin kawai shi ne, dole ne ya zama sakonnin da kake son aikawa suna kan kwamfutarka ne, in hotuna ne ko bidiyo.  In kuwa ba haka, sai dai ka koma kan wayarka ka tura ta can.  Kuma yin hakan bazai sa a rufe shafin da ka budo a kwamfuta ba.

Wannan, a takaice, shi ne yadda ake mu’amala da manhajar Whatsapp a kwamfuta.  Sai dai kuma a kiyaye, da zarar ka gama abin da kake yi, dole ne ka fita (wato: “Log Out”), in ba haka ba duk wanda ya samu hawa kan kwamfutar kuma ya budo manhajar lilo (Browser), zai iya ganin dukkan bayananka.  Don ficewa daga manhajar, kana iya matsa dige-dige uku dake bangaren sama a hagu, sai ka matsa: “Log Out.”  Kai tsaye za a rufe shafin. 

- Adv -

Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, da fatan kana lafiya Baban Sadik.  Don Allah ina so ayi mini bayani a kan manhaja da na’urar “CCTV Camera.”  Na gode. –  Aminu Marafa Katsina

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aminu Marafa.  Wannan na’ura ta CCTV dai na’ura ce dake dauke da manhajar daukan hoton bidiyo a asirce, a wurare na musamman, don samar da tsaro ta hanyar lura da shigi-ficin jama’a.  Akan sanya ta a ofisoshin gwamnati, da kamfanoni, da gidajen masu hali da sauran wurare masu dauke da tsaro matuka.

Wannan na’ura tana nan kala-kala, kuma tana zuwa ne da kananan na’urar daukar hoto (cameras).  Cikakken ma’anar lafazin CCTV na nufi: “Close Circuit Television” ne.  Akan girke asalin na’urar ne a wuri killatacce, kuma kamar Talabijin take (duk da yanzu ana iya amfani da talabijin din zamani masu shafaffen fuska).  Daga jikinta ake jojjona sauran kananan na’urorin daukan hoton, wadanda su ne za su rika hakaito mata shawagin mutane ita kuma tana taskance su a ma’adanai masu girma.

A galibin wurare ba a kashe wannan na’ura, domin sakonnin da take taskancewa ne ake adanawa don kafa hujja a lokacin bacin rana.  Don haka kullum cikin aiki take.  A wasu wurare idan kaje za ka ga ana sanya sanarwa cewa mutane suyi taka-tsantsan, saboda duk motsinsu ana lura dashi kuma ana dauka ta hanyar wannan na’ura.  A wasu wurare kuma ba a sanar da jama’a, sai matsala ta faru ake gane cewa akwai ta.

Wannan shi ne kadan cikin abin da ya sawwaka.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.