Sakonnin Masu Karatu (2014) (8)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

80

Assalamu alaikum Baban Sadiq, ina maka jinjina ta ban girma da yabawa game da yadda kake wayar da kan al’umma ta hanyoyin sadarwa daban-daban kan fannonin da suka shafi kwamfuta da wayoyin salula.  Allah ya saka maka da alkhairi, ya kuma jikan iyaye. Sakamakon yadda kake wayar da kan jama’a akan wannan ilimi, wannan ya bani sha’awa matuka, ya kuma sa ni kwadayin wannan harka taka, musamman a irin wannan zamani.  Sai dai bansan ko kana da makaranta ta koyar da wannan sana’a ba.  Idan akwai, to don Allah ayi mini bayani; da kudinta da dokokinta.  In kuma babu, to ina rokonka da ka taimaka min in koyi wannan ilimi a wajenka.  Don koyon ilimi a hannun wanda ya goge irinka yana da matukar amfani ga dalibi me neman wannan ilimi.  Allah ya saka da alkhari.  Daga: Bukhari M. Barau

Wa alaikumus salam Malam Bukhari, da fatan kana lafiya. Ina godiya matuka da wadannan addu’o’i naka, tare da kyautata zato da kake mini kan kwarewa, duk da cewa na san iya haddin kokarina bai kai haka ba.  Allah saka maka da alheri amin.  Dangane da ko ina da makaranta, amsar ita ce: a a. Har yanzu ban assasa wata cibiya don gudanar da ire-iren wadannan al’amura ba, sai dai nan gaba.  Akwai wani wannan kuduri mai karfi in Allah yaso.  Amma, a tare da rashin sanin inda kake zaune, akwai makarantar Malam Salisu Webmaster dake Kaduna a Unguwar Sunusi.  Akwai cibiya ta musamman da aka dade ana horar da matsanmu kan wannan fanni mai albarka, tare da samun shedar karatu mai inganci, bayan kwarewa a aikace.  In har an dace kana kusa da nan, kana iya tuntuba ta don karin bayani.  Allah sa mu dace baki daya, amin.


Assalaamu Alaikum, tambayata ita ce: wai yaya ake aiki da “service” din blackberry zuwa kwamfuta.  Misali, ka hada service din blackberry ya rika aiki a kwamfuta ko Wi-Fi ne ko USB. Na gode.  Daga Tasiu Ali G/Dutse

Wa alaikumus salam Malam Tasi’u, da fatan kana lafiya.  Idan na fahimceka, kana son amfani da wayar Blackberry ne ta hanyar kwamfutarka; da dukkan hanyoyin sadarwa da ke tare da ita.  Idan kana bukatar amfani da wayar Blackberry ta kwamfuta sai ka saukar da manhajar Blackberry wadda ta dace da nau’in wayarka.  Idan sabuwar babbar manhajar Blackberry take amfani dashi sai ka saukar da BB10 Blackberry Desktop App. Idan kuma tsohuwar babbar manhajar ce irin su BB5, 6, ko 7 a misali, sai ka saukar manhajar BB7 Blackberry App.  Za ka samu wannan manhaja ce a shafin yanar sadarwar kamfanin Blackberry dake www.blackberry.com.  Idan ka gama saukarwa sai ka loda mata, wato “Install” kenan.  Sai ka jona wayar da kwamfutarka, don su hada alaka da juna.  A jikin wannan manhaja da ka loda mata ne za ka dukkan abubuwan da z aka iya aiwatarwa da wayar ta hanyar kwamfutarka, cikin sauki.

Daga ciki, za ka iya amfani da wayarka a matsayin makalutun sadarwa ta Intanet.  Wato wayar ta zama ita ce mai baka yanayin sadarwar Intanet a kwamfutarka.  Amma hakan fa ya danganci ingancin sadarwar kamfanin wayar da kake amfani da SIM dinsu ne, da kuma yawan data da ke wayar.  Idan babu data a layinka, ba za ka iya aiwatar da duk wani abu da ya shafi Intanet ba, sai dai musayar bayanai tsakanin wayar da kwamfutarka ko akasin hakan.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum. Ina maka fatan alhairi da fatan Allah ya kara basira. Tambayata ita ce; ni ina amfani da wayar Nokia nau’in E5 ne. To idan na saukar da manhajar 2go ba na iya shigar wa wayar. Duk sadda nayi kokarin loda mata sai a gaya min cewa: “Java failed…” ko “Authorisation failed…” da makamantan haka.  Kuma duk manhajojin wayar lafiya suke, amma wannan ne yaci tura. Na gode.  – Ahmad Lawal

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Ahmad. Ina godiya da addu’o’inku.  Wannan sako da kake gani yana nuna cewa wayarka ba za ta iya daukan nau’in bayanin da ka saukar ba kenan.  Ko dai saboda haka aka tsara ta, ko kuma saboda gurbacewar bayanan a sadda k agama saukar dasu.  Abin da “gurbatan bayanai” ke nufi, wanda a harshen kimiyyar sadarwa ake kira “Data Corruption” shi ne lalacewar bayanai a sadda ake kokarin saukar dasu ko ta’ammali dasu, sanadiyyar ko dai yankewar yanayin sadarwar Intanet a sadda ake saukar dasu, ko kuma tasirin kwayar cutar kwamfuta (Virus) dake cikin ma’adanar da aka taskance su a ciki ko aka saukar dasu a ciki.

