Yadda Ake Harba Tauraron Dan Adam Cikin Falaki

A kashi na uku dai bayani ne cikakke kan yadda ake harba tauraron dan adam cikin falaki. Wannan aiki ne gagarumi, kuma ya kunshi abubuwa da dama na kimiyyar kere-kere da sararin samaniya. A sha karatu lafiya.

594

Harba  Tauraron Dan Adam Cikin Falaki

Kera tauraron dan Adam, ba ma harba shi kadai ba, wata jigila ce ta dimbin kudade da lokaci mai tsawo.  Kasancewar wannan fasaha zai je wani muhalli ne bako, mai dauke da kalubale na hakika, hakan ya tilasta wa masu kera shi yin amfani da kayayyaki masu inganci da jure wahala.  Bayan kerawa, babbar kalubale da ke tafe ita ce ta cillawa ko harba shi zuwa cikin falaki don gudanar da aiyukansa.  Wannan aiki na harbawa, shi ma aiki ne mai bukatar dimbim dukiya da kayan aiki da cikakkiyar nazari.  Wannan tasa ba kowace kasa ke gangacin fara kera tauraron dan Adam ba, balle tayi tunanin harba shi, sai kasar da ta sha ta batse wajen ilimin kimiyyar sararin samaniya, ta kuma tara dimbin dukiya.  Dangane da abin da ya shafi harbawa da kuma tafiyar da wannan fasaha zuwa cikin falaki, akwai matakai kamar haka:

Matakan Harba Tauraron Dan Adam

Harba tauraron dan Adam daga wannan duniya tamu zuwa sararinta (atmosphere) har zuwa cikin falakinta, abu ne da ke bukatar makamashin da zai tafiyar da injin roket mai wannan aiki a farkon lamari, ko kuma dukkan wani mashin da zai harba kumbon.  Bayan nan kuma, tauraron na bukatar iya kimar nisan da ya dace dashi daga wannan duniya tamu, don gudanar da aikinsa.  Mafi karancin nisan da kowane tauraron dan Adam ke bukata daga doron kasa zuwa muhallin da zai iya gudanar da wani abu, shi ne kilomita dari biyu daga ganin mai gani zuwa cikin sama.  Sannan kuma da kimar gudun tafiya na kilomita dubu ashirin da tara a duk sa’a guda (29,000 km/h), don kai wa cikin falaki.  Dole ne kowane tauraron dan Adam ya samu wadannan abubuwa biyu; tarin makamashi (na lantarki), da kuma karfin da zai tura shi zuwa cikin falaki daga doron kasa, don samun isa ga muhallinsa.  Wannan tazara da yake bukata daga doron kasa zuwa cikin sama, shi ake kira altitude  a turancin kimiyyar sararin samaniya.  Bayan haka, akwai matakai a kalla biyu, da kowane tauraron dan Adam yake wuce su kafin kaiwa ga muhallinsa cikin falaki.  Wadannan matakai dole ne ya wuce su muddin za a cilla shi ne ta amfani da roket.

- Adv -

Matakin farko shi ne tashinsa daga doron kasar wannan duniya zuwa saman sararin samaniyar wannan duniya tamu, wato atmostphere.  Wannan matakin shi ne matakin da ke lazimtar samuwar makamashin lantarki da zai sarrafa roket din da ke tunkuda tauraron zuwa can.  A kan sanya tauraron dan Adam din ne cikin wani kumbon harbawa (launch vehicle), sannan a sanya kumbon cikin kwanson roket mai cillawa. Daga nan sai a kunna wannan roket, ya dau zafi, sai ya mike kai tsaye zuwa cikin sama, a guje.  Da zarar ya wuce tarin hazo da iskar da ke saman wannan duniya, sai ya yanke daga jikin kumbon harbawan, ya fado duniya.  Sai kuma mataki na biyu, wanda kumbon da ke dauke da tauraron dan Adam din zai cika.  Da zarar roket din ya yanke ya fado kasa, sai kumbon ya cilla cikin falaki, dauke da tauraron dan Adam din.  Shi ma wannan kumbo na dauke ne da makamashin lantarkin da zai taimaka masa aiwatar da wannan aiki.

