Sakonnin Masu Karatu (2009) (12)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

64

Assalaamu alaikum, Baban Sadik ina fatan kana lafiya.  Bayan haka, tambaya ta a kan GPRS ne: wani lokaci alamar “G” na bayyana a waya, wani lokaci kuma alamar “E” ne ke bayyana. Ko hakan me yake nufi, dangane da bambancin da wadannan haruffan?  – Muhammad Abbass, Lafiya, Nassarawa: 08036647666

Malam Muhammad Abbass barka da war haka.  Babu wani bambanci dangane da abin da wadannan alamu guda biyu ke nunawa a shafin wayarka a yayin da kake lilo ko mu’amala da fasahar Intanet.  Bayyanar hakan shi ke nuna cewa kana mu’amala da fasahar Intanet ne ta hanyar tsarin “GPRS” da kamfanin wayarka ke da ita.  Don haka, idan ka ga alamar “G” ko “E”, to duk suna nufin tsarin “GPRS” ne, wanda ke amfani da tsarin nau’in sadarwa ta “2G”.  A wayoyin salula na zamani masu amfani da tsari ko nau’in sadarwa ta “3G” ko “3.5G”, alamar “3.5G” suke nunawa.  Don haka idan kaga “E” ko “G”, to duk tsarin “GPRS” ne.  Duk da yake wasu masana sun tafi a kan cewa alamar “E” na ishara ne zuwa ga ingantacciyar tsarin “GPRS” mai suna “EGPRS” (wato “Enhanced General Packet Radio Service”), mai amfani da tsarin sadarwa nau’in “2.5G”.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, wane irin alfanu Internet Groups, irinsu Yahoo Groups ke dauke da shi? Malam mai zai hana ka bude wa wannan filin nashi?  –  Ahmad Muhammad Amoeva, Kano: 08066038946

Malam Ahmad abin da ake nufi da “Yahoo Groups” shi ne “Majalisun Tattaunawa ta Intanet”.  Matattara ce inda mutane ke haduwa don tattauna wasu al’amura na rayuwa da addini.  Wasu sun ta’allaka ne kan abinci, ko abin sha, ko tufafi, ko motocin hawa, ko zamantakewa, ko addini da dai sauransu.  Tattaunawar ana yin ta ne ta hanyar sakonnin Imel.  Da zarar ka shiga cikin majalisar ta hanyar rajista, duk sa’adda wani mamba ya aiko da sako, akwai wata manhaja ko masarrafar kwamfuta mai suna “Listserver” da ke cilla sakon ga dukkan mambobi.  Sai ya zama abin da Malam “A” ya gani, shi ne abin da Malam “B” zai gani a jakar Imel dinsa.  Shahararrun Majalisun Tattaunawa na harshen Hausa su ne: Majalisar Fina_finan Hausa, da Majalisar Marubuta, da Majalisar Nurul-Islam (wacce nake lura da ita), da kuma Majalisar Hausa-da-Hausawa.  

Wannan shawara ce mai kyau, kuma zan duba yiwuwar hakan in gani.  Abin da wannan tsari ke bukata shi ne hadin kai da kuma lazimtar majalisar, don amfanuwa da abin da ake tattaunawa a ciki.  Idan ma har na bude, to zai zama wajen tattaunawa ce da neman agaji kai tsaye ga dukkan masu matsaloli, kamar dai yadda ake yi ta hanyar tes.  Tun farko ban yi hakan bane don tunatin cewa wayar salula a halin yanzu ta rinjayi rayuwar mutane.  An fi karkata wajen aiko da sakonni ta hanyar wayoyin salula da hanyar Intanet.  Wannan tasa na dan ja da baya.  Amma dai, kamar yadda nace a sama, zan duba yiwuwar hakan nan gaba.  Mun gode.


- Adv -

Salamu Alaikum Baban Sadik, tambaya ta ita ce: meye asalin launuka (colours) ne? – Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu wannan tambaya ce mai muhimmanci, kuma kasancewar bayanai kan haka sun ta’allaka ne ga tsantsar Kimiyyar lissafi da halitta a lokaci guda, nake ba da hakuri cewa sai hali ya samu za mu yi zama na musamman, don gabatar da bincike na musamman kan haka.  Amsa kan haka na bukatar gamsasshen bayani, wanda fili irin na amsa tambayoyi bazai iya bamu dama ba.  Don haka nake neman afuwa sai zuwa wani lokaci. Na gode.


“Hackers” da “Botnets”: akwai wani bambanci ne a tsakaninsu, ko duk abu daya ne? Ka huta lafiya.   –  Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07069191677

Ko kadan ba daya suke ba. A ilmin sadarwa ta kwamfuta, idan aka ce “Hackers”, ana nufin ‘yan Dandatsa kenan, masu amfani da kwarewarsu ta ilmin kwamfuta da dukkan hanyoyin sadarwa, wajen cutar da kwamfutocin mutane ko hukumomi ko kungiyoyi, a ko ina suke a duniya.  Duk da yake wasu kan yi amfani da kalmar har wa yau wajen nufin kwararru kan ilmin kwamfuta da hanyoyin sadarwa a sake ba kaidi, su kuma yi amfani da kalmar “Crackers” ga nau’in kwararru na farko.  Amma abin da yafi shahara a bakin mutane a duniya yanzu idan aka ambaci “Hackers”, shi ne kwararru masu ta’addanci ga kwamfuta.  A daya bangaren kuma, kalmar “Botnets” kalma ce mai tagwayen asali.  Daga kalmomin “Robot”, da kuma “Networks” aka tsago ta. 

A ilmin kwamfuta da tsarin sadarwa na zamani, idan aka ce “Botnets” ana nufin gungun kwamfutoci wadanda suka samo asali daga kasashe dabam-daban, da wasu ‘Yan Dandatsa suka mallake su ta hanyar miyagun masarrafan kwamfuta, kuma suke basu umarni don su darkake wasu kwamfutoci na musamman da ke wasu kasashe ko birane a duniya. Suna yin hakan ne ta hanyar amfani da kalmomi ko lambobin kwamfutocin da suke son darkakewa, wato “Internet Protocols” ko “IP Address” a turance.  Don haka, Kalmar “Hackers” tana nufin masu yin dandatsanci.  Ita kuma kalmar “Botnets” na nufin tsarin aikin ta’addancin da suke yi.  Da fatar ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.