Sakonnin Masu Karatu (2014) (10)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

68

Assalamu alaikum. Ina maka fatan alhairi da fatan Allah ya kara basira. Tambayata ita ce; ni ina amfani da wayar Nokia nau’in E5 ne. To idan na saukar da manhajar 2go ba na iya shigar wa wayar. Duk sadda nayi kokarin loda mata sai a gaya min cewa: “Java failed…” ko “Authorisation failed…” da makamantan haka.  Kuma duk manhajojin wayar lafiya suke, amma wannan ne yaci tura. Na gode.  – Ahmad Lawal

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Ahmad. Ina godiya da addu’o’inku.  Wannan sako da kake gani yana nuna cewa wayarka ba za ta iya daukan nau’in bayanin da ka saukar ba kenan.  Ko dai saboda haka aka tsara ta, ko kuma saboda gurbacewar bayanan a sadda k agama saukar dasu.  Abin da “gurbatan bayanai” ke nufi, wanda a harshen kimiyyar sadarwa ake kira “Data Corruption” shi ne lalacewar bayanai a sadda ake kokarin saukar dasu ko ta’ammali dasu, sanadiyyar ko dai yankewar yanayin sadarwar Intanet a sadda ake saukar dasu, ko kuma tasirin kwayar cutar kwamfuta (Virus) dake cikin ma’adanar da aka taskance su a ciki ko aka saukar dasu a ciki.

Don haka, idan sadda kake kokarin saukar da manhajar 2go din yanayin sadarwar Intanet dinka ya yi ta yankewa, to, kana iya sake saukar da ita a karo na biyu, ta yiwu manhajar da ka saukar ta gurbace; wayar ba za ta iya sarrafa sub a balle ka amfana da hakikanin abin da bayanan ke wakilta na manhaja ko masarrafa don aiwatar da sadarwa.  Idan kuma ka sake saukarwa ba tare da matsala ba amma duk da haka wayar taki daukawa, to, alamar cewa manhajar bata dace da yanayin tsarin wayar ba kenan.  Wannan shi ake kira “Incompatibility” a ilimin kimiyyar sadarwa na zamani. Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya. Ga tambayata; idan na tura sakon Imail daga baya sai a aiko min cewa sakon bai je ba ga wanda na tura masa. Yaya zan yi da matsalar?  Daga Umar Adamu Biriboy

Wa alaikumus salam Malam Umar, barka ka dai.  A ka’ida, ya kamata a duk sadda aka aika sakon Imel, to, lalle ne ya tafi.  Amma idan ka samu sanarwar cewa “Sakon da ka aika bai isa ga wanda aka aika mas aba,” – wanda dole ne a sanar da kai dalilin – to, dalilan ba su wuce dayan abubuwa biyu; ko dai ya zama adireshin da kayi amfani dashi wajen aikawa ba daidai bane, ko kuma a a, daidai ne, sai dai an rufe shi.  Muddin aka aika sako zuwa adireshin Imel din da ba daidai bane, to masarrafar da ke karban sakonnin Imel din (Mail Server) za ta dawo dashi nan take, babu jinkiri.  Haka idan adireshin daidai ne, amma aka yi rashin sa’a an rufe jakar Imel din mai adireshin, wato “Deactivated” nan ma sakon zai dawo; tunda babu jakar Imel din a hakika.

- Adv -

Don haka, nan gaba sai a kiyaye.  A duk sadda za a rubuta sakon Imel, a tabbatar adireshin daidai aka rubuta shi, sannan a tambayi mai adireshin in za a iya, shin, yana amfani da Imel din ko a a?  Idan har ya dauki tsawon watanni tara bai yi amfani da Imel din ba, to lalle babu makawa an rufe.  Mafi karancin lokacin da ake rufe jakar Imel shi ne watanni shida.  Mafi tsawon lokaci kuma watanni tara.  Sai a kiyaye.  Da fatan ka gamsu da wannan takaitaccen bayani.


Assalamu alaikum, barka da dare da fatan kana lafiya.  Muna godiya akan kokarinka game da wayar mana kai akan harkar kwamfuta da waya.  Gaskiya biyanka sai Allah.  Tambayata a nan itace; don Allah Wi-Fi na aiki a Nijeria, kuma yana aiki a kan Android da Java?  Kuma don Allah yaya ake aiki dashi ko saita shi?  Da fatan za ka taimaka.  Allah ya baka ikon taimakawa.  Daga Lawal Ahmad

Wa alaikumus salam Malam Lawal, barka da warhaka. Ina godiya da addu’a, Allah saka da alheri, amin.  Dangane da tambayarka, lallai tsarin Wi-Fi na aiki kuwa a Najeriya, sannan kuma yana nan a kan wayoyi masu dauke da babbar manhajar Android, da Windows Phone, iOS na kamfanin Apple.  Ba ma wadannan kadai ba, hatta wayoyin salula na zamanin baya masu dauke da babbar manhajar Java da Symbian, akwai masu dauke da tsarin Wi-Fi.  Abin da Kalmar “Wi-Fi” ke nufi shi ne, “Wireless Frequency Radio,” wanda tsari ne dake killace yanayin sadarwa na zamani.

Idan kana son ganin wannan tsari a wayarka mai dauke da babbar manhajar Android, ka je: “Settings”, a bangaren “Network Connections” za ka ga wannan tsari, sai ka kunna shi.  Idan akwai na’urar Wi-Fi a inda kake, nan take wayarka za ta sanar da kai cewa: “Akwai tsarin sadarwar Intanet a nan, ta hanyar Wi-Fi.  Shin, kana a son a jona ka da shi?”  Idan kace eh, sai a jona ka.  To amma sai ba dukkan tsarin Wi-Fi yake kyauta ba.  Galibin wuraren da za ka je ka ci karo da wannan tsari za ka samu na wasu kamfanoni ne ko hukumar gwamnati, wanda dole sai an saita maka ta hanyar shigar da wasu kalmomi na sirri da suka kebanci kamfani ko hukumar da ke dashi.  Da faran ka gamsu.


Assalamu alaikum, tambayata a nan ita ce; na kasance idan nasa na’urar ‘Wireless Bluetooth headphone” har ya jima a kunne na, sai kaina ya fara ciwo?  Me ye dalili?  –  Abubakar Musa Abdullahi

Wa alaikumus salam, Malam Abubakar barka ka dai. Shawarar da zan baka ita ce: kayi kokari kaje ka ga likita.  Domin alama ce dake nuna cewa akwai wata lalura ta musaman a kunnenka.  Duk da cewa su kansu kamfanonin da ke kera kayayyakin sadarwa na zamani sukan nusar da mai amfani dasu cewa yawan sauraran sauti mai karfi wanda ya kai makura yana illa ga kunne da tsarin ji na dan adam. Kana iya ganin likita don ya duba ka, don tabbatar da hakikanin abin da ke damunka.  Allah dada kiyayewa, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.