Sakonnin Masu Karatu (2012) (6)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

103

Assalaamu alaikum, Malam Abban Sadik, wai su ‘yan Dandatsa (Hackers) suna da wani shafin yanar sadarwa ne da za ka iya shiga don ganin manufofinsu?  – Khaleel Nasir Kuriwa, Kiru, Kano.

Wa alaikumus salam Malam Khalil, lallai ‘yan dandatsa suna da shafinsu na musamman sosai kuwa, inda za kaje ka ga manufofinsu. Babban shafinsu na wannan rariyar, sai ka shiga: http://hope94.hope.net Sai dai wani abu da ya kamata ka sani shi ne, galibin jawabinsu ba lale bane ka iya fahimtar abin da suke yi.  Suna magana ne cikin zaurance.  Idan kana bukatar sanin dabi’unsu da duk abin da ya shafe su, to, ka shiga Google sai ka rubuta: “Hackers”, ko “Crackers”, za ka samu bayanai masu dimbin yawa kan haka.  Da fatan an gamsu.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina yi maka barka da kokari.  Bayan haka, ina biye da kai kan irin abubuwan da kake tattaunawa a filinka na Kimiyya da Kere-kere duk mako a jaridar Aminiya, kuma muna karuwa kwarai da gaske.  Ina fatan Allah ya kara budi amin. Bayan haka, kwana biyu ka daina amsa tambayoyin masu karatu ta tes ko ta Imel.  Ka huta lafiya, na gode.  – Yusuf Muhammad Gagarawa, Jigawa.

Wa alaikumus salaam, Malam Yusuf Muhammad ka min hakuri, watau abubuwa ne suke mini yawa a galibin lokuta, kamar yadda na tabbata ka karanta a kasidar da ta gabata mai taken: “Tuna Baya…”  In Allah yaso zan canza tsari zuwa yadda aka saba iya gwargwado.  Da fatan za a gafarce ni, kamar yadda na bukata lokacin waiwaye adon tafiya.


Salam Baban Sadik, don Allah ina son a yi mini bayanin kalmomin “GSM” da “MTN”.  Na gode.  – Yunusa Zariya.

- Adv -

Wa alaikumus salaam, cikakkiyar ma’anar “GSM” ita ce: “Global System of Mobile Communications.”  Kalmar “MTN” kuma na nufin: “Mobile Telephone Network.”  Da fatan an gamsu.  Na gode.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya, Allah kara maka basira da hikima. Shin, me yasa idan aka boye lamba daga wayar salula, kuma aka turo sakon tes da ita, sai lambar ta bayyana a sakon?  –  Prince Sadiq Babanni, Yola.

Wa alaikumus salam, Malam Sadik barka da warhaka. A ka’idar aiwatar da kira da wayar salula, idan ka kira wani, za a nuna wa wanda ka kira lambarka a wayarsa, yana gani.  Amma idan kaje sashen Tsare-tsaren wayarka, watau “Settings”, ka canza wannan tsari cewa kada ta rika nuna wa wanda ka kira lambarka, to za ta boye lambar.  Wannan a kira ne kadai ya tsaya.  Amma idan ka aika sakon tes dole za ta nuna.  Domin babu wani tsari na boye lambar wanda ya aiko tes a wayar salula.  Dole za ta nuna.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum, barka da warhaka.  Yanzu don Allah kai Abdullahi Salihu Abubakar kace yin azumi a watan Rajab ba daidai bane?  A matsayinka na Musulmi? –  08031323908

Wa alaikumus salaam, na san kana ishara ne zuwa ga bayanin da nayi a cikin kasida ta mai taken: “Bunkasar Fasahar Sadarwar Zamani a Najeriya – Kalubale da Hanyoyin Ci Gaba,” inda nake bayani cewa jama’a su yi hankali da sakonnin da ake turo musu ta tes musamman lokacin azumi kan falalar ayyuka, da cewa akwai hadisan karya da ake aikowa.  Idan ka fahimce ni, ban ce yin azumi a watan Rajab ba, nace kan “…falalar yin azumin Rajab.”  Akwai bambanci tsakanin “yin azumi a watan Rajab, da falalar azumin Rajab.”  Akwai hadisan karya sama da talatin da aka kaga aka ce Manzon Allah ne ya fada, masu nuna falalar watan Rajab. 

A wasu kasashe bayan azumi, ana yanka dabba da ake kira “Ateerah”, ana kwana sallah a tsakiyar watan, watau “Salaatur Ragaa’ib,” ana rarraba gurasa da masa bayan an karanta musu Suratul Mulk, duk wannan bai inganta ba daga Manzon Allah.  Mu a nan abin da muka fi yi shi ne azumi, wanda muke kira azumin tsofaffi, da kuma sallar tsakiyar wata.  Amma yin azumin nafila cikin Rajab, kamar yadda aka saba yi a sauran watanni, ya halatta kuma ma abin so ne. musamman azumin litinin da alhamis, da yin azumi uku cikin kowane wata, duk sun inganta daga Manzon Allah. Amma idan da wancan manufa ce, cewa watan Rajab na da wata falala ta musamman, ba abin da ya inganta.  Don karin bayani ka duba littafin “Al-Fawaa’idul Majmoo’ah fil Ahaadeesil Mawdoo’ah” wanda Shawkaani ya rubuta, lambar hadisi na 287, da 288, da 289, da 290 da kuma 291.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.