Sakonnin Masu Karatu (2009) (11)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

84

Salam, tare da fatan alheri, ina fatan dukkan makaranta wannan fili muna lafiya, amin. Baban Sadik, wai ita wannan waya da kamfanin MTN take sanyawa a kasa, mene ne amfaninta ga sadarwa?  Kuma mutane suna cewa tana hade da sadarwa irin ta Intanet wajen sauri; meye gaskiyar al’amarin?  –  Ibrahim Yahaya Mai Ruwa Dan-hutu: 07080948888

Malam Ibrahim Dan-hutu lallai wannan tambaya ce mai muhimmanci ga harkar sadarwa kowane iri ne kuwa.  Ina fatan Allah ya bamu lokaci na musamman don mu gabatar da doguwar kasida kan yadda wannan tsari ke aiki.  Da farko dai abin da kaji ana fada na alakar da ke tsakanin wannan waya da ake binnewa a karkashin kasa da kuma sadarwa ta wayar tarho musamman, gaskiya ne ko shakka babu.  Na biyu kuma, wannan waya da ake shimfidawa, ba waya bace kamar sauran wayoyi.  Waya ce ta “kunun gilasai”, wadda aka tsattsaga gwargwadon kaurin silin gashin kai.  Yadda abin yake shi ne, gilasai ake narkawa, ko damawa, kamar kunu, sannan a sandarar dashi, tare da yayyanka shi filla-filla, ko sille-sille, ko sili-sili, gwargwadon kaurin gashin kai, sannan a hada su wuri guda, a suturce su da gasassun robobi (plastics), sannan a maye samansu da dafaffiyar roba (rubber). 

Wannan nau’in waya ita ake kira “Fiber-Optics”, ko kuma “Optical Fiber Cables”.  Kuma su ne wayoyin da suka fi saurin isar da sakonnin murya ko bayanai ko bidiyo, saboda suna tafiya ne a matsayin haske, cikin gaggawa ba bata lokaci.  Idan kana son fahimtar yadda tsarin saurin isar da sako da wannan waya ke yi, ka dubi yadda haske ke saurin isa idan aka haska tocila daga bakin wani bututu, zuwa karshensa. Nan take zai isa.  Idan ma bututun ba a saiti yake ba, sai ka dubi inda yake da kwana, ka sanya gilashi a wajen.  Da zarar ka kara haskawa, dungun da ke dauke da gilashi zai cilla hasken zuwa gaba, har ya isa inda ake son yaje.  To idan ka dubi wannan waya da aka kera da gilasai, sai ka ga cewa da zarar ballin haske ya sauka kan sillin waya guda daya, to duk zata haskaka sauran, tare da isar da hasken da ke dauke da bayanan cikin gaugawa. 

Wannan kuma ya shafi hasken da ke dauke da murya ne (Tarho da Rediyo), ko bayanai (Intanet), ko kuma hotuna masu motsi da daskararru (TV da Bidiyo), misali.  Don haka kake ganin kamfanin MTN (da ma GLO) suna binne wannan waya, don inganta tsarin sadarwarsu tsakanin tashoshin sadarwarsu da suka game dukkan jihohin kasar nan.  Kai ba nan kasar kadai ba, galibin manyan tekunan duniya na dauke ne da wadannan wayoyi a cikinsu, ko karkashinsu, wadanda kamfanonin sadarwa na kasashe dabam-daban ke binnewa don isar da sadarwa cikin gaugawa da sauki a duniya baki daya.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum, Malam a duba min mudawwana ta da ke: http://munbarin-musulunci.blogspot.com,  a Intanet.  –  Aliyu M. Sadisu: 08064022965

Malam Aliyu sannu da aiki.  Lallai na shiga Mudawwanar “Munbarin Musulunci” da ka bude a Intanet, na kuma gamsu da irin sakonnin da kake isarwa na ciyar da al’umma gaba a Musulunce.  Wannan aiki ne mai gwabin lada, kuma Allah Ya albarkaci wanann yunkuri taka, amin.  Dangane da tsarin Mudawwanar kuma, ina ganin ba wata matsala.  Domin kana shigar da kasidun yadda ya kamata.  Illa dai abin da zan iya cewa shi ne, ka cire alamar ruwa biyu (wato 🙂 da ka sanya a tsakanin “BARKA DA ZUWA”  da kuma “MUNBARIN MUSULUNCI”.  Kawai ka mayar dashi jumla guda, kamar haka: “Barka da Zuwa Munbarin Musulunci”.  Allah sa mu dace baki daya, amin.


