Sakonnin Masu Karatu (2013) (11)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

52

Salaamun Alaikum Baban Sadik, ina da waya kirar Nokia 300, kullum sai ta rika nuna jone take da Intanet, kuma hakan kan cinye mini kudi ko da kuwa banyi komai ba, kuma na rasa yadda zan yi.  To ina mafita?  Na biyu kuma, wai shin, meye bambancin waya kirar Japan da kirar Sin (China)?  Domin nag a dalibai da yaran masu kudi ba su sayan waya kirar Sin (China) sai kirar Japan; duk da kirar Japan tana dauke ne da SIM daya, ita kuma kirar Sin (China) na zuwa ne da SIM biyu ko uku a ciki.  –  Abdulwahhab Haladu, Zarma Hinna: 07060417970

Wa alaikumus salam, Malam Abdulwahhab wannan ba wata doguwar matsala bace.  Ka je “Settings”, ka shiga “Phone Settings”, sai ka gangara “Connection”, ka shiga “Packet Data” ka matsa, za ka ga inda ake saita wayar, sai ka canza daga “When Available” ko “Always” zuwa “When Needed.”  Duk da cewa Nokia 300 na dauke da babbar manhajar Asha ne, amma ba za a samu wani bambanci mai nisa a tsakanin abin da na kwatanta maka ba, don wayar Nokia ce, kuma wannan shi ne galibin tsarinsu wajen saita tsarin jona wayar salula da Intanet.

Dangane da tambayarka ta biyu kuma, ya danganci wadanda ka gani da wayar, da irin zabinsu. Amma kamar yadda akwai wayoyi masu inganci daga kasar Japan, haka akwai wayoyi masu inganci daga kasar Sin.  Me yasa wasu ke son na Japan amma ba son na kasar Sin?  Wannan kuma ya danganci zabi.  A baya galibin wayoyin da ke zuwa daga kasar Sin kanana ne, masu matsalar batir, kuma ba a cika samun kayayyakin gyararu ba idan suka lalace. Amma yanzu wannan yanayi ya canza musamman da bayyanar kamfanin TECNO, wanda ke kera wayoyi masu inganci kuma masu dauke da babbar manhajar Android, kamar yadda bayani ya gabata a sama.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, hakika ni bako ne wajen aiko da sako a wannan fili, amma kuma na dade ina amfanuwa da bayananka a wannan fili.  Don Allah wasu wayoyi ne masu ingantaccen batiri?  Wadanda za a iya amfani da fasahar Intanet na lokaci mai tsawo a kullum amma batirin bai kare ba; tayi kamar kwanaki biyu ko uku ana bugawa.  Allah Ya saka maka da alheri, amin.  –  Idris Muhammad, Funtua, Katsina: 08094286416

- Adv -

Wa alaikumus salam, Malam Idris samun wayar salula irin wannan siffar a wannan zamani zai yi wahala.  Na farko dai yana da kyau ka san cewa shi tsarin Intanet a wayar salula yana amfani ne da masarrafai da dama a lokaci daya, wadanda ke tilasta wa wayar aiwatar da ayyuka masu yawa cikin lokacin da ake mu’amala da shafukan Intanet din. Misali, idan ka budo shafin Intanet a wayarka, akwai masarrafar lilo (Phone Browser), wadda ita ce za ta yi ta hakilon nemo maka bayanan, da kokarin bayyanasu a shafin wayar, da budo maka duk shafin da ka bukata a kowane lokaci.  Wannan ba karamin aiki bane.  Shi yasa a duk sadda kake mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula, za ka ji wayar tana daukan zafi daga baya ko gefenta, daidai inda batiri ko kundun wayar (Processor) yake.

Bayan haka, wannan masarrafa da ke budo maka shafin Intanet, tana amfani ne da yanayin sadarwa (Network), wanda shi kanshi karin aiki ne ga wayar.  Domin a duk sadda waya ke amfani da yanayin sadarwa (wajen kira ko amsa kira, ko neman balas, ko aika sakonnin tes da karbarsu, ko mu’amala da fasahar Intanet), to, yanayin kuzarinta na karuwa, wanda hakan wani karin lodi ne a kan batir, domin shi ne makamashin da wayar ke amfani da shi.

Don haka, abin da ya fi komai cin batir a wayar salula shi ne mu’amala da fasahar Intanet na tsawon lokaci, domin wayar na amfani da masarrafa ne, tare da yanayin sadarwa a lokaci guda.  Sai kuma kira, da amsa kira, da aika sakonnin tes, da kallon hoton bidiyo.  Kari a kan haka, ya danganci tsarin gini ko kirar wayar. Idan mai shafaffen fuska ce (Touchscreen), mara maballin shigar da bayanai (Keypad), nan ma wani karin aiki ne. A takaice dai, iya gwargwadon yawan kyale-kyale da cikar waya wajen gini da kintsi da kira, iya gwargwadon yadda za ta ci makamashin batir.

Don haka, sai ka duba; me kake tunanin za ka fi yi da wayar salula idan ka saya?  Wannan shi zai baka damar samun wacce take da inganci wajen aiwatar da irin wannan aikin.  Daga nan sai ka san yadda za ka tsara wa kanka hanyar tafiyar da ita, musamman wajen manejin batirinta.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.