Sakonnin Masu Karatu (2017) (23)

Ci gaban sakonnin masu karatu. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

128

Salamun alaikum Baban Sadik, don Allah me yasa idan aka canza wa waya “file” ko “flashing” yake kin yi?  Domin ina da waya Samsung GLX4-Lite.  Idan na kunna ta sai ta rubuta: “Samsung glx4-lite”, amma daga nan ba ta sake nuno komai.  Na kaita wajen mai gyara an canza mata “file” ko “flashing” har sau uku, amma ba canji.  Daga Mukhtar I. Ya’u

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Mukhtar.  Daga bayanan da kayi zan iya fahimtar cewa matsala ce wayar ta samu a karon farko, daga baya aka kai wajen mai gyara aka mata filashin amma har yanzu ta kasa tashi.  A ka’ida, matsalolin wayoyin salula suna samuwa ne daga manyan bangarori guda biyu; da bangaren ruhi ko manhajarta, da kuma matsala ta bangaren gangar jikinta.  Matsalolin da suke da alaka da manhajar waya, musamman ma babbar manhajarta, wato: “Operating System,” ana iya gyara su ta la’akari da manhajar.  Idan komai yaki, da zarar an mata filashin shikenan, dole ta koma yadda take kamar ran da aka kera ta.  Domin shi filashin tsari ne dake kawar da dukkan wasu bayanai dake manhajar wayar gaba, ya mayar da hakikanin bayanan da wayar tazo dasu, a farkon lamari.

Bangaren matsalar waya na biyu kuma kan samu ne daga gangar jikin  wayar, kamar maballanta (Keypads), ko sipika, ko batir, ko kuma fuskarta, wato: “Screen” kenan.  Dukkan matsalolin dake da alaka da gangar jikin waya ana iya kawar dasu ne ta hanyar gyara gabar dake da matsalar.  Idan komai yaci tura, sai a cire (idan zai yiwu) a sa mata sabuwar gaba, don bata damar ci gaba da rayuwa.  Misali, idan wayar salula ta fada cikin ruwan zafi, mai zafi sosai.  Da wahala ta rayu.  Ma’ana, wannan lalur na iya kona hakikanin “shimfidar” injin wayar baki daya, wato: “Motherboard” kenan.  Idan kuwa haka ta faru, to zai yi wahala wayar ta sake farfadowa.

Don haka, shawarata ita ce, ka canza mai gyara ko kuma a kalla ka shawarci mai gyara maka wayar da ya duba dukkan bangarorin gangar jikinta, don tabbatar da lafiyarsu baki daya.  Kada ya dogara ga filashin dinta kadai.  Domin ba dukkan matsalolin waya bane ake iya magance ta su hanyar filashin.  Sai in sun danganci matsala ce da ta samo asali daga daya daga cikin manhajojin dake wayar.

Wannan ita ce shawarar da zan iya bayarwa.  Ina kuma maka fatan Allah sa a dace, amin.


Salamun alaikum Baban Sadik, sunana Mukhtar Ibrahim.  Don Allah ina so ka bani shawara akan littafin da zan nema wanda zai taimaka min don koyon “Programing” ta yaren Java.  Kuma da me da me ya kamata in nema?  Na gode.

Wa alaikumus salam Malam Mukhtar.  Koyon “Programming” abin so ne, domin fanni ne mai kayatarwa cikin fannonin kimiyya da fasahar sadarwa.  Ilimin “Programming” ya dada kayatarwa tare da habbaka na’urorin wayar salula da kwamfuta da kuma gidajen yanar sadarwa.  Koyon wannan ilimi yana bukatar hakuri, da juriya, da jajircewa da kuma sadaukar da kai da lokacinka.  Dangane da wane littafi za ka nema don koyon dabarun gina manhaja na “Java”, yana da kyau da farko ka san cewa, koyon wannan ilimi yana da madakai.  Na farko shi ne ya zama ka iya sarrafa kwamfuta, wajen kunnawa, da kashewa, da rubuta bayanai, da taskance su, da nemo su, da kuma iya mu’amala da shafukan Intanet wajen neman bayanai. 

Mataki na biyu shi ne ilimi kan “Programming”; me yake nufi?  Meye tarihinsa?  Nau’ukan dabarun gina manhaja nawa ake dasu?  Wanne ne ya kamata ka fara dashi?  Sannan, idan ka samu kwarewa a fannin gina manhaja ko “Programming” din, me kake son yi da ilimin?  Amsa wadannan tambayoyi daga zuciyarka, ba daga kwakwalwarka ba, shi zai taimaka maka wajen samar da tsari cikin abin da kake son aiwatarwa da ilimin.  Amma idan kawai kana son koyon “Java” ne don ka ji sunan ya shahara a bakin mutane, ko don ka ga wani ya yi, ko don kaji an ce da wannan yaren ne ake iya kera manhajojin wayar salula dake “Play Store”, sai kawai ka dauka kaima bari ka koya don ka iya kera manhajoji, to, wannan zai zama kuskure.  Kuma koyon yaren ta wannan dalili bazai sa ka fahimci komai a lamarin ba.