Salamu Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: tsarin canje-canjen sautin murya na wayar salula, wato Magic Voices; Malam karin bayani nake nema dangane da yadda tsarinsa yake?  – Aliyu Muktar Sa’id (IT), Kano: 08034332200

- Adv -

Malam Aliyu sannu da aiki, kwana biyu bamu gaisa ba.  Da fatan kana cikin koshin lafiya, amin.  Tsarin “Magic Voices” a fannin sadarwar tarho ko wayar salula, shi ne tsarin da ke bai wa mai waya damar canja sautin muryarsa da aka sanshi da ita, zuwa wata murya dabam.  Misali, kana iya canja muryarka ta koma ta mace, idan namiji ne kai, ko kuma ta zama siririya, idan babbar murya kake da ita.  Hakan na faruwa ne cikin sauki a wayar salula sanadiyyar wata manhaja da aka kera wayar da ita.  Sannan kana iya neman ire-iren wadannan manhajojin canjin murya ka sanya wa wayarka.  Duk wanda ya kira ka, kafin ka amsa, kana iya canja muryarka.  Maimakon ya ji asalin muryarka, sai yaji wata murya dabam. 

Sai dai kuma, idan ba tsananin bukata bace ta kama, bai dace a kullum mutum ya rika yaudarar mutane da wata murya ba: ko don ba ya son Magana dasu, ko don kauce musu.  Yana da kyau a kullum mutum ya zama yana wakiltar kansa. Ire-iren wayoyin salular da ke zuwa da irin wannan tsari galibinsu daga kasar Sin (China) ake zuwa dasu. Da fatar ka gamsu.


“Yabon gwani ya zama dole”.  A cikin duka shafukan AMINIYA, shafi na 16 (wato Shafin “Kimiyya da Fasaha”) shi ne gwani na, saboda ina karuwa dashi ainun, kasancewar ni mutum ne mai son mu’amala da na’urar kwamfuta da sauransu.  Baban Sadik Allah ya kara maka basira a kan aikinka, amin.  –  Bashir (GZG964), Minna, Neja: 08034629830

Malam Bashir mun gode da wannan addu’a taka, kuma Allah ya mana jagora baki daya, kuma inda an ga kura-kurai cikin abin da muke ciyar da kwakwalen mutane, to don Allah a rika tunatar damu.  Allah saka maka da alheri, amin.


Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: meye amfanin “Recycle Bin” a jikin kwamfuta?  –  Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu amfanin jakar “Recycle Bin” da ke shafi ko fuskar kwamfuta, shi ne taskance dukkan bayanan da ka goge ko share daga kwamfutarka.  Kamar kwandon zuba shara ce, ko bola.  Duk sa’adda ka goge wasu bayanai (delete) daga kwamfutar, an tsara kwamfutar ne ta yadda za ta rika zuba su a cikin wannan Kwando ko burgamin adana bayanai.  Hikimar yin hakan shi ne, idan ka canza ra’ayi daga baya kaji kana bukatar abin da ka share ko goge, to kana iya bude wannan jaka, ka matsa jakar bayanin da kake bukata, za a mayar maka da jakar bayanin zuwa inda aka dauko ta da farko.

Har way au, kana iya share karikitan da ke cikin wannan jaka gaba daya.  Sai dai kuma idan ka share shikenan.  Baza ka taba samun abin da ka zuba ciki ba.  A takaice dai, aikin “Recycle Bin” shi ne ajiye maka share da ka sharo daga cikin kwamfuta.  Idan kana bukata, kana iya komawa ka nemo su.  Amma idan ka share su duka daga cikin jakar, shikenan.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.