Dan Dandatsan (Hacker) Da Yayi Kutse Cikin Cibiyar Hada-Hadar Kudaden Kirifto Ta “Poly Network”, Kuma Yayi Awon Gaba Da Dala Miliyan 610 ($610M), Ya Fara Dawo Da Kudaden Da Ya Wawashe (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 20 ga watan Agusta, 2021.

339

A wani lamari mai kama da almara, wani Dan Dandatsa (Hacker), ya yi kutse cikin shafin cibiyar hada-hadar kudaden kirifto (Cryptocurrency) na kamfanin Poly Network a ranar talatar makon jiya, inda yayi awon gaba da nau’ukan kudaden kirifto guda 12 da kimarsu ta kai dalar Amurka miliyan 610 ($610 mil), kwatankwacin naira biliyan 302.10 (N302.10bn).  Wannan lamari dai ya auku ne a yammacin Talatar makon jiya, 10 ga watan Agusta, 2021, lokacin da shugaban kamfanin Poly Network, ya sanar a shafinsa na Twitter.  Wannan, a cewar masana harkar kirifto a duniya, shi ne sata ta hanyar kutse mafi girma da muni, a tarihin hada-hadar kudaden zamani na Intanet, wato: “Cryptocurrency”.

Kamfanin Poly Network dai shafin yanar sadarwa ne mai dauke da manhajar musayar kudaden kirifto tsakanin mutane, ta amfani da magudanar hada-hadar kudade (Blockchain) na cibiyar Binance Smart Chain (BSC), da Etherium, da Polygon, da Neo, da Ontology da dai sauransu.  Masu hada-hadar kirifto a Binance da Ether, misali, suna iya amfani da cibiyar Poly Network wajen aika kudade a tsakaninsu, kai tsaye, ta amfani da manhajar tantance hada-hadar kudi na kai tsaye, wato: “Smart Contracts”.  Ta amfani da wannan manhaja ne, a matsayinsa na kwararre a fannin gina manhajar kwamfuta, ya wawashe adadi mai yawa na nau’ukan kudaden kirifto guda 12, wanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyan 610.  A cewar Kelvin Fichter, mai fashin baki kan harkokin kudaden zamani na Intanet kuma masani a tsarin gina manhajar “Cryptocurrency”, “Dan Dandatsan ya yi amfani da kwarewarsa ne wajen goge bayanan tantancewa da kamfanonin uku (Binance SC, da Etherium, da kuma Polygon) ke amfani dashi a manhajarsu, da dora nasa adireshin asusun.”

Daga nan ne ya ingiza wadannan kudade ta hanyar rarraba su zuwa wasu asusunsa guda uku.  Bayan ya ingiza kudaden, nan take ya debi dala miliyan 100 ya aika su cikin wani asusu dake cibiyar hada-hadar kudaden kirifto mai suna: “Ellipsis Finance”.   Da yayi yunkurin ingiza wasu zuwa wani asusu dake cibiyar hada-hadar kudade na “Curve.fi”, sai ya tarar an toshe hanyar yin hakan, ta hanyar dakile adireshin asusunsa.

- Adv -

Ganin munin wannan lamari, da yadda abin ya shafi dubban masu ajiya a wannan shafi na Poly Netowork, yasa kamfanin ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga dan Dandatsan da ya aiwatar da wannan kutse, yana mai sanar dashi cewa: “Ka sani, wannan zunzurutn kudade da ka sace ta hanyar kutse, shi ne adadi mafi yawa a tarihin hada-hadar kudaden kirifto a duniya.  Kudaden da ka sace (har wa yau), kudaden dubunnan mutane ne da ke hada-hada a wannan mahalli.  Ya kamata mu fara tattaunawa da kai, don samun mafita.”  A karshe sakon yaci gaba da cewa: “Amma idan kaki yarda, to, ka sani abin da ka aikata laifi ne mai girma, wanda za a iya hukunta ka a kai, a kowace kasa ce kuwa.”

Aika wannan sako ke da wuya, sai wannan dan Dandatsa ya fara dawo da wani adadi ko kaso na kudaden da ya sace, inda a tsakanin sakon ya sanar da cewa: “Na amince, zan dawo da wadannan kudade gaba dayansu.  Amma kafin nan, a sanar dani adireshin taskar da zan aika kudaden gaba daya.  Daman na yi hakan ne ba don zalunci ba, sai don nuna wa masu wannan cibiya irin kura-kuran da madaukan hada-hadar kudadensu ke dauke dashi. Ban yi haka don guduwa da kudaden ba.”

Wannan lamari ya daure wa mutane kai. Domin wannan shi ne karo na farko a tarihin duniyar sadarwa da wani zai sace kudade masu dimbin yawa irin wannan, sannan ya dawo dasu ba tare da ko sisi yayi ciwon kai ba.  To amma sadda ya fadi hakan, ba kowa ya yarda da zancensa ba.  Nan take kamfanin Poly Netowork ya bude asusu na musamman, ya kuma aika masa adireshin asusun, don bashi damar dawo da wadannan kudade.  Wannan asusu da aka bude dai yana dauke ne da sa hannun mutane sama da daya (Multisig address), wanda a tsarin hada-hadar kudade na kirifto, idan ya bude asusun, ya kuma zuba kudaden a ciki, zai aiko mabudin asusun ne don bai wa kamfanin damar budewa da kuma ingiza kudaden zuwa asusun masu su.

Abin mamaki, nan take yaci gaba da ingizo wadannan nau’ukan kudade da ya wawashe, kadan, kadan; lokaci bayan lokaci.  Kwanaki biyu bayan wannan tabargaza, dan Dandatsar ya dawo da adadin kudaden da kimarsu ya kai dala miliyan 325 ($325 mil).  A duk sadda ya ingizo kudade, kamfanin Poly Network kan fitar da sanarwa mai dauke da adadin kudaden da ya ingizo, da kuma lokacin da ya ingizo.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.