Mataki na uku shi ne, idan ka gama sanin wadannan abubuwa dake matakai na farko da na biyu da bayaninsu ya gabata, sai ka je matakin koyon harshe ko dabara ta musamman daga cikin dabarun gina manhajar kwamfuta.  Na ji ka ambaci yaren “Java”, tabbas yare ne mai kyau, kuma kashi 40 cikin manhajojin da ake amfani dasu na’urorin sadarwa da Intanet a yau, duk an gina su ne da yaren “Java”.  To amma ba nan gizo ke sakar ba.  Ga dan koyo wanda bai taba sanin me ake nufi da “Programming” ba, wannan zai zama tsallen-badake.  Don haka, ni shawarata it ace ka fara da kananan dabarun gina manhaja masu sauki, musamman wadanda ake amfani dasu wajen gina gidajen yanar sadarwa.

- Adv -

Misali, kana iya farawa da yaren “HTML”, da “CSS”, da kuma “JavaScript”.  Wadannan su ne manyan yarukan da ake amfani dasu wajen gina yanar sadarwa, na kwamfuta ko na wayar salula.  Idan ka mallaki kwarewa a wadannan fanno ko yaruka uku, koyon kowane irin yaren gina manhajar kwamfuta ko na Intanet bazai maka wahala ba.  Idan kuma ka dage kana son lallai ka fara gina manhajar kwamfuta ce kai tsaye, kana iya farawa da yaruka masu sauki irin su: “Python.”  Yare ne mai sauki, wanda ke amfani da karancin kalamai wajen baiwa kwamfuta umarni don gina manhaja.  Koyon Python zai taimaka maka kwarai musamman wajen kara cusa maka sha’awa da son fannin gina manhajar kwamfuta, wato: “Programming.”  Ba don komai ba sai don saukinsa, da kuma nishadin dake dauke dashi.

Ala ayyi halin, idan ma ka zabi ka koyi “Java” din ne kai tsaye, to, dole ne ka sadaukar da kanka, da kuma lokacinka, tare da karfafa zuciyarka wajen soyar da abin da kake yi gare ta.  Da wannan ne za ka samu cinma nasara.  Ina maka fatan alheri, tare da rokon Allah ya taimaka maka cikin dukkan abin da kasa gaba na alheri.


Assalamu alaikum, Abban Sadik, tare da fatan kana lafiya.  Dan Allah ta yaya ake bude sabon gidan yanar sadarwa?  Na jima ina so in koya amma har yanzu Allah bai yi ba. Daga Abbati Yaya!

Wa alaikumus salam Malam Abbati.  Barka ka dai.  Abin da nake iya fahimta daga tambayarka shi ne, kana so ne ka mallaki gidan yanar sadarwa, ta hanyar ginawa da hannunka ko kanka, kamar yadda a al’ada bahaushe ke fada.  Idan wannan ne manufarka, ga matakan hanyoyin nan.

Mataki na farko shi ne mallakar ilimin yin hakan, in dai da kanka kake son ginawa ba bai ka baiwa wani ya gina maka ba.  Amma idan kana son mallaka ne ta hanyar wani ya gina maka, kana iya tuntubata don tauttaunawa kan haka din.  Idan ka mallaki ilimin gina gidan yanar sadarwa, sai ka gina naka da kanka.  Shi ilimin gina gidan yanar sadarwa ya kasu kashi biyu.  Kana iya ginawa ta amfani da dabarun gina shafukan Intanet, irin su: “HTML” da “CSS” da kuma “JavaScript.”  Wadannan su ne yaruka uku dake baiwa mutum daman ginda shafin Intanet mai inganci, iya kwarewarsa.  Kashi na biyu kuma shi ne, kana iya amfani da ginannun kwarangwal din gidan yanar sadarwa na zamani da ake samunsu kyauta ko ta hanyar saya a Intanet, don kayatar dasu iya yadda kake so.  Wadannan kwarangwal dai madaukai ne da ake amfani dasu wajen tsarawa da kuma dora bayanan da ake son dorawa (zallan rubutu, da hotuna, da bidiyo da sauransu).  Kuma su ake kira: “Content Management System” ko “CMS” a gajarce.  Shahararru daga cikinsu sun hada da: “Bootstrap” da “Wordpress” da “Joomla” da dai sauran makamantansu.

Kana iya mallakar wadannan kwarangwal kyauta daga shafukansu (misali: www.wordpress.org/download) sannan ka tsara shafin a kan kwamfutarka. Da zarar ka gama, sai mataki na gaba.

Mataki na biyu shi ne, mallakar adireshi, wato: “Domain” kenan.  Wannan adireshi ne masu neman shafinka zasu rika shigarwa cikin rariyar lilo (Browser) don isa ga bayanan dake shafinka na Intanet.  Za ka yi rajistan wannan adireshi ne daga kamfanonin dake aikin rajistan adireshin yanar gizo a Intanet.

Sai mataki na uku, wato mallakar ma’adanar shafin gaba daya.  Wannan shi ake kira: “Web Hosting”, kuma shi ne tsarin dake dauke da dukkan bayanan da kowane gidan yanar sadarwa ke dauke dashi.  Da zarar ka mallaki wadannan abubuwa biyu, sai ka dora shafin da ka gina a mahallin da aka baka na “Hosting”, sannan ka nuna wancan adireshi da ka yi rajistansa a farko, zuwa ga mahallin da bayanan gidan yanar sadarwan ke dauke dasu. 

Wannan, a takaice, ita hanyar da ake bi wajen mallakan gidan yanar sadarwa.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    Masha Allah

Leave A Reply

Your email address will not be published.