Idan aikin tauraron a iya falakin wannan duniya ne, sai kumbon ya cilla shi cikin muhallinsa kai tsaye.  Idan kuma tauraron na bukatar zuwa wata duniyar ce don gudanar da aikinsa, misali zuwa cikin falakin duniyar Mirrik (Mars), to daman kowane tauraron dan Adam na dauke ne da injin roket mai taimaka masa gudanar da aiyuka dabam-daban; don haka sai injin roket din ya harba shi zuwa duniyar, wanda mafi karancin tazarar da yake bukata ita ce kilomita dubu talatin da biyar (35,000 km) daga doron wannan kasa.  Idan ya isa falakin, sai wannan inji dai har wa yau, ya daidaita masa tsayuwa, don fuskantar jihar da yake bukata a cikin falakin. Yin hakan shi zai sa ya rika shawagi a sifar da’ira, don kewaya duniyar da yake gudanar da aikinsa a farfajiyarta.  Wannan shi ne tsarin harba tauraron dan Adam cikin falaki na farko, mai dauke da wadannan matakai biyu zuwa uku.  Har wa yau, hanyar gargajiya kenan, wato wacce aka saba amfani da ita tun tale-tale.

Amma a shekarar 1990, sai kasar Amurka ta kirikiro wani tsari da ya shafi harba taurarin dan Adam zuwa falaki ta yin amfani da jiragen sama masu nisan taku daga doron kasa.  Duk da cewa ana amfani ne da jiragen sama, wannan tsari ya kunshi yin amfani da kumbon harbawa masu amfani da injin roket.  Wadannan kumbon harbawa, wato launch vehicles, su ke cilla taurarin dan Adam din zuwa cikin falaki da zarar jiragen sun wuce dukkan gargada da galof din da ke cikin sararin samaniya.  Sai dai kuma ba kowane irin tauraron dan Adam ake iya harbawa ta amfani da wannan tsari ba, sai kanana masu karamin ruwa.  Domin jiragen ba wasu manya bane.  Don haka duk tauraron da ke da girma basu iya cilla shi zuwa cikin falaki.  Amfanin wannan tsari shi ne don rage yawan kudaden da ake kashewa wajen amfani da tsarin roket daga doron kasa don harba tauraron dan Adam zuwa sama.  Domin, kamar yadda bayani ya gabata, hakan na bukatar kashe kudade masu dimbin yawa, wanda a tsarin amfani da jiragen sama ba a kashewa.  Bayan nan, tsarin amfani da jiragen sama na rage iya matakan da tauraron dan Adam ke bi a tsarin farko, da kuma tarin makamashin da ake konawa wajen kutsawa da shi cikin gargada da galof din da ke sararin wannan samaniya namu.

Tsari na uku kuma shi ne ta amfani da Babban Kumbon Tashar Binciken Sararin Samaniya, wato US Space Shuttle, wanda ke can sararin samaniya, don cillawa  ko harba tauraron dan Adam, musamman ma manya daga cikinsu.  Wannan tasha ta binciken sararin samaniya, kumbo ne mai dauke da kwararru kan kimiyyar sararin samaniya.  Wadannan kwararru na iya harba tauraron dan Adam cikin falakinsa daga wannan tasha, kuma su lura da shawaginsa.  Yin amfani da wannan tsari na da amfani biyu manya; na farko shi ne, rage yawan kudaden da ake kashewa wajen amfani da tsarin farko da na biyu da bayaninsu ya gabata, sai kuma damar lura da tauraron da aka harba – lafiya ya isa ko ba lafiya ba? – wanda yin hakan daga doron kasa ba karamin aiki bane.  Yin sa a can, a takaice, shi yafi sauki.  Sannan kuma, duk wani tauraron dan Adam da ya samu matsala a halin shawaginsa, su wadannan kwararru da ke wannan tasha na iya dauko shi su dawo dashi doron wannan duniya tamu don a gyara shi, idan sun kasa gyara shi a can kenan.  Nan ba da dadewa ba, akwai tsarin da ake son fitowa da shi mai suna Single Stage to Orbit, ko ince Tsalle-daya Zuwa Falaki a Hausance.

Wannan tsari zai dada rage yawan matakai da kudaden da ake kashewa wajen harba tauraron dan Adam zuwa cikin falaki daga wannan duniya tamu.  Tsarin zai tanadi yin amfani ne da wani kumbon harba tauraron dan Adam na musamman, mai sifa da dabi’a irin ta Babban Kumbon Tashar Bincike da ke sararin samaniya, don harbawa da gyatta kowane irin tauraron dan Adam ne, zuwa cikin falaki.  Domin da zarar an sanya tauraron dan Adam din cikinsa, wannan kumbon zai yi jigilarsa, ya tsunduma shi cikin falaki da taku guda, ba sai an ta amfani da matakan da suka gabata ba a baya.  Wannan tsari zai rage yawan kudade da makamashin da ake kashewa wajen harba tauraron dan Adam, nesa ba  kusa ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.