Sakonnin Masu Karatu (2014) (11)

Kamar kullum, yau ma za mu duba taskar sakonninku ne. A sha karatu lafiya.

88

Sakonninku

A yau kuma cikin yardar Ubangiji ga mu dauke da wasu daga cikin sakonnin masu karatu, kamar yadda aka saba. Tsawon wannan lokaci da ya gabata na samu sakonninku masu dimbin yawa; da wadanda kuka aiko ta hanyar tes, da wadanda kuka aiko ta hanyar Imel, sai wadanda kuke rubuto mini ta shafina da ke Dandalin Facebook (www.facebook.com/babansadik).  Galibin sakonnin da ke bukatar amsar gaggawa, kuma suka dace da yanayin da ba na cikin shagulgula, nakan amsa su nan take ba bata lokaci, musamman wadanda suka kebanci bukatar kasidun baya, da wadanda ake gani a facebook inda nake sakawa lokaci zuwa lokaci, da kuma wadanda ake gani a Mudawwanar Kimiyyar Fasahar sadarwa (http://fasahar-intanet.blogspot.com), duk da cewa na kwana biyu ban zuba kasidun ‘yan watannin da suka gabata ba. 

Don haka, sakonnin da ke dauke a nan, wadanda na amsa su yanzu, duk sakonnin tes ne.  Ina bayar da hakuri ga wadanda suka so a ce sun samu amsar tambayoyinsu ko bukatar karin bayani kan wani abu da na rubuta, cikin gaggawa, amma hakan bai yiwu ba. Kamar yadda na sha fada; akwai mantuwa, akwai shagala sanadiyyar aiki, sannan kuma wasu lokuta dole ina bukatar aiwatar da bincike ga tambayoyin da ke dauke da sarkakiya a cikinsu. Yin hakan na da muhimmanci, musamman ganin cewa da yawa cikin masu karanta wannan shafi dalibai ne ‘yan uwana a jami’a ko makarantun gaba da sakandare.  Akwai bukatar tantancewa kan duk amsar da za a bayar don kaucewa jefa dalibi ko mai tambaya daga neman sani mai inganci zuwa rudani.

Haka kuma, ga wadanda suka saba mu’amala da Dandalin Facebook, akwai shafi na musamman na bude don zuba kasidun da nake rubutawa a nan, da amsa tambayoyin masu karatu, tare da dukkan wasu bayanai da suka shafi harkar sadarwa ta zamani, da shirye-shiryen da nake gabatarwa a Tashar Sunnah TV a duk ranar Litinin. Ga adireshin shafin kamar haka: www.facebook.com/kimiyyadafasaharsadarwa ko kuma idan ka shiga shafinka, ka gangara kasa inda aka rubuta “Search” sai ka rubuta Dandalin Kimiyya da Fasahar Sadarwa za a kaika shafin, sai ka matsa “Like.”  Da zarar ka yi haka, to duk sadda aka zuba wasu bayanai a shafin, za ka rika ganinsu kai tsaye. 

A karshe, ina sanar masu karatu cewa daga wannan mako na canza layin waya, wanda zan rika karbar sakonninku kadai, daga wadda ke sama zuwa wannan layi: 08021225082. Kuma a kiyaye, wannan layi ne na tes zalla, ba a karbar kira daga gare ta. Duk wanda ya bugo ba a dauka ba kada yaji haushi. Wancan layin sai a goge ta; musamman ga wadanda suke da ita a wayoyinsu.  Ta sabuwar layin da na bayar a sama ce kadai za a rika turo sakonni. Allah sa mu dace baki daya, amin.


Salaamun alaikum, ina maka fatan alheri da jinjina a gare ka.  A gaskiya babu abin da za mu ce a gare ka sai dai Allah Ya biya ka.  Domin kasidarka mai taken: “Hanyoyin Inganta Al’umma ta Hanyar Kimiyya da Kere-kere” ta taba kowane fanni.  Domin na dade ban karanta kasidar da ta birgeni ba irin wannan kasida.  Sannan kuma ta sanya ni kara jajircewa.  Allah saka da alheri.  Daga: Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Gidan Mai mangwaro.

