Tsarin Gudanuwar Kwakwalwar Dan Adam (1)

A wannan mako bincikenmu ya tabo yadda kwakwalwar dan adam ke gudanuwa ne, da irin kudurarta wajen aiwatar da ayyuka sama da daya a lokaci daya.

153

Mabudin Kunnuwa

“Kun raba mini hankali” wai an ce wa rago ya sha fura ya kama hanyar gona.  Domin shi abin da yafi so, a matsayinsa na rago wanda ba ya son ko kadan ya motsa gabobin jikinsa, shi ne, ya sha furan, sannan ya kwanta ko ya zauna ya kama hira da jama’a. To ta yaya aka yi hankalinsa ya rabu kashi biyu, alhalin ayyukan da ake nemansa da yi ba a lokaci daya aka ce ya yi su ba?  An ce ya sha fura.  Aikin farko kenan.  Sannan aka ce masa ya kama hanyar gona, wato bayan ya sha furan kenan.  Wannan shi ne aiki na biyu. Kuma kowanne a lokaci daban-daban zai aiwatar da shi.  Watakila mai karatu bai taba damuwa da sanin dalilin da yasa rago yace an raba masa hankali ba.

Masu karatu, a yau shafin Kimiyya da Kere-kere zai kutsa wani fanni mai matukar muhimmanci a rayuwar dan adam da sauran kayayyakin sadarwa na zamani. Wannan fanni kuwa shi ne bangaren da ke lura da tsarin gudanarwar kwakwalwar dan adam wajen aiwatar da ayyuka fiye da daya, a kuma lokaci daya, cikin yanayi daya.  A turancin malaman kimiyyar bangaren kwakwalwa da tunanin dan adam, wannan fanni shi ake kira “Human Brain Multitasking.”  Ba za mu tsaya da bayani kan yadda dan adam ke fuskantar kalubale wajen aiwatar da ayyuka fiye da daya a lokaci daya kadai ba, za mu gwama kwarewarsa (in har ya kware kenan) da yadda masarrafar sarrafa bayanai ta kwamfuta (Computer Processor) ke aiwatar da nata ayyukan cikin lokaci daya. A karshe za mu fahimci dalilin da ya kai rago ga cewa: “Kun raba mini hankali,” sa’adda aka ce masa ya sha fura, sannan ya kama hanyar gona.

Kwakwalwar Dan Adam

Kwakwalwar dan adam (wato Brain) wata masana’anta ce, ma’adana ce, sannan kuma masarrafa ce ta musamman.  Yadda aka yi ta kasance masana’anta kuwa shi ne, aikin ta ne sarrafa bayanan abubuwan da dan adam ke alaka da su – mutane ne, kayayyaki ne, bayanan ilmi ne, dabbobi ne, ko ma dai mene ne – wajen tantance launinsu, da yanayinsu, da tsarinsu, da kimarsu, da adadinsu, tare da kawo su a duk lokacin da dan adam ya neme su ta hanyar tunani.  Har wa yau aikin kwakwalwa ne tantancewa tsakanin abubuwa guda biyuko fiye da haka da ke gabanta.  Aikin ta ne auna kima da yanke hukuncin wanda ya fi wajen girma ko karko ko duk wani abin da aka bata a matsayin mizani da zabi.  Duk bangaren masana’anta ce ke wannan aikin.

- Adv -

Mun kuma ce kwakwalwa ma’adana ce, sosai kuwa.  Duk abin da ka taba gani, da wanda ka taba da hannunka, da abin da ka ji da kunnuwanka na labari ko sauti, da abin da hancinka ke susnsuno maka, duk aikin kwakwalwa ne ta taskance maka yadda abin yake.  Ita ce za ta adana maka warin da ka ji ko doyi a yayin da ka wuce wata bola. Da zarar kuma ka zo ba da labari, nan take za ta tuno maka irin warin da kaji, har ka iya gaya wa mutane.  Idan sauti ne mai firgitarwa, za ta iya tuno maka da yadda yake, sannan ka sifata wa jama’a cewa sauti iri kaza na ji, mai firgitarwa.  Idan labari ne aka baka na wani abu mai girma, zuciya za ta sifata maka girman, sannan kwakwalwarka kuma ta adana maka wannan sifa da ka baiwa abin da aka sifata maka ko da kuwa baka taba ganinsa ba.  Ida kuma kai ganau ne a inda wani abu ya taba faruwa, duk aikin kwakwalwa ce taskance maka labarin baki dayansa, sannan ka samu saukin watsawa idan bukatar hakan ta taso.

