Sakonnin Masu Karatu (2014) (15)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

78

Assalamu alaikum, ina so Malam yayi mini bayanin a kan Hotspot da ke zuwa a wayoyin zamani.  Daga: Muhammad Abubakar Damaturu, Yobe

Wa alaikumus salam, kalmar “Hotspot” na ishara ne ga wani takaitaccen “hurumin sadarwa ta Intanet a tsarin wayar iska” da wata wayar salula ke iya bayarwa don wata wayar salula ‘yar uwarta tayi amfani da shi don mu’amala da fasahar Intanet.  Wannan hurumi na samuwa ne a galibin wayoyin salula na zamani; daga wayoyi nau’in Blackberry zuwa Windows Phone da Android, duk sukan zo da masarrafar dake samar da wannan hurumi.  Kafin wata wayar salula ta iya amfani da wannan hurumi dake wata wayar salular, dole ne ya zama wayar da ke dauke da hurumin na da tsarin sadarwa ta Intanet, wato “Data Bundle” ko kuma “Data Subscription” idan wayar Blackberry ce.  Har wa yau, samun hurumi na iya yiwuwa idan wayar na jone da tsarin sadarwar wayar iska na wani kamfani, wato “Wi-Fi” ko “Wireless LAN Network.”

Abu na biyu kuma, sai an kunna ko zaburar (Activate) da wannan tsari a jikin wayar da ke dauke dashi.  Sannan dole ne ya zama wayar da zata jonu da wannan hurumi ta mallaki tsarin mu’amala da Intanet ta wayar iska, wato “Wi-Fi,” sannan kuma dole ne mai wayar ya kunna, don neman wani hurumin sadarwa da ke kusa dashi.  Muddin hurumin a kunne yake, da zarar ya nemo (Search) zai ga hurumin ta amfani da sunan wayar dake dauke dashi.  Daga nan sai ya matsa sunan wayar, wancan wayar za ta sanar da mai wayar cewa: “Wance (sunan waya) na neman shiga huruminki na sadarwar Intanet, a barta ta shigo?”  Idan mai wayar ya amince, sai ya zabi tsarin da yake so wancan wayar ta bi wajen amfani da hurumin.  Idan yana son tsari ne tsararre (Secured), dole sai ya rubuta wasu lambobi, sannan ya sanar da mai wancan wayar cewa ga lambobin.  Wayarsa za ta sanar dashi cewa: “Wannan hurumi fa tsararre ne, kana da kalmomin sirrin shiga?”  Idan yace eh, sai ya shigar.  Da zarar ya shigar sai kawai wayarsa ta samu tsarin sadarwa na wayar iska don mu’amala da fasahar Intanet.  Wannan, a takaice, shi ne abin da ake kira “Hotspot” kuma da fatan ka gamsu.


Salamun Alaikum Baban Sadik, da fatan iyali lafiya.  Don Allah akwai hanyar da zan bi in maido akwatin Imel din Yahoo di na da aka rufe min kusan shekara guda amma kuma ina amfani dashi a Facebook?  Daga: 08028338892

Wa alaikumus salam, barka dai.  Wanann ke nuna cewa an dakatar da wannan akwatin Imel din naka kenan, wato “Deactivated,” kuma kana iya dawo dashi ne ta hanyar shiga.  Idan ka bukaci shiga, za a sanar da kai halin da akwatin ke ciki.  Galibin gidajen yanar sadarwa masu dauke da manhajar Imel irin su Yahoo!, da Hotmail, da Gmail, sukan bayar da tazarara na musamman kafin su rufe, kuma za su ta aiko maka da sako kan haka.  Idan ka share su shikenan, sai su rufe.  Gmail kan bayar da watanni 9 ne kafin su rufe.  Hotmail kan bayar da shekara daya ne. A yayin da Yahoo! kuma ke bayar da tazarar watanni 8.   Idan an rufe, a duk sadda ka bukaci a bude maka suna budewa.  Amma idan tazarar lokaci ya wuce shekara, ko shekaru 2 misali, galibi sukan goge akwatin gaba daya (Delete), sai su saki sunan (username) ga duk mai bukata, sai a bashi.  Wannan shi ake kira “Username Recycling,” kamar  yadda kamfanonin waya suke yi su ma, ga duk wanda ya daina amfani da layinsa na tsawon lokaci.

