Mu Leka Duniyar ‘Yan Dandatsa (Hackers) (2)

Kashi na biyu cikin nazarin da muke yi kan dabi’un ‘yan dandatsa. A sha karatu lafiya.

362

Shahararrun Fina-finai kansu

Akwai fina-finai da dama da aka yi kan sana’ar dandatsanci (Hacking), kuma sun yi tasiri wajen kara yawan masu sha’awan wannan sana’a, hatta cikin wadanda ba su da manufa irin tasu.  Fim na farko da aka fara yi shi ne Tron, wanda aka shirya shi cikin shekarar 1982.  Jarumin fim din, Jeff Bridges, masani ne kan kwamfuta da manhajojinta a wani kamfani, wanda ya rubuta manhajar wasan kwamfuta (Video Game), uban gidansa ya karbe ya kuma kore shi, shi kuma ya kai farmaki cikin zangon kwamfutocin ma’aikatan, don daukan fansa.  Sai War Games, wanda shi kuma a shekarar 1983 aka shirya shi. Jarumin fim din shi ne David Lightman, wanda dan dandatsa ne da ke amfani da kwamfutarsa wajen kai farmaki cikin kwamfutocin hukumar tsaro na Amurka.

Ana shiga shekarar 1985 kuma sai ga Real Genuis, wanda ke nuna wasu yara ‘yan jami’a, masana harkar kwamfuta da manhajojinta, inda suka haura da wani farfesan makarantar, kan wata fasaha da suka kirkira don amfanin makarantar, amma ya dauke ya sayar wa hukumar sojin Amurka, su kuma suka fara amfani dashi wajen habbaka makamashin nokiliya (Nuclear Power Plant)Suna ganin haka sai suka yi maza wajen kai hari ga kwamfutar da ke dauke da asalin dabarun fasahar, suka bata tsarin aiki da fasahar, don ramuwar gayya.  Sai fim din Sneakers, shiri na farko da ke dauke da tsarin yadda ake yaudaran mai amfani da kwamfuta wajen satar kalmomin iznin shigansa (Passwords).  Wannan tsari ko fanni shi ake kira Reverse Engineering, a ilimin harkar tsaron kwamfuta, kuma da shi ne galibin ‘yan dandatsa ke amfani wajen satan bayanan sirrin mutane a Intanet.  Wannan fim ya fito ne cikin shekarar 1992.

Cikin shekarar 1995 kuma sai ga shirin Goldeneye, wanda ya fitar da James Bond, shahararren dan fim kan harkar kuru da sai da rai, a matsayin Jarumi.  A ciki, wasu shahararrun ‘yan dandatsan kasar Rasha ne suka sace wani jirgin saman shawagi (Helicopter) mai dauke da komatsen sadarwa na zamani tare da tauraron dan adam, wanda kuma ke da karfin tarwatsa kowace irin kwamfuta ce daga nisan mil sama da dari, cikin dakika guda.  Wannan shi ne fim na farko da ke nuna yadda ake hayan ‘yan Dandatsa wajen ta’addanci, kuma shagube ne ga wani sa-in-sa da aka taba yi tsakanin kasar Amurka da kasar Jamus, lokacin da hukumar gwamnatin Jamus tayi amfani da ‘yan dandatsa wajen sato mata wasu bayanan sirri cikin kwamfutocin tsaron kasar Amurka a shekarar 1986.

A wannan shekara ne dai har wa yau, wani fim mai suna Hackers, ya fito, wanda musamman aka shirya shi don nuna hakikanin dandatsanci. Wani masanin kwamfuta ne ya samar da kwayoyin cutar kwamfuta (Computer Virus) masu tarin yawa, yake neman aika su cikin kwamfutocin wasu kamfanoni don samun kudade masu dimbin yawa, amma yaran sa da yake koyarwa suka ki, aka ta hayaniya.  A bangare daya kuma ga jami’an tsaro na neman su, don labarin ya fito fili, su kuma suna can suna ta hayaniya da  mai gidan su. A karshe dai sun yi nasara wajen hana shi watso wadannan kwayoyin cuta, tare da kare kansu daga jami’an tsaro.  Wannan shi ne shiri na farko da ya nuna ‘yar dandatsa mace, wanda shahararriyar ‘yar fim mai suna Angelina Jolie ta fito a madadi.

