Sakonnin Masu Karatu (2018) (8)

Ga wasu daga cikin sakonnin da nake samu a lokuta daban-daban. Na amsa su iya gwargwado. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

194

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya gida da ayyuka?  A gaskiya babu kalaman da za mu iya gode maka dasu sai dai muce Allah ya saka da alkhairi, amin.  Na kasance ina bibiyan shafinka da kuma kasidunka a AMINIYA tsawon shekaru.  Don Allah ina da tambaya: shin, mene ne (Aliens)?  Sannan meye anfaninsu? Sako daga Almustapha M. Aliyu, Birnin Kebbi.  Ka huta lafiya. Almustapha altinealmustapha@gmail.com 

Wa alaikumus salam Malam Mustapha. Da fatan kana cikin koshin lafiya, amin.  Da farko dai tukun, kalmar “Alien” a asalin lugga na turanci, na ishara ne ga wani abu bako, wanda ba a sanshi ba.  A harshen malaman kimiyyar wannan zamani kuma, musamman na kasar Amurka, kalmar na ishara ne ga wasu bakin halittu da ake ikirarin ana ganin wulkitawarsu a wannan duniya tamu, wadanda kuma, a cewar wasu, yanayin bai yi kama da na halittun wannan duniya da muke rayuwa a ciki ba.

Misali, akwai hotunan bidiyo birjik dake yawo a Intanet, musamman a youtube, masu dauke da ire-iren wadannan halittu, a cewar masu loda bidiyon, wadanda suka shigo wannan duniya tamu.  Ko kuma suke wannan duniya tamu amma ba a san daga ina suke zuwa ba, masu wulkitawa a sasannin sararin samaniyar wannan duniya tamu.

A jumlace, wadannan halittu da ake kira: “Aliens”, an kira su da wannan suna ne saboda ba a san wasu irin halittu bane.  Suna cikin jerin abubuwan da ake ganin suna wulkitawa a wannan duniya ba tare da sanin hakikaninsu ba.  Malaman kimiyyar sararin samaniya da kimiyyar halittu na kiransu: “Unidentified Flying Objects” ko “UFO” a gajarce.  Ma’ana, abubuwa masu wulkitawa da ba a san hakikaninsu ba.

- Adv -

Bayani kan “Aliens” abu ne mai cike da rudani.  Wasu sunce tabbas halittu ne dake shigowa wannan duniya tamu daga wasu duniyoyin.  Wasu kuma suka ce a a, duk tatsuniya ce lamarin.  Shi yasa, har yanzu babu wani tabbaci kan hakikanin wadannan halittu ko abubuwa dake aka ce suna yawo a sararin samaniya masu kama da wasu halittun da dan adam bai sansu ba.  Wadanda ke tallatawa tare da yada samuwar wadannan halittu dai, da kuma nuna cewa dole akwai su, ana musu lakabi da: “Conspiracy Theorists”, wato mutanen dake ganin yiwuwar faruwar kowane irin abu; da wanda hankali da ala’ada zai iya dauka, da wanda bazai iya dauka ba.

Don haka, a duk duniya gaba baya, babu zance tsayayye kan hakikaninsu da samuwarsu, balle muyi batu kan amfaninsu.  Wannan shi ne abin da zan iya cewa.  Allah sa a mu dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alkairi.  Na dade ina bibiyan shafinka tun shekarar 2009.  Ban taba aiko maka gaisuwa ba sai wannan karon. Ka huta lafiya, a gaishe min da Sadik.  Daga Ibrahim Majidadi: ibrahimmajidadi3@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Ibrahim barka ka dai.  Ina godiya matuka da wannan sako naka.  Allah saka da alheri, ya kuma hada fuskokinmu da alheri a duk inda muke.  Na gode.  Na gode.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.