Tsarin Fasahar Sadarwar Rediyo a Kimiyyance (1)

Bincike na musamman kan hakikanin fasaha da na’urar dake tafiyar da rediyo. Kasidun da muka gabatar a baya kan fasahar rediyo sun shafi tsarin shirye-shirye ne da yadda ake saurare. Amma wannan jerin kasidu da za mu fara daga yau, za su ta’allaka ne ga asalin fasahar dake samar da siginar rediyo, da yadda tasoshi suke samuwa, da kuma nau’ukannsu.

383

Gabatarwa

Shekaru kusan bakwai da suka gabata ne muka gabatar da wasu jerin kasidu kan nau’ukan hanyoyin sadarwa dake dauke kan yanar gizo na duniya.  A cikin wadannan kasidu dai mun kawo bayanai ne kan fasahar sadarwa ta Talabijin, da ta Rediyo, da kuma kafafen jaridun al’ada (Traditional Media), don nuna daya daga cikin kebantattun tasirin wannan fasaha ta Intanet wajen lakume fannonin rayuwa daban-daban.

A yau cikin yardar Allah ga mu dauke da jerin kasidu kan fasahar sadarwa ta Rediyo.  Za mu dubi wannan fasaha ne ta bangarori daban-daban; fannin kere-kere – yadda aka samar da na’urorin yada murya daga dakin labaru zuwa akwatin rediyon mai sauraro –  da fannin kimiyyar haske, wanda ya shafi hakikanin motar da ke daukar sautin mai yada labarai, cikin yanayin hasken maganadisu, da fannin sararin samaniya ta bangaren sadarwa – wajen la’akari da titin da sautin mai yada labarai ko gabatar da shirye-shiryen rediyo ke bi a sararin samaniya, da irin matsalolin da wannan sauti ke cin karo dasu (wato: Artificial & Natural Noise), sannan mu dubi fannin tarihi don sanin daga ina kalmar “Radio” ta samo asali?  Shin, kalmar Turanci ce ko wani harshen ne daban?  

In da hali har wa yau za mu dubi yadda akwatin rediyo ke iya cafko sautin shirye-shiryen rediyo daga sararin samaniya, da yadda na’urar “Tuned Circuit” ke iya lalubo tashar da mai sauraro ke nema, sannan, idan ta samo tashar, mu ga yadda take iya killace sauran tashoshi daga yin katsalandan ga mai sauraro idan yana sauraro.  A karshe, cikin dacewar Allah, za mu dubi wasu bangarorin sadarwa da hasken maganadisun lantarki ke taimaka musu wajen aiwatar da sadarwa, musamman fannin Talabijin da tsarin sadarwa tsakanin direban jirgin sama da masu bashi umarni daga filin saukan jirgi.

Wannan kasida za ta yi tsawo, don haka, kamar yadda muka saba, za mu kacalcalata zuwa bangarori daban-daban.  A yau za mu fara ne da bayani kan abin da yake jigo wajen sadar da sauti da mai sauraron rediyo ke ji ta akwatin rediyonsa.  Wannan jigo kuwa shi ne Haske; ma’anarsa, da yadda yake samuwa, da karkasuwarsa, da yadda yake iya daukan sauti don aikawa dashi, sannan a karshe mu duba nau’ukan haske da Allah ya ambata a cikin Al-kur’ani. 

Da fatan masu karatu za su ci gaba da kasancewa tare damu.


Ma’anar Haske a Kimiyyance

Kafin yin bayani kan tsari da samuwar haske, zai dace mai karatu ya samu bayanai kan ma’anar hakikanin haske; mene ne haske a ma’anance, cikin fannin kimiyya?  Malaman Fiziya (Physicists) sun bayar da ma’anar haske a bisa fahimta da bincikensu.  Inda suka ce abin da haske ke nufi shi ne: Samuwar sinadaran maganadisun lantarki masu bazuwa daga zango zuwa zango.  Wadannan sinadarai na maganadisun lantarki wadanda su ne hakikanin haske, ana iya ganinsu – wasu nau’ukan kuma ba a iya ganinsu.  Akwai bangaren da a ke iya gani, da kuma wani nau’in hasken da idanu basu iya riskarsa.  Akwai kuma nau’i na uku, wanda ya kamata a ce ana iya ganinsa, to amma saboda kaifi da tasirinsa, ido ba ya iya riskarsa.  A takaice dai, ko ana gani ko ba a iya ganinsu, wadannan sinadaran maganadisun lantarki su ne hakikanin abin da ake kira “haske”, ko Light” a turance.

