Sakonnin Masu Karatu (2017) (19)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

127

Salaamun alaikum Baban Sadik, barka dai.  Yaya jama’a?  Tambayata ita ce: don Allah wace irin manhaja zan yi amfani da ita a “Laptop” dina don yin zane-zane da hada hotuna da bidiyo (Graphics) masu kyau, ko hada nau’in “Business Cards”?  A huta lafiya.  –  08188146087

Wa alaikumus salam, barka dai.  Akwai manhajojin tsara hotuna da zane daban-daban a kasuwa.  Wasu na sayarwa ne, wasu kuma kyauta ake bayar dasu.  Wasu masu sauki ne wasu kuma sai kwararru ke iya amfani dasu.  Amma da koyo, ana iya sarrafa su.  Domin da babu makoyi, da tuni gwanaye sun kare.  Kada in cika ka da surutu.

Wacce tafi kowacce fice dai ita ce: Photoshop na kamfanin Adobe dake kasar Amurka.  Wannan manhaja tana da dan Karen tsada gaskiya, sannan tana dauke ne da hanyoyin tsarawa da zana hotuna marasa iyaka.  Na ce marasa iyaka ne saboda kowane tsari dake dauke dashi, kana iya amfani dashi ta hanyoyi sama da goma wajen aiwatar da abu guda.  Kamar yadda na fada, akwai tsada gaskiya.  Idan za ka iya saya, to, ita ce tayi fice wajen inganci da kayatarwa da kuma kyau. 

Sannan akwai na kyauta wadanda za ka saukar kayi yadda kake so dasu.  Sai dai basu kai Photoshop ba, duk da cewa su ma ba baya bane, muddin ka san abin da kake son aiwatarwa dasu.  Akwai Gravit Design da za ka samu kyauta a shafinsu dake: www.designer.io.  Akwai Vectr da za ka samu kyauta ita ma, a shafinsu dake: www.vectr.com.  Sai kuma InkSpace, wacce ita ma ta shahara kamar yadda Photoshop ta shahara, amma kyauta ce ita.  Za ka samu InkSpace a shafinsu dake: www.inkspace.org.  Bayan wadannan akwai Gimp, wadda ita ma ta shahara kamar InkSpace.  Ita ma kyauta ce, don ina amfani da ita yanzu haka a kwamfuta ta.  Za ka samu Gimp a shafinsu dake: www.gimp.org

A karshe, idan kana bukatar manhajar sarrafa bidiyo da za na hoton bidiyo irin su: Cartoon misali, kana iya saukar da manhajar Blender kyauta ita ma, wacce ke shafinsu a www.blender.org.  Wannan manhaja ita ce kishiyar After Effects na kamfanin Adobe, wato kanwar Photoshop ce amma a bangaren sarrafa abubuwa masu motsi.  Sai dai After Effects ta kudi ce; tana da tsada matuka.  Bayan ita akwai kawayenta masu dan Karen tsada irin su: Maya, da kuma Cinema4D.

A takaice dai, muddin kana da kudi kuma za ka iya mallakar Photoshop, to, ita ce tafi kowacce kayatarwa.  Duk da cewa akwai wadanda aka yi fasakwaurinsu (Pirated) ana sayarwa a kasuwa.  Ba sa wuce naira dubu daya ko biyu.  Amma ban goyi bayan ka sayi irin wannan ba.  In da hali ka mallaki taka ta halaliyarka.  Idan babu hali, ga wadanda na zana maka nan, kyauta suke, kuma musamman idan makoyi ne kai, za ka fi samun saukin koyo a kansu fiye da wancan.  Ina maka fatan alheri.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik yaya aiki?  Don Allah a turo mini kasidar tsibirin bamuda ta adireshin Imel dina: ashamsu032@gmail.com.  Na gode.  – Shamsu Abdu, Rimi, Katsina.

Wa alaikumus salam, Malam Abdu Rimi barka dai.  Ina maka fatan alheri.  Kana iya zuwa shafin dake wannan rariyar don karanta kasidar da ka bukata, kai tsaye: https://babansadik.com/category/teku, sai ka gangara kasa kadan za ka ci karo da kasidar, daga na farko har zuwa kashi na uku.  Idan kuma kana son saukar da kasidar ne zuwa kan kwamfutarka, kaje wannan shafin: https://babansadik.com/dunkulallun-kasidu, sai ka gangara lamba ta 3, daga bangaren dama da taken kasidar za ka ci karo da wata alama shudiya mai suna: “Sauke”, kana matsawa za a saukar maka da kasidar a kan wayarka, kai tsaye.   Da fatan ka gamsu.  Na gode.


Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki?  Yaya dawainiya?  Allah Ya saka maka da gidan aljanna, amin.  Don Allah Baban Sadik yaya zan kwafi sako a Facebook daga wani wuri ya koma kan Wall dina , ya zama kamar ni ne na kirkireshi kai tsaye?  –  Sabo Magnet Tsakuwa: 08033622231

- Adv -

Wa alaikumus  salam, barka dai Malam Sabo Magnet.  Wannan abu ne mai sauki.  Kana iya neman izinin mai sakon kan cewa za ka yada shi a Wall dinka, wato: “Sharing” kenan.  Ko kuma, idan mai sakon abokinka ne kuna da kyakkyawar fahimta sai kace ya sa ka cikin masu “Yada” sakon, wato yayi “Sharing” da kai kenan.  Idan yayi haka, za ka ga sakon a kan shafinka kai tsaye, sai dai da sunansa ne, ba da sunanka ba.   Domin manhajar Facebook ta dauki hakkin mallaka da mahimmanci sosai.  Da zarar ka rubuta sako, to ya zama mallakinka.  Baza su taba ba wani wata dama ya mallaki sakon kai tsaye ba tare da kai ne ka sa shi cikin masu yadawa ba, ko ka amince masa ba.

Idan kaje ka matsa alamar “Share Post” daga sakon da wani ya rubuta, in dai hoto ne ba za ka ga hoton a kan shafinka nan take ba, sai an nemi iznin mai sakon tukun.  Idan ya amince, za ka gani.  Amma idan yaki amincewa, baza ka ga hoton a shafinka ba.  In dai rubutu ne kana iya yada shi ne

Hanya ta karshe dai tana da sauki, amma tana da hadari.  Ga ta kamar haka: ka shiga shafin wani sai ka ga sakon da ya birge ka.  Sai ka nado sakon (Highlighting), sannan ka kwafa (Copy), kaje shafinka ka zuba (Paste).  Da zarar ka matsa: “Publish Post”, nan take za ka ga sakon a shafinka, kamar kai ka kirkireshi.  Sai dai wannan hanya ce mai hadari. 

Na farko dai, idan kayi haka, to, ka mallaki abin da ba naka bane.  Domin mai asalin sakon bai san ka kwafa ba; sai in gaya masa kayi cewa za ka kwafa, kuma ya amince.  Abu na biyu, duk wanda yaga sakon a shafinka, alhali ya san asalin mai sakon, to, mutuncinka zai zube warwas.  Abu na uku, idan manhajar Facebook dake lura da dabi’u da mu’amalar mutane a dandalin ta gano ka, hakan na iya zama matsala a gareka.  Domin suna iya kulle shafinka baki daya.

A karshe dai, idan kana bukatar wani abu makamancin wannan, kawai ka zauna ka tsara rubutu daga kwakwalwarka.   Idan abin da ka gani ya birge ka, kana iya neman izinin mai sakon cewa zaka yada shi a shafinka.  Idan ya amince kuma ka yada a shafinka, sunansa ne zai bayyana ba naka ba, domin shi ne marubucin sakon.  Idan kana son sunanka ya bayyana, to, ka kirkiri naka sakon.  Da fatan ka fahimceni kuma ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.


Salaamun alaikum Baban Sadik, don Allah ina so ka turo mani kasidar da ka rubuta mai take: “Fasahar Binciken Bayanai a Google,” ta Imel dina dake: abdullahidanbaba@yahoo.com

Wa alaikumus salam, barka dai takwarana.  Da fatan kana lafiya.  Kamar yadda na sanar a baya dai, na tattare dukkan kasidun a gidan yanar sadarwa na musamman a Intanet, mai take: “TASKAR BABAN SADIK.”  Kana iya bin wannan adireshin don samun kasidar kai tsaye: https://babansadik.com/tsarin-neman-bayanai-a-intanet-2.  Idan kana bukatar kashi na dayan ne, da zarar ka kai can kasa daga hagu, za ka ga taken, sai ka matsa.  Allah sa a dace ya kuma kara fahimta, amin.


Salaamun alaikum Baban Sadik, game da waya nau’in iPhone 7 ce, idan misali ta samu matsala ta yadda sai an mata filashin na iTunes da iCloud, to, file za a canza mata kenan ko kamfanin zaka mayar su canza maka?  Ka mini bayanin wani mataki ya kamata mutum ya dauka.  –  Safiyanu Uba Manaba, Jigawa: 09063919460

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Safiyanu.  Ai in har ya zama wayar ta samu matsala ta yadda babu makawa sai an mata filashin, kamar yadda ka ayyana, hanya mafi sauki ita ce a kai wajen mai gyara ya duba.  Idan filashin ita ce waraka, sai a mata.  Sannan, filashin na iya zama farke babbar manhajar ce.  Wannan ya fi faruwa galibi a wayoyi masu babbar manhajar Android.  Akwai kuma nau’in filashin da ya shafi mayar da bayanan wayar su koma kamar yadda aka kera ta a farkon lamari.  Wannan shi ake kira: “Factory Reset.”  Wannan na biyun, a nawa fahimta, shi zai fi dacewa wa wannan wayar.

Ala ayyi halin, mai gyaran wayar zai duba don tantance abin da ya fi dacewa da ita kafin.  Allah sa a dace, ya kuma kara fahimta, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.