Tsarin Sadarwar Wayar Salula (2)

Kashi na 12 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

242

“The Killer Application Theory”

Fahimtar manufa da ma’anar wannan ka’ida ta “Killer Application”, cikin harshen Hausa, na bukatar kyakkyawan misali a farko, kamar dai yadda muka kawo misali wajen bayar da ma’anar ka’idar “The Black Box” a baya.  Bayar da misali na daga cikin abin dake kara sa a fahimci abin daake Magana a kai.  Sanin kowa ne cewa wayar salula, a farkon al’amari, an kera ta ne don sadar da murya; ma’ana ka kira mutum kana jinsa, yana jinka, ku gaisa ta hanyar jin muryar juna.  Da zaran kun gama, ka kashe wayar.  Shikenan!  Amma bayan bullo da wannan hanya ta Magana da jin murya, da tafiya tayi nisa, sai masana kan wannan harka suka fara tunanin wasu hayoyi kuma da za su iya taimakawa wajen sadarwa, ba murya kadai ba.  Sai aka bullo da hanyar rubutu, irin na “text”, kamar yadda muke yi yanzu.

Daga nan kuma sai masana suka sake tunani, “me zai hana mu sake duba wata hanya, bayan murya da rubutu?”  Nan take aka samu sake bullowa da fasaha irin su na’uran daukan hoto (camera), na’urar daukan bidiyo (video recorder), na’urar daukan sauti/murya (voice recorder) da dai sauransu.  Ana cikin haka sai kuma wata fikira ta kara shigowa, cewa “me zai hana a taimaka ma mai amfani da wannan fasaha saukin aikawa da dukkan abin daya tanada na bayanai ta amfani da wadannan hanyoyin daukansu?”  Misali, idan ka dauki hoto, za ka iya aika ma wani dashi;  haka idan murya ka dauka ko sakon text ka rubuta.  Sai ba a tsaya a haka ba, masana suka sake tunani, cewa “ai tunda akwai wasu hanyoyin sadarwa irin su Fasahar Intanet da Talabijin da na’urar DVD Player da kwamfutoci, me zai hana a samo hanyar sadar dasu da wayar salula?”  Nan take aka bullo da na’urar “Universal Serial Bus” (USB Port), hanyar da za ta taimaka maka debowa da zubawa na dukkan bayanai daga wayar salularka zuwa kwamfuta ko gidan yanar sadarwa (Web Site), ko Talabijin da dai sauran su, ta hanyar jona wayar kebul a tsakani.

A yanzu na tabbata kowa zai amince idan nace ba hanyar sadarwa ta murya ce kadai ta kara ma wayar salula shahara da saukin saye da mu’amala ba, illa wadannan makale-makale da jone-jone da aka kara ma wayar daga baya.  To wadannan nau’ukan hanyoyin sadarwa da suka tsiru daga baya, suka kuma kara ma wannan fasaha ta wayar salula shahara da saukin mu’amala da ma araha, su ake kira “The Killer Application”.  Wannan ka’ida kuwa tana cikin dukkan hanyoyin sadarwa, kai hatta talabijin da rediyo.  Duk wani abin dayazo, kari a bisa manufar farko, kuma ya zama sanadiyyar samun shahara da inganci ga wani abin amfani, shi ake kira “Killer Application”. 

Don haka, hanyoyin daukan hoto da sadar dasu, da daukan murya da sadar dasu, da kuma daukan majigi (bidiyo) da sadar da shi, ta hanyar wayar salula irin ta yau, shi ake nufi da “Killer Application”, kuma tasirin sa ne ya kara ma wayar salula shahara da inganci da kuma saukin farashi.  Wannan ka’ida ta “Killer Application” ce ta haifar da dukkan tasirin da za mu yi Magana a kan su a yanzu.  Manyan dalilan kuwa su ne: murya, sakonnin text, hoto mara motsi, daukan sauti, daukan majigi da kuma hanyoyin mikawa da karbansu a tsakanin wayar salula da sauran hanyoyin sadarwa na zamani a yau.

Tasirin “GSM”

Tasirin fasahar sadarwa ta “GSM” a wannan kasa tamu abu ne da kowa ke iya sheda shi.  Gamammiyar tasirin wannan fasaha na kumshe ne cikin sadarwa, wanda ya kunshi dalilai da hanyoyi daban-daban.  Sadar da zumunci tsakanin mutane ya yawaita, wanda samuwar wannan a cikin kowace al’umma, alheri ne. Mutane da dama sun samu hanyar mika gaishe-gaishensu ga ‘yan uwa da abokan arzuka da ke nesa, wanda wannan bai samuwa ta dadi kafin zuwan wannan tsari, sam ko kadan.  Har wa yau, samuwan wannan fasaha ta “GSM” ya taimaka ma masu kasuwanci ta hanyoyi da dama.  Wasu ma basu da ofis, sam, daga lambar wayar su za ka same su, kuyi Magana, har ku hadu su maka abin dakake son ayi maka.  Ga wasu kuma wannan fasaha ta samar musu sana’a tsayayye, wanda kafin zuwansa basu taba mafarkin sa ba.  Za ka samu mutum ya gama makaranta, ga shedar karatun ga komai, amma bai da aiki.