Duk da cewa an kulle akwatin naka, wannan bai hana ka iya amfani dashi wajen shiga shafinka na Facebook, amma na san ka bude shafin Facebook dinka ne tun kafin a rufe wancan akwatin Imel din naka.  Idan kana son ci gaba da amfani dashi kana iya gyara shi, domin a duk sadda shafinka na Facebook ya samu matsala, kuma kana son ka warware, to, can za su tura maka sakon Imel don gyara matsalar.  Ka ga idan kuma an riga an rufe, sakon ba inda zai je, kuma wannan ke nuna matsalar ba za ta warwaru ba kenan.  Don haka, ko dai ka cire adireshin wannan Imel a shafinka na Facebook ka sa lambar wayarka ko wani sabon adireshin Imel, ko kuma ka gyara wancan da aka kulle.  Allah sa a dace, amin.


- Adv -

Assalamu alaikum, Ina son karin bayani akan nau’ukan kwamfutoci na musamman, wato “Specialised Computer Systems.”  Daga: Fahad Musa, Sokoto

Wa alaikumus salam, Malam Fahad barka ka dai.  Su “Specialised Computer Systems” dai nau’ukan kwamfutoci ne na musamman da ake kera su don aiwatar da wasu ayyuka na musamman musamman a fagen binciken ilimi, da fagen sararin samaniya, da fegen harkar lafiya, da fagen yada labarai da dai sauransu.  Kwamfutoci ne amma galibi ba su da siffofin zahiri da muke ganin ire-iren wadannan kwamfutoci da muke amfani dasu.  Galibinsu ma gingimarayen kwamfutoci ne, wato “Main Frame Computers,” wadanda wasu hukumomi ko kasashe ko kamfanoni ke amfani dasu wajen aiwatar da ayyuka na musamman.

Galibin kwamfutocin da kamfanin kera kwamfuta na IBM ke kerawa duk kwamfutoci ne na musamman.  Daga cikinsu akwai jerin kwamfutocin da ya kera masu suna “Blue Gene” da dukkan nau’ukansu.  Sannan akwai nau’in kwamfuta ta musamman da kasar Sin ta kera cikin shekarar da ta gabata (2013) mai suna “TIANHE-2” wacce ke dauke da mizanin ma’adana (Storage) mai girman Perabyte 12 (wato Terabyte 12,000), da na’urar “Processor” sama da miliyan daya, sannan a kalla tana bukatar makamashin lantarki da ya kai Kilowat dubu goma sha bakwai (17,000 Kw).

A takaice dai farashin wannan kwamfuta ya kai dalar Amurka miliyan 380, kwatankwacin naira Biliya sittin da shida da miliyan dari uku kenan (N66.3B).  Wannan duk kudin kwamfuta guda daya ne, kuma gari guda ne, ba kwamfuta ce da za ka siyo ka dauko a jaka ba.   A duk duniya ita ce kwamfutar da tafi tsada a halin yanzu.  Da fatan ka gamsu.


Salaamun alaikum, Malam yaya mutum zai yi domin ya kiyaye daga kamuwa da kwayar cutar kwamfuta (Virus)?  Daga:  Muhammad Rimaye, Kaduna

Wa alaikumus salam, abin da ake bukata shi ne, ka sanya mata masarrafar tace kwayoyin cutar kwamfuta, wato “Anti-Virus Software,” ka zama mai kiyayewa wajen amfani da ma’adanar shigar da bayanai (irin su Flash Drive dsr), bayan haka, idan kai mai yawan mu’amala da fasahar Intanet ne a kwamfutar, ka zama mai kaffa-kaffa wajen wurararen da kake shiga.  Kada ka rika bude makalutun sakon Imel (Email Attachment) sai ka san daga wajen wa sakon ya zo kuma ka amintu da shi.  In da hali, a duk wata ka rika tace bayanan da ke kwamfutar ta amfani da wannan masarrafa, wato “On Deman Scan” kenan.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.