Sakonnin Masu Karatu (2013) (3)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

55

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah wace hanya zan bi wajen bude akwatin Imel?  Daga: Baban-Yaya Dan Employer, Kwanar-Dangora.

Wa alaikumus salam, barka dai.  Bude akwatin Imel abu ne mai sauki.  Sai dai in ba wayar salula mai dauke da babbar manhajar Android kake amfani da ita, sai dai kayi amfani da kwamfuta wajen yin hakan. Ka shiga wannan gidan yanar sadarwa idan na Gmail kake so: http://mail.google.com sai ka gangara kasa inda aka rubuta “Create and Account,” ka matsa, za a kaika inda za ka cike fom ta hanyar shigar da dukkan bayanan da ake bukata daga gare ka kafin ka bude. A ciki za a bukaci ka zabi suna (username) da kalmar iznin shiga (password), da dai sauran bayanai.

Idan kuma Yahoo kake so, ka shiga nan: http://mail.yahoo.com, duk tsarin iri daya ne.  Idan wayarka ba Android bace, kana iya shigar da wancan adireshi na Google, amma za su bukaci ka shigar da lambar wayarka ne, sai su turo maka shafin da ke dauke da fom da za ka cike.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum, don Allah ina son a mini bayanin yadda zan adana sakon wayata cikin katin ma’adanar waya (Memory Card).  Saboda na ji kayi bayani a jaridar AMINIYA, kuma ni lokacin da aka yi bayanin ba ni da ita.  Daga Almajirinka: Kabiru Ridwan Sokoto.

- Adv -

Wa alaikumus salam, wannan ba wani abu bane mai wahala.  Na farko ka sanya katin ma’adanar wayar a cikin waya, sannan ka je manhajar sakonni (Messages), ka shiga “Options” wato bangaren zabe-zabe kenan.  Za ka ganshi a bangaren hagu ko dama; ya danganci nau’in wayarka.  A jerin bayanan dake “Opetions” za ka ga inda aka rubuta “Mark All,”  sai ka matsa.  Hakan zai sanya wa dukkan sakonnin dake ciki alamar “maki” (wato check mark).  Da zarar an sa musu alamar maki, sai ka sake zuwa “Options” har wa yau, ka latsa.  Daga cikin jerin zabin da ke wurin za ka “Move to Memory Card” ko wani abu makamancin haka.  Sai kawai ka zaba, za a kwafe su duka a kai maka su cikin katin ma’adanar wayar ba bata lokaci.  Sannan kana iya kwafe su ma zuwa katin SIM dinka, duk ta wannan hanya, muddin lambobinka basu cike ma’adanar SIM din ba.

Idan kuma wayar Nokia ce, kana iya saukar da manhajar “Nokia PC” sai ka jona wayar da kwamfutarka, sai ka bi tsare-tsaren da ke ciki, za a baka damar kwashe duk abin da ke cikin wayarka zuwa kwamfutarka.  Wannan ma shi ne yafi sauki.   Da fatan ka gamsu.


Assalamu Alaikum Malam, tambayata ita ce: mene ne bambancin waya nau’in Android da Windows Phone?  Daga: 08052380474

Wa alaikumus salam, da fatan kana lafiya.  A gaskiya wannan tambaya ta sha maimaituwa a wannan shafi, don haka idan kana bukatar amsa gamsasshe, kana iya zuwa shafina da ke Facebook mai suna “Dandalin Kimiyya da Fasahar Sadarwa,” (www.facebook.com/kimiyyadafasaharsadarwa)  za ka ga amsar da na bayar a baya.  Amsa ce mai gamsarwa, domin ta kai shafuka kusan uku.  Wannan zai fi sauki da ace in sake ba ka amsa a nan.  Da fatan za a yi hakuri.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.