Siffofin Haske

Kasancewar haske jiki ne kamar sauran samammun abubuwa  da ke wannan duniya tamu, akwai abubuwa guda hudu da ke tabbatar da samuwar haske ko yanayinsa a ko ina.  Abu na farko shi ne “kima.”  Haske yana da kima ko wani yanayi takamaimai na kauri ko rashinsa, wanda ke mamaye mahallin da yake.  Abu na biyu kuma shi ne maimaituwa.  Haske na maimaituwa ne daga wani mahalli zuwa wani, ko daga wani zango zuwa wani.  Hakan na faruwa ne a kan tafarkin da yake tafiya a ciki.  Sai abu na uku, wato watsuwa ko bazuwa.  Shi haske da zarar ya samu a wani wuri, yakan bazu.  Sai sifa ta karshe, wato mataki.  Yakan tashi daga wannan mataki zuwa wancan, a halin tafiya ko gudanuwarsa.  Wadannan su ne sifofi guda hudu da tsarin haske ya sifatu da su.

- Adv -

Daga Ina Haske Yake Samuwa?

Samuwar haske wani abu ne da ke ta’allake da wuraren da ke samar da shi.  Akwai mahallai guda uku manya da ke samar da haske da dukkan nau’ukansa.  Da bangaren da ake iya gani, da wanda ba a iya gani; duk ana samunsu ne daga wadannan wurare ko mahallai uku.  Mahalli na farko da ke samar da haske dai shi ne kowane irin “jiki mai wani mizanin zafi tabbatacce ko takaitacce”.  Misalin wannan shi ne gudar Rana wacce ke hasko mana haske a dukkan yini.  Hasken da ke samuwa daga halittar Rana nau’uka ne guda uku.  Akwai wanda idanu ba su iya ganinsa.  Wannan shi ne nau’in hasken makamashin Infra-red, mai dauke da zafi da ke samuwa daga jikin ranar.  Wannan shi ne kashi sittin ciki dari (60%) na bangaren abin da rana ke samarwa.  Sai kuma hasken da muke gani da idonmu daga rana.  Wannan nau’in shi ne ke dauke da sauran kashi arba’in (40%) na hasken da ke samuwa daga jikin rana.  Kashi na uku kuma shi ne haske mafi kaifi da rana ke fitarwa, wanda a harshen Turancin kimiyya ake kira: “Ultraviolet Light.”  Dukkan wadannan nau’ukan haske ana kiransu nau’in Thermal, a kimiyyance.

Mahalli na biyu da ke samar da haske a wannan duniya ta mu shi ne kwayayen lantarki (fari ne ko ja, da dukkan launukansa), ko kwayayen lantarki na mota  ko mashin ko dukkan wani mahallin lantarki irin na dan Adam da ke samar da haske.  Dukkan kwayayen da ke gidajenmu, da wadanda ke masallatanmu, da wadanda ke kasuwanninmu da kuma wadanda ke sauran wurare, kashi goma cikin dari (10%) na haskensu ne kadai suke fitarwa muke gani.  Sauran nau’ukan haske kashi casa’in (90%) din kuma duk zafi ne, kamar yadda na tabbata duk masu karatu na iya fahimtar haka daga kwayayen lantarkin da ke gidajensu.  Wannan zafi da ke samuwa daga wadannan kwayayen lantarki, duk nau’in haske ne na makamashin Infra-red.  Shi yasa ma idanu ba su iya riskarsu.  Wadannan nau’ukan kwayayen lantarki da nake Magana akai su ne wanda muka fi sani da: “Light Bulbs.”

Sai mahalli na uku da ke samar da haske, wanda shi ne hasken da ke samuwa daga konewa ko konannun abubuwa – sanadiyyar wuta ko duk abin da ke haddasa konewa tare da bayar da haske.  Wannan ya hada da konewar abubuwa sanadiyyar wuta na man fetur, ko gas, ko dizel, ko kananzir ko duk wani makamashi da ke haddasa wuta mai bayar da haske.  Wadannan makamashi da ke haddasa wuta mai samar da haske, su ke tabbatar da launin hasken da ke samuwa a yayin da konewar ke faruwa.  Wadannan, a takaice, su ne wurare ko abubuwan da ke samar da haske a irin yanayin da ya kamace shi.