- Adv -

Kafin shekarar ta kare kuma, sai ga fim din The Net, wanda shahararriyar ‘yar wasa Sandra Bullock ta fito a matsayin jaruma.  Tana da kawa wacce suka hadu ta Intanet, rannan ta aiko mata da wani sako ta hanyar Imel.  Kafin ta karanta sakon, sai ta samu labarin an hallaka wannan kawa nata.  Sai tai maza ta bude wannan sako.  Tana budewa sai ta ci karo da wasu kuramen bakake da aka rikidar dasu ta amfani da tsarin EncryptionDaga nan tayi ta hakilon neman wanda zai gano mata bakin zare kan wannan sako mai cike da hatsari.  Wannan fim din bai samu darakta kwararre kan harkar kwamfuta da manhajojin ta ba, don galibin jaruman da ke ciki sun yi ta cakuda ma’anar Internet Protocol (IP) ; a wasu lokuta su ce ‘IP’, wasu lokuta kuma su ce ‘PI’.  Har wa yau, akwai rashin tunani da sanayya kan tsarin ma’adanan kwamfuta, inda wani yayi kokarin shigar da bayanai da mizanin su ya kai biliyan daya (1 gigabyte), cikin ma’adar Floppy Disk, wacce duk mizanin ta bai shige miliyan daya da rabi ba.  Duk da haka fim din ya kayatar ta wasu bangarorin, musamman wajen nuna cewa dan dandatsa na iya sato bayanai daga kowace irin kwamfuta ce, a kusa take ko nesa dashi.

Ana shiga shekarar 1999 kuma sai ga shahararren fim din nan mai suna The MatrixShi ne fim na farko da ke nuna gamammen tasirin kwamfuta a rayuwar al’umma a duniya gaba daya.  Jarumi Keanu Reeves, masanin kwamfuta ne mai lura da kwamfutocin wani babban kamfani , amma idan dare yayi, sai ya hadu da wani abokin sa mai suna Neo, wanda shahararren dan dandatsa ne, su yi ta dandatsanci cikin kwamfutocin jama’a.  Wannan fim na nuna cewa galibin masana manhajar kwamfuta (Computer Programmers) kan taba dandatsanci lokaci-lokaci.  Wannan fim har yau ya dada nuna irin yadda duniya ta kusa gamewa wajen dogaro da fasahar kwamfuta da sauran nau’ukan hanyoyi ko kayayyakin sadarwa.

Fim na karshe kan ‘yan Dandatsa kuma shi ne AntiTrust, wanda ya fito cikin shekarar 2001.  Jarumi Ryan Phillippe na gama karatunsa kan kwamfuta da manhajojinta, sai ya samu aiki a kamfanin Tim Robbins, shugaban wani kamfani mai kera fasahar sadarwa da leken asiri ta hanyar tauraron dan adam.  Yana kan kera wani babban na’ura kan wannan fasaha, wanda kuma Ryan ne ke lura da dukkan shirin da ma kwamfutocin kamfanin gaba daya, sai ya lura cewa Tim na amfani da wannan fasaha ne wajen aikin leken asiri kan abokan hamayyansa masu irin wannan sana’a, wanda kuma wannan ya saba ma doka.  Ana cikin haka ne, sai shugaban wannan kamfani ya kashe wani cikin abokan Ryan, wanda a ganinsa yana kawo masa cikas ne.  Ana cikin haka sai Ryan yayi amfani da kwarewarsa na gina manhajar kwamfuta (Programming), don bata wannan tsari ma gaba daya.

A karshe ya kuma fallasa wannan mugun ta’ada da Tim ke yi a kamfaninsa, inda ya aika ma kafafen watsa labaru bayanai, su kuma suka yada ta kowa yaji.  Wannan fim, kamar fim din Goldeneye da ya gabace shi, shagube ne ga kamfanin Microsoft, inda galibin kamfanoni da ma hukumomi ke kuka da shi wajen gaje kasuwannin hanyoyi da kayayyakin fasahar sadarwa a kasar Amurka da ma Turai.  Taken fim din ma kadai ya isa sheda kan haka.

Kammalawa

A halin yanzu na tabbata mai karatu ya gamsu iya gwargwado da takaitattun bayanan da muka ta korowa kan wannan sana’a na dandatsanci da masu yinsa.  Idan Allah Ya kai mu mako na gaba, za mu karkare bayani kan hanyoyin da mai karatu zai iya bi wajen tsare kwamfutarsa daga wannan mutane da ma ayyukan su gaba daya.  Idan da akwai tambayoyi sai a rubuto ta Imel ko text ko kuma a bugo kamar yadda aka saba.  Lambar wayar mu ita ce 08034592444; adireshin Imel kuma kamar yadda aka sani, shi ne fasaha2007@yahoo.comIdan an samu shiga giza-gizan sadarwa ta Intanet, sai a ziyarci mudawwanar wannan shafi, a http://fasahar-intanet.blogspot.comA ci gaba da kasancewa tare da mu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.