Hira da BBC Hausa kan Bikin Ranar Tsaftace Intanet a Duniya (3)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 28 ga watan Fabrairu, 2020.

528

Kamar yadda muka fara kawowa a makonni biyu da suka wuce, yau ma za mu ci gaba da hirar da sashen BBC Hausa yayi dani don bikin Ranar Tsaftace Intanet a Duniya na shekara ta 2020, wanda ya gabata a ranar talata, 11 ga watan Fabrairu. A yau mun dauko ragowar hirar ce. A sha karatu lafiya.
—————
BBC Hausa: Za ka iya gaya mana wasu matakai ne masu amfani da Intanet za su dauka domin kare kansa daga wadannan shafuka (munana) da ma wasu shafukan da basu kamata ba? Musamman ganin cewa wasu lokutan kana cikin amfani da Intanet sai a rika maka tallan irin wadannan shafukan?

Baban Sadik: Abu na farko dai shi ne, mai mu’amala da fasahar Intanet ya zama yana da manufa. Mece ce manufarsa na amfani da fashar Intanet – a wayar salula ne ko a kwamfuta ne? Idan manufarsa bincike ne na ilimi, ko karatu don karuwar fahimta, ko kasuwanci yake yi ko kuma kawai don sadarwa ne. Abu mai mahimmanci dai shi ne ya zama yana da manufa. Kada ya zama don ya ga wasu na amfani da fasahar ne kawai shi ma yace bari yayi. Idan haka ya kasance, to, zai yi ta walagigi ne kawai.

Abu na biyu shi ne, bayan kasancewarsa yana da manufa, ya zama ya tabbata a kan wannan manufa tasa a kodayaushe. Duk wani abin da ba ya cikin manufofinsa, to yayi kokari ya kawar da kansa daga gare shi. In har ma zai yi mu’amala da wani abin da ba ya cikin manufarsa, to, ya zama wannan abu yana daga cikin abubuwan da za su taimaka masa ne wajen cinma wancan manufa tasa, ko kuma fadada fahimtarsa kan manufar da yake son cinma. A takaice dai, ya zama duk wani abin da ba shi da alaka da manufarsa, kada ya bashi wata mahimmanci.

Abu na uku shi ne, yayi kokarin wayar da kansa kan wannan fasaha ta Intanet. Ya tambayi kansa mece ce Intanet? Kuma daga ina wadannan shafuka da yake ma’amala dasu suke samuwa? Sannan ya rika tambayar kansa a kullum, shin, duk abin da nake gani ko nake ma’amala dasu a Intanet din nan daidai ne, ko akwai wasu abubuwan da ake sanya su da wata manufa (da ta sha banban da samar da fa’ida)? Domin bayanan da muke ma’amala dasu a Intanet sun kasu kashi uku ne: na farko akwai abin da yake tsantsar amfani ne; an zuba shi ne don samar da fa’ida ga mai ziyara ko ma’amala dashi. Na biyu kuma su ne nau’ukan bayanan da suke dauke da amfani da kuma cutarwa. Wadannan su ne galibin bayanan da suka shafi tallace-tallace misali, musamman a kafafen sada zumunta. Sannan na uku su ne nau’ukan bayanan da suke tsantsar cutarwa ne, babu wata fa’ida da suke bayarwa. Su kuma wadannan ba a ganinsu a ko ina, sai in kaje inda suke. Wannan shi ne hakikanin gaskiya. Musamman shafukan batsa; da wahala kana hawa Intanet kawai kaga shafukan batsa.