- Adv -

Wa alaikumus salam, ina matukar farin ciki da jin cewa wannan kasida ta kayatar da kai. Allah sa hakan ya zama tafarkin ci gaba a gare ka da al’umma baki daya. Na gode matuka, a ci gaba da karfafa mu, don samun kwarin gwiwa a ko yaushe.  Na gode matuka.


Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da kokari.  Da fatan Allah ya saka maka da mafificin alherinsa, amin.  Shin, a kimiyyance ko akwai wani amfani da rayuwar dan adam ke amfanuwa da shi daga itatuwa?  Daga:  Aliyu Ibrahim Zawiyya, Gusau.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aliyu.  Idan na fahimceka, kana son sanin fa’idar da samuwar bishiyoyi ke da ita ne a bangaren lafiya ko ince a kimiyyance, bayan fa’idar tattalin arziki, da na tsaro.  Akwai fa’idoji sama da ashirin da masana kimiyya suka tantance dake samuwa daga bishiyoyin da ke muhallinmu a kullum.  Daga cikinsu akwai tsabtace iskar da muke shaka a kullum, sanadiyyar kamewa da daure kura da suke yi a duk sadda kura ke kadawa.  Akwai samar da iskar shaka, wanda wani bangare cikin abin da ke taimaka wa dan adam rayuwa a doron wannan kasa.  Malam kimiyya sun tabbatar da cewa a shekara guda, gungun itatuwa ko bishiyoyi da ke tare a fadin kasa eka guda na iya baiwa mutane 18 iskar shaka su rayu.

Har wa yau, samuwar bishiyoyi a muhallinmu na taimakawa wajen sanyaya yanayi.  Wannan na faruwa ne sanadiyyar inuwa na musamman da bishiyoyi ke samarwa da ganyayyakinsu.  Bayan haka, samuwar bishiyoyi a muhalli na taimakawa wajen kare kananan yara daga matsanancin sinadarin zafin rana (Ultraviolet Rays).  A karshe, kariya ne wajen hana zaizayar kasa.  Wadannan kadan ne daga cikin fa’idojin da samuwar bishiyoyi a muhalli ke samarwa, da fatan ka gamsu.


Salaamun alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alheri a koda yaushe.  Don Allah ina son gamsasshen bayani a kan wayar salula nau’in BlackBerry Z10.  A baya na yi amfani da nau’in Galaxy 2 mai dauke da babbar manhajar Android.  Sannan ina son sanin bambancin da ke tsakanin BlackBerry da Samsung Galaxy 2?  Na gode: Sameer Ibrahim Kano, 08037310464

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Sameer.  Wayar salula nau’in Blackberry Z10 dai tana dauke ne da sabuwar babbar manhajar Blackberry 10, sabanin sauran da suka gabaceta masu dauke da zubin Blackberry 6 ko Blackberry 7.  Wannan sabuwa kuma babbar manhaja tsarinta ya sha bamban da wadanda suka gabata. A yayin da za ka iya sayan layin mu’amala da Intanet mai bai-daya (wanda ya hade BB Chat da dukkan hanyoyin mu’amala da Intanet da Imel) a tsohuwar babbar manhajar, a wannan dole sai ka sayi layin shiga Intanet nau’i biyu.  Na farko za ka sayi data ne, sannan kuma ka biya kudin layi na wata ko mako daya ko biyu, don yin mu’amala da manhajar BB Chat in kana so.  Bayan haka, akwai bambance-bambance a bangaren kananan masarrafar wayar wadanda suka sha bamban da na babbar manhajar baya.

A daya bangaren kuma, bambancin da ke tsakanin Blackberry da Samsung Galaxy da dukkan nau’ukanta dai shi ne: kamfaninsu dai ba daya bane. Blackberry na kamfanin Research in Motion (RIM) ne, a yayin da Samsun Galaxy kuma na kamfanin Samsung ne.  Babbar manhajar Samsung Galaxy ita ce Android, a yayin da babbar manhajar Blackberry kuma ita ce Blackberry OS.  Wadannan, a takaice, su ne manya kuma muhimman bambancin da ke tsakaninsu.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.