Tsarin Fasahar Faifan DVD (4)

A wannan mako cikin dacewar Ubangiji, za mu xora daga inda muka dakata. Wannan shi ne kashi na 4. A sha karatu lafiya.

343

Matashiya

A makon jiya bayani ya gabata kan nau’ukan na’urar sarrafa faifan CD, inda mai karatu yaga bamban-bambancen dake tsakanin wacce aka qera a farkon zamani, mai zaman kanta, da wacce ke xauke kan kwamfuta, da na mota, sai kuma waxanda aka qera masu tafi-da-gidanka, waxanda ba sa buqatar talabijin wajen amfani dasu.  Duk da cewa suna sarrafa bayanan dake xauke cikin faifan CD ne, sai dai wasun su sunfi gamewa wajen amfaninsu; wasu kan sarrafa nau’in sauti da bidiyo ne kaxai, kamar yadda bayani ya gabaya.  A yayin da wasu kuma ke iya sarrafa sauti da bidiyo da rubutattun bayanai da kuma manhajar kwamfuta.  A wannan mako cikin dacewar Ubangiji, za mu xora daga inda muka dakata.

Na’urar “DVD Player”

Wannan ita na’urar da aka samar tare da fasahar DVD.  Bayani ya gabata cewa fasahar DVD ta biyo bayan fasahar CD ce, wadda sanadiyyar naqasun da suka bayyana na rashin juriya, da rashin qarko da kuma qarancin mizanin ma’adana, aka samu canji da fasahar DVD.  Samar da faifan DVD ya haifar da samuwar na’urar sarrafa faifan DVD, kamar yadda samar da faifan garmaho ya haifar da samuwar na’urar sarrafan faifan garmaho (Gramophone Player), a lokuta ko zamanin baya.

Na’urar sarrafawa da bayyana bayanan dake xauke cikin faifan DVD ita ake kira: “DVD Player”.  Wannan na’ura ta xara na’urar sarrafa faifan CD, saboda bambancin nau’in bayanan da faya-fayan ke xauke dasu, da kuma bambancin asalin fasahohin da aka yi amfani dasu wajen samar da su.  Na’urar DVD Player na amfani da nau’in hasken lantarki na leza ne, wato: “Laser Light”, launin ja, wajen karva, da sarrafawa da kuma bayyana bayanan da ake zuba mata a farkon lamari ko a duk sadda aka tashi sabunta su, idan faifan nau’in “Re-Writable” ne, wato: DVD-WR.  Wannan tsari ya xara na CD nesa ba kusa ba.  Sannan yana xauke ne da fasahar dake iya tsallakawa daga fallen farko zuwa falle na biyu, idan faifan mai tagwayen falle ne, wato: “Double Layer DVD”.

Na’urar sarrafa DVD na zuwa nau’i-nau’i ne.  Akwai nau’in gama-gari, wato na’ura ta musamman mai zaman kanta, wacce aka qera don sarrafawa da kuma kallo ko mu’amala da bayanan dake xauke cikin faifan DVD.  Wannan ita ce aka fara qerawa a farkon bayyanar faifan DVD, kuma ana jona ta da talabijin ne, don amfani da ita.  Wannan nau’i tana iya sarrafa bayanan sauti ne ko bidiyo dake xauke cikin faifan.  Amma duk abin da ya shafi rubutattun bayanai ko wasu manhajoji na kwamfuta da ake iya taskance su cikin faifan DVD, wannan na’ura ba ta iya sarrafa su ko kaxan.  Wannan, a al’adance, idan kaji an ce: “DVD Player”, to, ita ake nufi.

- Adv -

Sai nau’in na’urar sarrafa DVD dake zuwa cikin na’urar kwamfuta.  Wannan ake kira: “DVD-ROM”.  Kamar “CD-ROM” dake iya sarrafa faifan CD a kwamfuta, wannan na’ura ita ce ke iya sarrafa faifan DVD a jikin kwamfuta.  Ba wai sarrafawa ma kaxai ba, tana iya taskance bayanai, ko sauti ko bidiyo a kan faifan DVD sabo, wanda babu komai a cikinsa.  Sannan tana iya goge bayanan dake cikin faifan DVD-RW, wato nau’in faifan DVD da ake iya sabunta bayanai a cikinsa kenan, sannan ta zuba wasu bayanan.  Ko kuma sabunta waxanda ke ciki.  Wannan na’ura bata tsaya wajen sarrafawa da zuba bayanan sauti da bidiyo da rubutattun bayanai kaxai ba, hatta manhajar kwamfuta (Computer Applications) tana iya taskance ta a kan faifan DVD, sannan idan ma aka kawo faifan DVD mai dauke da manhajar kwamfuta, tana iya sarrafa shi don loda wa kwamfutar wannan manhaja dake ciki.  Kamar yadda bayani ya gabata, idan kaji ance: “DVD-ROM”, to, wannan na’ura ake nufi.

Sai nau’in na’urar saffara DVD mai zuwa cikin mota.  Wannan nau’i kuma da mota kaxai ta kevanta.  Ba a iya amfani da ita a kan wata na’ura in dai ba mota ba.  Sannan ba a iya jona ta da talabijin; a mota kaxai ake kiya amfani da ita.  Qari a kan haka, bayanan sauti da bidiyo kaxai take iya sarrafawa.  Ba ta iya sarrafa rubutattun bayanai ko faifan DVD mai xauke da manhajar kwamfuta.

Sai na qarshe da za mu dakata akai, wato: “Portable DVD Player”.  Ita kuma na’ura ce ta musamman, tafi-da-gidanka, wacce ake amfani da ita wajen sarrafa bayanan faifan DVD ba tare da an buqaci talabijin ko kwamfuta ba.  Kuma kana iya sanya ta cikin jaka kayi tafiya da ita.  Bayan haka, kana iya jona mata sifika ta kunne (Earpiece), don sauraren sautin waqoqi ko fim xin da kake kallo, idan bidiyo ne.

Qarko da Tsawon Rayuwar Faifan DVD

A qarshe dai, masana sun tabbatar da cewa faifan DVD ya xara faifan CD qarko da juriya, da ma tsawon rayuwa.  A cikin wani bincike na musamman da aka gudanar, sakamako ya tabbatar da cewa faya-fayan DVD, da DVD-R, da DVD+R na xaukan shekaru 30 zuwa 100 ana amfani dasu, waxanda suka danganci sauti da bidiyo kenan.  Ga nau’in faifan DVD-RW, da DVD+RW, da kuma DVD-RAM, sakamakon gwajin da aka yi ya nuna suna iya xaukan shekaru 30 ana amfani dasu.  Wannan ke tabbatar da qarkonsu a kan faifan CD.

A xaya vangaren kuma an tabbatar da cewa babban abin da ke daqushe qarkon faifan DVD dai shi ne danshi sanadiyyar ruwa ko rava, da kuma hasken rana mai kaifi, dawwamamme, wanda ke tasiri wajen rage tagomashin bayanan dake cikinsa.  Idan ka xauke waxannan dalilai, faifan DVD na iya rayuwa muddin za a samu na’urar da za ta sarrafa bayanan da ke cikinsa, ba tare da wata matsala ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.