- Adv -

Zuwan “GSM” ke da wuya sai sana’a ya samu.  Idan muka koma kan addini, sai mu ga kusan kowa (musulmai musamman) ya zama mai da’awa, musamman ma cikin watan azumi.  Wannan yafi yaduwa ta hanyar sakonnin “text”, kuma hakan abu ne mai kyau, don ya takaita ma malamai aiki sosai, ta wani bangaren fa amma.  Wasu kuma hanyar yada manufa da furofaganda kawai suka samu. Idan ana son aibanta wani ko wata al’umma ko wani, sai kawai a tsara sakon text mai zaki ko daci, iya gwargwadon batanci ko tallan da ake son yi, a ci gaba da yadawa.  Wannan hanya na da tasiri sosai, domin ba sai ka kira mutum ba, balle yaki amsa kiranka; da zaran sakon ya iso wayarsa shikenan, sai in gogewa zai yi, wanda kuma dole ne ya bude ya karanta abin dake ciki.

Ga wasu kuma wannan hanya ta sawwake musu hanyar karfafa sana’ar samartakan da ke tsakaninsu da ‘yan matansu.  Wasu sun yi ‘yan mata ta wannan hanya, wasu sun karfafa alakarsu da mata ko yan matansu, musamman ma ta hanyar tsarin Xtracool da kamfanin MTN ke bayarwa cikin dare.  Ga wasu kuma, kwarewa suka samu wajen fasahar gyaran wayar salula, cikin sauki.  Da dama sun dauki wannan a matsayin sana’a ne da suke cin abinci ta hanyarsa.  Akwai wasu hanyoyi har wa yau da wasu suka kirkira wajen caja wayoyin su, musamman fulanin da ke rugage, kuma masu amfani da wayar salula.

Makon jiya wani abokina ke bani labari cewa kasancewan basu da wutar lantarki, sai su samu fitilar hannu (torchlight), masu batura bibbiyu, guda biyu, sai su cire kawunansu duka, su sanya wayoyi a daidai inda ake sa kwan lantarkin (globe).  Daga nan sai su hade fitilun daga baya, su daure su ta yadda zai zama fitila guda, mai kawuna biyu, batura hudu.  Wayoyin da ke kan kowanne za su dauka su hade su biyu, don samun baki guda, wanda shi za su dofana a saman batirin wayar salula ko kuma su samu na’urar cajin waya (charger), su yanke kanshi, don hada shi da kan wayar da ke jikin fitilun, don caja wayar su.  Wannan fasaha ce abin alfahari, wanda ke nuna kwazon dan Adam wajen samo ma kansa mafita a yayin da ya samu kansa cikin matsala ko rashi.

Kada mu shagala, daga cikin tasirin da amfani da fasahar “GSM” ta hukumta ma al’umma, akwai iya rubutu da karatu.  Akwai da dama cikin mutane da na sani, wadanda ko dai basu iya rubutu da karatu cikin harshen Hausa ko turanci ba kafin su fara mu’amala da wayar salula, ko kuma basu iya takaita rubutu da kuma iya karanta takaitattun rubutu ba (shorthand), kafin haka.  Amma a halin yanzu duk sun iya, saboda tsananin shakuwa da wannan fasaha.  To duk bayan wannan, sai me?

Sai harkan shashanci da wasu suka mayar da wannan fasaha a matsayin wasila.  Wasu kuma ba abin dayafi musu sauki sai su sace maka wayar salularka, ko dai su sayar a arahar wulakanci, ko kuma su la’anta  maka ita.  Sace-sacen wayoyin salula ba wani abu bane mai wahala.  Wahalarsa kawai a ce baka ajiye galala ba.  Yanzu sai wani ya gyara ma wayar zama, ba ruwansa.   Wasu kuma zamba-cikin-aminci kawai suka iya, wato 419.  Za su yi kirdadon lambobin wayoyin jama’a, idan suka dace, sai suka buga maka su ce akwai wata ‘yar harkalla mai maiko.  Idan kabi nasu kuma shikenan.

Wasu kuma su aiko maka da sakonnin text, cewa kaci gasar tambola ko kacici-kacici da aka yi lokaci kaza.  Idan kana son karban la’adanka, ka aiko da katin waya na naira kaza, kazo waje kaza, lokaci kaza, a rana kaza, don karba.  Idan kabi nasu, wankin hula sai ya kai ka asuba, ba ma dare ba.  A takaice dai, wannan hanya ta fasahar sadarwa ta GSM ta kawo sauyi mai dimbin yawa cikin al’umma.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, mai karatu ya samu sanayya kan shigowan wannan fasaha ne da kuma yaduwarsa.  A karshe kuma bayani ya biyo baya kan tasirin da wannan yaduwa ya haifar cikin al’umma.  Idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa, za mu ci gaba, inda bayani zai zo kan hakikanin tsarin sadarwa a tsakanin wayoyin salula da kuma kamfanin da ke sadar da masu mu’amala.  Idan da abin daba a fahimta ba, don Allah a rubuto. Na kuma samu sakonnin masu karatu, kuma in Allah Ya so, za mu yi tsokaci kansu a makonni biyu masu zuwa, inda za mu sake zama don yin waiwaye adon tafiya kashi na uku.  A biyo mu!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.