Fasahar “Digital Currency”: Manyan Matsalolin Cryptocurrency (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 4 ga watan Yuni, 2021.

451

Manyan Matsalolin “Cryptocurrency” (2)

Aringizon Farashin Kwandaloli

Duk da cewa nau’ukan kudaden Intanet babu wata hukuma ko wani kamfani shi kadai dake lura da samuwa da yaduwarsu, wanda hakan na cikin siffofin da suka bambantasu da kudaden takarda da hukumomin kasashe ke samarwa a zahirin rayuwa, sai dai kuma, akwai wani gungun kamfanoni ko mutane dake tasiri wajen sauyawar farashin wasu kwandaloli su kadai.  Ire-ire wadannan mutane suna yin hakan ne ta hanyar saye wani adadi na kwandalolin daga hannun mutane, don samar da “karanci na wucin-gadi” (artificial scarcity) a kasuwa.  Wannan zai sa farashin kwandalar ya haura sama, saboda yawan mabukata.  Irin wannan aringizo yana nan sosai a kasuwar hada-hadar kudade na zamani dake Intanet.  Kuma, sabanin tsarin kudaden takarda na kasashe wanda ke da hukumomin dake lura da yadda ake gudanar dashi, a duniyar Intanet ba wanda ke lura da masu hada-hadar Cryptocurrency.  Don haka, kamfanin da ya samar da wata kwandala kawai na iya janye su daga kasuwa lokaci daya, don neman farashin ya haura a samu riba, ko kuma ya sako kwandaloli da yawa cikin kasuwa don farashin ya fadi, mutane suyi hasarar kudade masu dimbin yawa; kawai saboda wata bukata ta kashin kansa.  Haka ma shahararrun masu kudin duniya, irin su Elon Musk da sauransu, suna iya sayan kwandaloli da yawa su rike, sai farashin ya haura sosai, kwatsam sai su sayar da abin da ke hannunsu.  Saboda yawan kwandalolin, shigowansu cikin kasuwa na iya karya farashin kwandalar nan take, miliyoyin mutane su talauce.  Irin haka na faruwa hatta a kasuwannin hada-hadar kudade na Zahiri.  Bambancin kawai shi ne, a na Zahiri, hukuma na iya gano dalili, idan ya saba wa ka’ida, a hukunta mai laifi.  Wannan shi ake kira: “Insider Dealing” ko “Market Manipulation”, a fannin hada-hadar kudi na hannun jari (Capital Market).  Amma a duniyar Cryptocurrency babu wannan doka ko tsarin kama mai laifi.

Babu Uzurin Kuskure da Tsarin Mayar da Kudi

Karkashin tsarin hada-hadar kudade na zamani dake Intanet, idan kayi kuskuren aika wasu kwandaloli ga wani daban ba wanda kake nufi ba, to, kwandalolin sun tafi kenan.  Haka idan wani ya aiko maka cikin kuskure, ba za ka iya mayar masa ba, don ba lalai bane ma ka sanshi, ko shi ya sanka.  Wannan yana cikin matsaloli mafi girma da wannan tsari ke dauke dashi.  Sabanin tsarin hada-hadar kudade na zahirin rayuwa; kana iya kai kokenka ga banki, sai su gyara kuskuren da kayi, muddin bai kwashe kudaden ba.  Kuma ko ya kwashe ma, da zarar wasu kudade sun shigo taskarsa, ana iya kulle taskar bai sani ba, sai kudin sun shiga ya kasa cirewa.  Amma a tsarin “Cryptocurrency” babu wannan tsarin.  Kana zaune kawai kana iya ganin kwandaloli ko daloli sun shigo taskarka ba tare da ka sayar da wata haja ba ko ka saya.  Kuma babu yadda za ayi ka mayar da kudaden ga wanda ya aiko su.  Haka tsarin magudanar yake, ba yadda ka iya.