- Adv -

Don haka, idan sadda kake kokarin saukar da manhajar 2go din yanayin sadarwar Intanet dinka ya yi ta yankewa, to, kana iya sake saukar da ita a karo na biyu, ta yiwu manhajar da ka saukar ta gurbace; wayar ba za ta iya sarrafa sub a balle ka amfana da hakikanin abin da bayanan ke wakilta na manhaja ko masarrafa don aiwatar da sadarwa.  Idan kuma ka sake saukarwa ba tare da matsala ba amma duk da haka wayar taki daukawa, to, alamar cewa manhajar bata dace da yanayin tsarin wayar ba kenan.  Wannan shi ake kira “Incompatibility” a ilimin kimiyyar sadarwa na zamani. Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya. Ga tambayata; idan na tura sakon Imail daga baya sai a aiko min cewa sakon bai je ba ga wanda na tura masa. Yaya zan yi da matsalar?  Daga Umar Adamu Biriboy

Wa alaikumus salam Malam Umar, barka ka dai.  A ka’ida, ya kamata a duk sadda aka aika sakon Imel, to, lalle ne ya tafi.  Amma idan ka samu sanarwar cewa “Sakon da ka aika bai isa ga wanda aka aika mas aba,” – wanda dole ne a sanar da kai dalilin – to, dalilan ba su wuce dayan abubuwa biyu; ko dai ya zama adireshin da kayi amfani dashi wajen aikawa ba daidai bane, ko kuma a a, daidai ne, sai dai an rufe shi.  Muddin aka aika sako zuwa adireshin Imel din da ba daidai bane, to masarrafar da ke karban sakonnin Imel din (Mail Server) za ta dawo dashi nan take, babu jinkiri.  Haka idan adireshin daidai ne, amma aka yi rashin sa’a an rufe jakar Imel din mai adireshin, wato “Deactivated” nan ma sakon zai dawo; tunda babu jakar Imel din a hakika.

Don haka, nan gaba sai a kiyaye.  A duk sadda za a rubuta sakon Imel, a tabbatar adireshin daidai aka rubuta shi, sannan a tambayi mai adireshin in za a iya, shin, yana amfani da Imel din ko a a?  Idan har ya dauki tsawon watanni tara bai yi amfani da Imel din ba, to lalle babu makawa an rufe.  Mafi karancin lokacin da ake rufe jakar Imel shi ne watanni shida.  Mafi tsawon lokaci kuma watanni tara.  Sai a kiyaye.  Da fatan ka gamsu da wannan takaitaccen bayani.


Assalamu alaikum, barka da dare da fatan kana lafiya.  Muna godiya akan kokarinka game da wayar mana kai akan harkar kwamfuta da waya.  Gaskiya biyanka sai Allah.  Tambayata a nan itace; don Allah Wi-Fi na aiki a Nijeria, kuma yana aiki a kan Android da Java?  Kuma don Allah yaya ake aiki dashi ko saita shi?  Da fatan za ka taimaka.  Allah ya baka ikon taimakawa.  Daga Lawal Ahmad

Wa alaikumus salam Malam Lawal, barka da warhaka. Ina godiya da addu’a, Allah saka da alheri, amin.  Dangane da tambayarka, lallai tsarin Wi-Fi na aiki kuwa a Najeriya, sannan kuma yana nan a kan wayoyi masu dauke da babbar manhajar Android, da Windows Phone, iOS na kamfanin Apple.  Ba ma wadannan kadai ba, hatta wayoyin salula na zamanin baya masu dauke da babbar manhajar Java da Symbian, akwai masu dauke da tsarin Wi-Fi.  Abin da Kalmar “Wi-Fi” ke nufi shi ne, “Wireless Frequency Radio,” wanda tsari ne dake killace yanayin sadarwa na zamani.

Idan kana son ganin wannan tsari a wayarka mai dauke da babbar manhajar Android, ka je: “Settings”, a bangaren “Network Connections” za ka ga wannan tsari, sai ka kunna shi.  Idan akwai na’urar Wi-Fi a inda kake, nan take wayarka za ta sanar da kai cewa: “Akwai tsarin sadarwar Intanet a nan, ta hanyar Wi-Fi.  Shin, kana a son a jona ka da shi?”  Idan kace eh, sai a jona ka.  To amma sai ba dukkan tsarin Wi-Fi yake kyauta ba.  Galibin wuraren da za ka je ka ci karo da wannan tsari za ka samu na wasu kamfanoni ne ko hukumar gwamnati, wanda dole sai an saita maka ta hanyar shigar da wasu kalmomi na sirri da suka kebanci kamfani ko hukumar da ke dashi.  Da faran ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.