Sannan kwakwalwar dan adam masarrafa ce ko wajen gudanarwa, saboda muhimmancinta wajen taya dan adam gunadar da ayyukan da yake fuskanta a rayuwarsa ta yau da gobe.  Idan aiki guda kake yi, hankalinka zai koma kansa ne kacokam.  Idan kuma ayyuka biyu ne a gabanka, duk wanda ka fi bashi muhimmanci shi ne za ka fi yinshi da kyau.  Me yasa?  Dalilin na tafe.  A takaice dai, duk abin da ka tashi gudanarwa, to kwakwalwa ce za ta taimaka maka da lokaci, mai dauke da hankalin lura, don aiwatar da wannan aiki. A takaice dai, wadannan ayyuka da bayaninsu ya gabata, suna samuwa ne ta bangarorin kwakwalwa daban-daban. Akwai bangaren da aikinsa ne kawai adana bayanai.  Akwai bangaren da aikinsa ne tuna abubuwan da suka gabata. Akwai bangaren da aikinsa ne gudanar da ayyuka ta hanyar samar da lokacin lura da mai aikin ke yi, da dai sauransu.

Bincike Cikin Wannan Fanni

Wannan fannin ilmi na tsarin gudanarwa ta kwakwalwar dan adam, wato Human Brain Multitasking, ya fara shahara ne tun shekarar 1990.  A takaice dai sabon fanni ne da aka bambaro shi daga fannin ilmin kanikancin kwamfuta, wato Computer Engineering.  Wadanda suka fara gudanar da bincike mai zurfi a kanshi sun hada da Mayer da Moreno, wadanda kwararru ne a fannin Gwajin Tsarin Tunanin Dan Adam, wato Experimental Psychology.  Sun gudanar da bincikensu ne kan tasirin wannan tsari na cakuda ayyuka fiye da daya a kwakwalwa a lokaci daya, ga karatun dalibai a makarantu.  Sakamakonsu ya nuna cewa lallai yin hakan na cikin ababen da ke kashe kuzari da karshashin dalibai, tare da rage musu kokari da kwazonsu cikin karatu.  Sai kuma Juanco da Cotton, wadanda suka dubi tasirin hakan wajen rayuwar dan adam baki daya.

Bayan su, an samu Richard Hallowell, wanda shahararre ne a fannin Ilmin Dabi’a. Shi ne ya dada gano cewa, yawan damun kwakwalwa da ayyuka fiye da daya a lokaci daya kan haifar da kurakurai cikin hukuncin da kwakwalwa za ta rika bayarwa, ko cikin ayyukan da kwakwalwar ke gudanarwa.  A nata bangaren kuma, Monica Luciana da ke Jami’ar Minnesota a kasar Amurka ta gano cewa, duk da cewa kwakwalwar dan adam ba za ta iya daukan ayyuka fiye da biyu ba a lokaci daya, amma idan aka dabi’antar da kwakwalwar ta hanyar maimaci da karantarwa kafin shekaru 16 zuwa 17 na farkon rayuwa, yara na iya sabawa da irin wannan tsari.  Amma hakan sai ya dauki lokaci mai tsawo kafin kwakwalwa ta saba.  Wannan sakamako har wa yau shi ne sakamakon da Paul E. Dux da ke Jami’ar Verderbilt ya fitar shi ma; cewa lallai hakan na iya yiwuwa, amma sai da dan karen tarbiyya na tsawon lokaci.  Sai kuma Koechlin da ya gabatar da nasa binciken cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, inda shi ma ya gano cewa kwakwalwa ba za ta iya daukan ayyuka sama da guda biyu ba a lokaci daya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.