- Adv -

Karancin Kudaden Kasashe Don Juya Kimar Kwandala

A tsarin hada-hadar kudade na zahirin rayuwa, idan kana da takardar kudin kasarku, kana iya sayen da yawa cikin kudaden wasu kasashe a duniya, in ma ba duka ba.  Amma a tsarin “Cryptocurrency”, ba kowace kwandala ake iya saya da dalar Amurka ko kudin wata kasa ba.  In ka kebe kwandalar Bitcoin, galibin kwandaloli kana iya sayensu ne ko sayar dasu da kudin wata kasa, musamman kasar da kamfanin kwandalar yake.  Idan kana bukatar sayan kwandalar da ake sayarwa da kudin kasar Jamus misali, kai kuma dalar Amurka ce dakai, dole sai ka canza dalar Amurka zuwa kudin jamus sannan ka iya saye.  Haka idan kana da kwandalar dake kudin kasar Sin, idan ka sayar da kudin Sin za a biya ka.  Idan a Najeriya kake, wannan ba karamar matsala bace.  Hakan na nufin dole sai ka mallaki taskar ajiyar kudaden kasashen waje (Domiciliary account) na iya adadin kasashen da kake cinikayya da kudinsu kenan, kafin ka iya juya kudin zuwa kudin kasarku.  Wannan aiki ne ja, inji mutan Dan Ja dake Katsina.  A tare da cewa na san akwai dabaru da dama da wasu keyi wajen juya wadannan kudade, wanda wannan ba mahallinsa bane.

Mummunan Tasiri Kan Mahalli

Mai karatu zai yi mamakin jin an kawo tasirin kudaden zamani na Intanet kan mahalli.  Meye alakar dake tsakaninsu?  Kamar yadda na fada a farko, wadannan kudade na Cryptocurrency dai ana samar dasu ne ta hanyar da ake kira: “Mining”, wanda a harshen Hausa na kira: “Hakowa”.  Kamar yaddda masu neman zinare da azurfa ke hakosu daga karkashin kasa.  Sai dai su wadannan nau’ukan kudade ba daga gundarin kasa ake hako su ba, ana samar dasu ne ta amfani da ka’idojin lissafi na kwamfuta masu tsauri, wanda magudanar Bitcoin, wato “Bitcoin Blockchain” ke ingizo wa kwamfutar mai hakowa, tana ba da amsarsu.  Idan ta ba da amsar tambayar daidai, sai magudanar ta kara ingiza wa kwamfutar wata tambayar kuma, har sai ta amsa tambayoyin lissafi masu tsauri (Complex mathematical equations) iya yadda magudanar ta tanada, sannan sai a saka wa kwamfutar da ladar wannan aiki, ta hanyar ba ta kwandala guda, ko wani bangare na kwandalar.  Wannan shi ne tsarin hako kudin Crypocurrency a takaice.  Kuma aiki ne mai girman gaske wanda ke bukatar makamashin lantarki mai dimbin yawa, da kwamfutoci masu dan karen tsada wadanda ke dauke da manyan masarrafai (processors) masu taimaka mata wajen warware ka’idar lissafin da ake ingizo mata cikin sauki.  Ba irin kwamfutar yau da kullum bace ke iya wannan aiki.  Hakan na bukatar kudi mai dimbin yawa da wutar lantarki mai yawa, da kuma tsawon lokaci.

Tasirin wannan aiki ga mahalli yana da muni sosai a kasashen da ake gudanar da aikin.  Shi yasa ma ba kowa ke iya hada kwamfutocin da ake amfani dasu wajen hako wadannan kudade ba, kafin ma aje kan bayanin makamashin lantarki da za a yi amfani dashi wajen aikin.  A halin yanzu an kiyasta cewa makamashin lantarkin da wannan aiki na hako kudaden Cryptocurrency ke handamewa ya wuce makamashin lantarkin da kasar Holland ke amfani dashi a duk shekara.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.