Darajoji da Nau’ukan Haske

 

 

Dangane da daraja da nau’i, haske ya kasu zuwa kashi biyar.  Wannan rabe-rabe ya ta’allaka ne da yanayin kima, da launi, da bayyana – ana iya gani ko a a  –  da kuma tsarin da suke samuwa. Wannan har wa yau ya ta’allaka ne da tsarin gudun haske da maimaituwarsa. Wannan tsarin gudun haske da maimaituwarsa da ke samuwa a sararin samaniya, shi ake kira “Electromagnetic Wavelength”,  kuma yana da bangarori biyar ko shida, kuma kowanne daga cikinsu na da nashi aiki wajen taimaka wa dan Adam yin wani abu da zai amfane shi (idan ya binciko  kenan ko gane hakan), ko kuma iya cutar da shi ko mahallinsa.

Banganren farko shi ne tsarin haske mai dumi na lantarki mai takaitaccen maimaituwa, amma mai cin dogon zango idan aka yi amfani da shi wajen aikawa da sako na sauti.  Wannan shi ake kira Radio Waves, kuma da shi ne ake iya aikawa da shirye-shiryen gidajen rediyo da talabijin.  Da kuma shi ne har wa yau, ake amfani wajen gina na’urar hangen nesa da ke dukkan filayen jirgin sama, wato Radars.  Yana daukan dogon zango, amma yana da takaitaccen maimaituwa, wato Frequency Rate.  Sai kuma mai biye masa, wato tsarin haske mai tattare da dumi, mai taimakawa wajen dafe-dafe.  Da wannan tsari ake amfani wajen gina na’urar dumama abinci da sauran kayayyakin makulashe, wato Microwaves.

Sai kuma na uku, wanda haske ne da ke tattare da dumi da kuma launi, amma da shi da sauran tsarin hasken da suka gabata, dan Adam ba ya iya ganinsu da idonsa;  kasa suke da ganinsa; sai dai kawai yaji duminsu, iya kusancin da ke tsakaninsa da inda suke samuwa.  Wannan shi ne tsarin hasken da ake kira Infra-red, kuma ana amfani da shi wajen yin abubuwa da dama, ciki har da aikawa da sakonni a tsakanin kayayyakin sadarwa na zamani.  Sai tsarin haske na gaba, wanda ya kunshi shahararrun launuka bakwai masu bayyana a yanayin Bakan Gizo, wato Rainbow (Red, Orange, Blue, Yellow, Green, Indigo & Violet).  Wannan nau’in haske shi ne hakikanin haske da muke samu daga rana amma wanda ke riskarmu a wannan duniya da  muke ciki; tataccen haske kenan, wato Visible Light.  Wannan har wa yau shi ne nau’in hasken da ya keto sararin samaniya, har muke amfana da shi.

Bayan wannan sai kuma nau’in haske mai tsanani da ke samuwa daga rana; gundarin hasken kenan, wanda ke fitowa kai tsaye daga ranar.  Ba halittar da ke iya jure masa.  Wannan shi ake kira Ultraviolet Light, kuma yana da saurin maimaituwa wajen isa ga abin da ya hasko, mai cin gajeren zango.  Idan ya fito daga rana, akwai dabaka-dabaka da Allah Yai masa a sararin samaniya da ke tace shi, ya takaita mana haske da zafinsa zuwa nau’in hasken da muke iya rayuwa cikinsa.  Sai kuma hasken na’urar bincike ko hango cututtuka da ke jikin dan Adam ko halittu, wato X-Ray Light.  Wannan nau’in haske ne da ke cin gajeren zango, mai saurin maimaituwa don ya darkake duk abin da aka haska shi gareshi.  Da shi ake hasko illolin da ke damunmu galibi a asibitocinmu; da shi ake hango jarirai da lura da halin da suke ciki a mahaifa.  Wadannan, a takaice, su ne tsarin gudun haske da maimaituwansa da muke mu’amala da su a sararin wannan duniya da muke ciki.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.