Sakonnin Masu Karatu (2010) (8)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

55

Assalaamu Alaikum, don Allah Baban Sadik wai shin mai yiwuwa ne mutum ya iya gina Mudawwanarsa (blog) ta wayar salula ko kuwa dole sai a kwamfuta?  –  Jamilu Ahmad, Kaduna: 08032424168

Malam Jamilu ya danganci irin wayar da kake da ita.  Idan babbar waya ce, mai shafi mai fadi, da kuma saurin sadarwa da Intanet, kana iyawa.  Amma idan ba haka ba, zai dace ka yi amfani da kwamfuta.  Domin zai dauke ka tsawon lokaci, sannan galibin gidajen yanar sadarwa na Mudawwanai suna da shafuka zubi biyu ne; da wanda ake iya shiga da kwamfuta, da kuma shafin da ake  shiga ta amfani da wayar salula.  Idan ka shiga shafin da ake shiga ta kwamfuta a wayarka, ba za kaji dadin mu’amala da shafin ba, domin zai kasance mai fadi ne, kuma yana dauke da hotunan da za su ci maka kudi sosai kafin ka gama gabatar da dukkan abin da kake son gabatarwa.  A takaice dai ka yi amfani da kwamfuta wajen ginawa, in yaso sai ka rika shiga ta wayarka kana aikawa da sakonni.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum, Baban Sadik na kasance mai bibiyar makarantarka sama da shekara uku, kuma ina maka fatan alheri, Allah shi kara basira, amin.  Don Allah ina da waya ne kirar Nokia 6260, ko tana da manhajar Opera?  In har akwai, to yaya zan yi in rika shiga Intanet? Na gode.  –  Aliyu Danlabaran, Zariya: 08036158781

Malam Aliyu mun gode da addu’a, Allah kara basira da juriyar kasancewa tare da mu.  Hakika galibin wayoyin salula na zamani suna da nau’in manhajar Opera Mini a tare dasu, ko kuma idan kaje gidan yanar sadarwan Opera, za ka samu nau’in da ya dace da wayarka, tabbas. To amma kafin nan, ina son sanar da kai cewa dukkan wayoyin salula suna da masarrafar lilo da tsallake-tsallake, wato “Browser”, wacce kuma kana iya mu’amala da ita wajen shiga Intanet.  Amma idan kana son “Opera Mini” ce, to duk babu damuwa, kana iya saukar da ita zuwa wayarka, sannan ka loda mata.  Don haka sai kaje inda ake mu’amala da Intanet a wayarka (wato “Browser”), ka shigar da wannan adireshin http://mini.opera.com/download  shafin da ke dauke da manhajar zai budo, sai ka bi umarnin da ke shafin, ka saukar, tare da loda ta a wayarka.  Allah sa a dace.


Assalaamu Alaikum,  ina fatan kana cikin koshin lafiya tare da iyalanka.  Na dade ina karatun shafinka a cikin Jaridar AMINIYA, kuma yana kara min fahimtar ayyuka na.  Domin ina da shedar karatu ta NCE a fannin karantar da kimiyyar kere-kere, wato Technical Education, da  kuma Difiloma a fannin kwamfuta. Ina jin dadin karatun shafinka.  Allah ya kara mana fahimta, amin.  –  M. A. Faruk, Sokoto: 08036029098

- Adv -

To mun gode mu ma, kuma Allah kara dankon zumunci, da fahimta, da kuma juriya wajen kasancewa tare da mu.  Tsarkakakkiya kuma cikakkiyar godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda duk wata ni’ima ta fahimta ko wayewa ko ci gaba, daga gareshi take.  Mun gode.


Salamu Alaikum, ina amfani da wayar Nokia 6760 kuma ina da manhajar Opera mini a ciki. Ina son bude Imel ne don karban sako da aikawa, don Allah yaya zan yi? Na gode.   –  08036017399

Kamar yadda muka sha bayani kwanakin da suka wuce, bude akwatin Imel ta wayar salula, in dai ba nau’ukan “Smartphones” bane, ba abu bane mai yiwuwa.  Na farko dai asalin shafin da za a budo maka don ka yi rajista, ba ya samuwa sai ka aika da sakon “START”, zuwa wata lambar, wacce kuma bamu da kamfanin a nan nahiyar Afirka, ko ince Nijeriya.  Wannan sakon da za ka aika ne zai sa a aiko maka da rariyar likau din da zaka bi, don samun shafin.  Abu na biyu kuma shi ne, yin rajistan a waya na iya ci maka kudi da yawa.  Duk da haka, idan kana amfani da wayar salula nau’in “SmartPhones” ne, (irin su “Blackberry” ko nau’ukan “E-Series” na kamfanin Nokia) to kana iya yin rajista ba matsala. Domin wadannan nau’ukan wayoyin salula suna mu’amala ne da Intanet tamkar kwamfuta cikakkiya.  Da fatan an gamsu.


Da fatan Malam yana nan lafiya.  Ni matsalata ita ce: a da ina karba ko aika sakon Imel ta hanyar Yahoo a wayata, amma tun shigowar wannan shekarar ko na shiga sai dai in ga tsoffin sakonnin da na aika ko karba.  Shin a ina matsalar take ne:  daga waya ta ne, ko daga Yahoo?  –  Sani Abubakar ‘Yankatsare, Jos: 08026023796

Malam Sani barka da war haka kuma ya aka ji da dawainiya da mu?  Da fatan ana lafiya.  Wato akwai abubuwa guda biyu ko uku.  Da farko dai ya danganci tsarinka.  Watakila tun da aka shiga wannan shekarar baka aika da sako ko kuma karbi wani sako daga wani ba.  In kuwa haka ta kasance, to ai babu yadda za a yi ka samu wani sabon sako a jakar Imel dinka.  Na biyu kuma, a iya cewa matsalar daga wayarka ce, amma hakan da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. 

Domin in daga wayarka ne, ai baza ka iya ma shiga Imel din ba tun farko.  In har kana ganin sakonnin da ka aika a baya, da wadanda aka aiko maka a baya, kuma babu wanda ya sanar da kai cewa ya aiko maka sako amma ka kasa gani, to ba zai zama matsalar daga gareta ba.  Abu na uku shi ne a ce laifin kamfanin Yahoo.  Hakan kuwa bazai yiwu ba, domin muddin kana iya shiga jakar Imel dinka daga wayarka, to ba yadda za a yi laifin yazo daga kamfanin Yahoo.  Da fatan Malam ya gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.