Fasahar “Digital Currency”: Tarihin Hada-Hadar Kudi a Zamunnan Baya (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 26 ga watan Maris, 2021.

476

Tarihin Hada-Hadar Kudi: Tsakanin Jiya da Yau

Malaman tarihin hada-hadar kudi da cinikayya da tattalin arziki sun tabbatar da cewa abin da yake asali wajen samuwar kudi ya samo asali ne daga bukatar dan adam ga wani abu na rayuwa wanda ba shi da shi.  Wannan ne ya tirsasa shi neman abokan mu’amala da zai samu abin da yake so daga gare su.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, babu wani dan adam da aka halicce cikin wadatuwa na abin da yake bukatar da gudanar wa da rayuwarsa dashi.  Hakan ne kuwa ya ja masa neman abokin kasuwanci ko hulda, wanda zasu fahimci juna, don ba shi damar samun abin da yake bukata na abinci ne, ko tufafi, ko wurin zama, daga wajen wani wanda shi kuma wani abin daban yake nema.

Tsarin Bani-Gishiri-In-Baka-Manda (Barter System)

Wannan bukatuwar ce ta kawo dan adam ga wani tsarin hada-hadar kasuwanci na “bani-gishiri-in-baka-manda”, wanda a harshen turanci ake kira: “The Barter economy” ko “Barter system”.  Tsari ne da ya kunshi mutane biyu, kowannensu da na neman abin da samu ne ta hanyar musayar abin da ya mallaka.  Misali, sai a samu mutumin dake da sukari, yana son gishiri.  Sai ya ba sukarin, ya karbi gishirin daga wajen wanda ya bashi sukarin.  Sai dai kuma wannan zamani ko tsari bai dawwama ba, saboda matsalolin da yake dauke dasu.  Mafi girmar kalubalen da tsarin ke dauke dashi kuwa shi ne, kana iya neman mai madara, ya zama shi zuma yake so, kai kuma sukari kake dashi.  Ka ga a nan, musayar haja zai yi wahala.  Domin bazai baka madara shi kuma ya karbi abin da ba shi yake bukata ba.  Daga nan mutane suka fara tunanin wani tsari mai sauki da armashi.

Tsarin Zinare da Azurfa (The Gold Era)

- Adv -

Wannan ya kawo mu zamanin cinikayya ta amfani da zinare da azurfa.  Wannan tsari shi ake kira: “The Gold Era”.  Karkashin wannan tsari dai jama’a da dauloli sun amince a tsakaninsu ne su rika aiwatar da cinikayya ta amfani da zinare da azurfa a matsayin kudi.  Wadannan hajoji guda biyu – wato zinare da azurfa – su ne asalin kudi.  Wannan ittifaki ne tsakanin malaman shari’ar musulunci da malaman hada-hadar kudi na zamanin yanzu.  Wannan yasa dauloli a wancan lokaci suka dandaka zinare zuwa adadin kima daban-daban.  Misali, a kasashen larabawa, akwai dinari, da dirhami, wadanda zallar zinare da azurfa ne aka yi kwandala ko silallansu, don baiwa mutane damar aiwatar da cinikayya, da biyan hakkokin aiki, da saye da sayarwa, da kuma taskance kimar arziki a yanayi daban-daban.  Har wa yau, wannan tsari ya ba da damar taskance zinare da azurfa a matsayin kudade da kowa ya yarda dasu.  Sannan tsari ne ya baiwa zinare da azurfa daraja biyu.  Na farko dai kudade da ake iya cinikayya dasu.  Na biyu kuma, kadarori ne (Commodities) da za a iya ajiye su a matsayin kadara.  Wannan, a cewar masana, shi ne zamani mafi mahimmanci a tarihin kudi da hada-hadar kudade a duniya.  Domin shi ne zamanin da ya samar da asalin duk wani hada-hadar kudade da ake yanzu a duniya.

Tsarin Banki (Banking System)

Kasancewar zinare da azurfa kudade ne kuma kadarori ne, wannan yasa duk wanda ya mallakesu, to fa, yana da bukatar wurin ajiyesu.  Kuma ganin cewa abubuwa ne masu kimar gaske, domin bayan matsayi da suke dashi wajen tattalin arziki da kasuwanci, kayan alatu ne a bisa karankansu.  Wannan yasa mutane suka fara neman inda za su rika adana don kauce wa salwantarsu.  Kamar yadda bayani ya gabata a baya, a wasu dauloli shugabanni ne suka jibinci sarrafa zinare da azurfa don amfani dasu a matsayin kudade.  A kasashen turai su kuma an samu wadanda suka bude shaguna ko abin da yanzu a iya kira da ofishi, don karbar ajiyar zinare da azurfar jama’a, ga mai bukatar a ajiye masa.  Da zarar ka zo da zinarenka ko azurfa wajen mai ajiya, zai karba, sai ya rubuta takarda mai dauke da bayanin sunanka, da kwanan watan ranar da ka kawo ajiyar, da adadin da kazo dashi (ma’ana wajen nauyi ko adadin silalla, idan kwandaloli ne ka kawo ajiya).  A duk sadda ka tashi bukatar zinarenka ko wani adadi na abin da ka kawo ajiya, sai kazo da wancan takarda da aka baka, ka mika, a baka kayanka.

Da tafiya tayi nisa sai gwamnatoci suka kirkiri nau’in takardun kudi don saukaka mu’amala, suka zama sune makwafin zinare da azurfa.  Sai ya zama ana buga takardun kudi ne iya yawa da kimar duwatsun zinare da azurfa da ke ajiye wajen masu ajiyan nan.  A hankali sai tsarin ya sake rikidewa zuwa amfani da zallar takardun kudi gaba daya.  Hukumomi suka bude bankunan hukuma (Central Banks), wadanda sune ke da hakkin baiwa ‘yan kasuwa dama da lasisin bude bankunan kasuwanci a kasa (Commercial Banks), don sawwake tsarin hada-hadar kudi a kasa.

Wannan sabon tsari da ya bullo a kasashen turai a wancan lokaci, shi ne ya rikide ya zama tsarin banki da muke dashi a halin yanzu.  Wancan takarda da ake baiwa mai ajiya a baya, ita ce aka mayar da ita a matsayin takardar cak (Cheque Book), da takardar ajiyar kudi (Deposit Slip), da na ciran kudi (Withdrawal Slip), da kuma katin ATM da muke amfani dashi yanzu.  Wannan shi ne tsarin hada-hadar kudi na banki, wato: “Banking System”.  Kuma takardun kudin da muke amfani dasu yanzu su ake kira: “Fiat Currency”, saboda hukuma ce kadai ke da ikon buga su, da kara yawansu, da rage yawansu; iya gwargwadon yadda take ganin maslaha ne ga al’umma.  Abin da wannan ke nunawa dai a takaice shi ne, karkashin wannan tsari na hada-hadar kudi, dole ne sai an samu bankuna, domin su ne masu dillacin kudade – wajen karba, da bayarwa, da lamuni da sauransu.  Sannan hukuma ce kadai ke da hakkin buga kudade.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.