- Adv -

Eh, na yarda za ka iya cin karo da hotunan mata da dan tofi haka, ko kaga mace gashin kanta a bude haka (ko wani bangaren kirjinta a bayyane). Wannan ya faru ne saboda masu galibin wadannan shafuka basu yarda cewa mace ta rufe gashinta yana da wata alaka da ci gaban rayuwa ko addini ba. Ka ga wannan daban. Su a gare su wannan shiga ce ta al’ada. Amma kaga mace tsirara haka kawai a Intanet, (da wahala), sai in ka kutsa inda ke dauke da wadannan ire-iren bayanai. Haka ma duk wani abin da ya shafi hotunan bidiyo, in dai na batsa ne, to, za ka samu sai in mutum shi ya kai kanshi wannan wuri. Don haka dai a takaice, duk abubuwan da suke da alaka da harkoki na cutarwa irin su batsa, da irin wuraren da ake zambatar mutane da sauransu. To, za ka samu sai in mutum ne da kansa yayi mu’amala da masu ire-iren wadannan shafuka.

Abu na hudu shi ne, idan abota kake yi da mutane a shafuka ko ta manhajojin sadarwa irin su Whatsapp, da Facebook da sauransu, to, na farko dai tukun mu sani, Dandalin Facebook matattara ce wacce take babbar matattara (a Intanet). Daya daga cikin masana harkar sadarwa da kariyar bayanai (Information Security) mai suna: Graham Cluly – babban jami’i a kamfanin Sophos – yana cewa a duniyar Intanet gaba daya babu wurin da yafi hadari irin Dandalin Facebook. Babu wurin da ake da tarin mazambata, da ‘yan dagaji, da ‘yan ta’adda, da ‘yan kashe-mu-raba irin Dandalin Facebook. A takaice dai, Dandalin Facebook matattara ce dake dauke da duk wani bala’i da ka sani a duniyar Intanet. To, amma kai idan ka shiga wajen, me ke baka kariya ko rashin kariya? Su ne irin abokanan da kake ma’amala dasu. Idan mutanen kirki ne, shikenan. Amma idan ka sake ka kutsa kanka wancan wuri inda ‘yan rudu suke, to, duk wadancan abubuwa da Graham Cluly ya siffata, su ne zasu shafi mutum. Don haka, wannan kenan. Kasan inda za ka je, sannan da irin mutanen da zaka yi ma’amala dasu; idan wuri ne da ake tattaunawa misali.

Sannan (abu na biyar), idan kana ma’amala da mutane a wadannan kafafe na sadarwa irin su Whatsapp ko Facebook ko zaurukan Imel – irin su “Yahoo Groups” ko “Google Groups” – misali, yana da kyau ka san cewa, ba dukkan adireshin Intanet (Internet link) da aka aiko bane zaka latsa don ganin me ke ciki. Haka ba dukkan bayanan da aka aiko ko tunkudo zauren bane yake daidai. Akwai sakonni da yawa wadanda suke na bogi ne, wato: “Fake News”. Kai, a takaice ma dai, kusan kashi 70 ko 80 cikin 100 na sakonnin da ake musayansu a wadannan kafafe, duk sakonnin bogi ne. Duk galibin sakonnin da ake tunkudo su (Forwarded message), da yawa zaka samu wani kato ne ya zauna ya kirkiri wani labari don samar da wani yanayi da yake son ya shigar cikin kwakwalen masu karanta da sunan fadakarwa, ko wata harkalla ce ta kasuwanci da aka kawo da sunan “garabasa”, ko wata karya da aka yi wa Allah da ManzonSa aka lullubeta da sunan “falala” – ma’ana dai, karairayi ne zalla ake shiryawa. Abu ne sananne daman cewa labarun karya (Fake News) da sakonnin bogi (Spam messages) abubuwa ne guda biyu da suka fi komai addabar jama’a a duniyar Intanet, kuma ana amfani da wadannan kafafe ne wajen yada su cikin sauki.

Abu na karshe shi ne, mutum ya gaya wa kansa gaskiya. Idan kana gaya wa kanka gaskiya wajen mu’amala da wadannan kafafen sadarwa, to ba za ka samu matsala ba. Amma idan mutum bai gaya wa kansa gaskiya, kawai yana bin duk abin da yaga ya birge shi ne kawai, to, zai fada cikin bala’i. Allah sawwake.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.