Fasahar AI: Misalan Fasahar “Artificial Intelligence” a Aikace

An guba wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar jumma’a, 14 ga watan Agusta, 2020.

291

Wasu Misalai Kan Fasahar “AI”

Wannan fanni na fasahar “AI”, kamar yadda na sanar a baya, tuni an fara amfani dashi.  Yana nan birjiki a wayoyinmu na salula, kuma tuni mun dade muna amfani da manhajoji ko wasu na’urorin dake dauke dashi.  Ta bangaren sadarwa, wanda shi ne yafi yaduwa, akwai manhajoji masu fasaha (Intelligent Apps) a wayoyinmu na salula ko kwamfuta, masu dauke da wannan tsari.  Misali, wayoyin iPhone na kamfanin Apple, suna dauke da wata manhaja mai suna: “Siri”, wacce ke iya fahimtar dukkan abubuwan da kake gudanarwa a wayarka, da wuraren da kake ziyarta, da sadda kake fita gida da sadda kake dawowa aiki, da mutanen da kake yawan kira, da wadanda kake aika musu sakonnin tes, duk tana tantance su.  Haka idan akwai wasu abubuwa da ka rubuta su a kalandar wayarka don gudanar da wasu abubuwa, da zarar lokacin ya yi, nan take za ta tunatar dakai, ta hanyar murya. Idan wani kake son kira, da zarar ka umarceta da yin hakan, da kanta za ta kira maka shi kai tsaye.  Idan ka tambayeta inda ya kamata kaci abinci, nan take za ta yi nazarin inda kake, ta lalubo maka wuraren cin abinci dake unguwar da kake.  Abubuwan da take yi suna da yawa.

Daga cikin ire-iren wadannan kananan manhajoji masu fasaha akwai na kamfanin Microsoft mai suna: “Cortana”, wacce ke iya gudanar da irin wadancan ayyuka na “Siri”.  Duk da cewa tana kwamfuta ne, amma yanzu an samar da na wayar salula. Duk dabi’unsu daya ne.  Komai kake yi a kwamfuta tana lura dasu, kuma da zarar ka nemi wasu bayanai, nan take za ta gabatar maka.  Idan ma bata samu ba, za ta sanar dakai.  Idan wata kalma ce kake son a nemo maka ma’anarta, nan take za ta hau Intanet ta nemo maka.  Idan so kake ta baka shawara, abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka!  Za ka iya yin hira da ita tsaf, kamar yadda kake hira ko zance da abokinka. A daya bangaren kuma, idan kana amfani da manhajar sarrafa bayanai na kamfanin Microsoft mai suna: “Microsoft 365” ko “Office 365” ne, irin su: “Word 365” ko “Excel 365” ko “PowerPoint 365”, dukkansu suna dauke ne da wannan fasaha ta “AI” a gine.  Duk abin da kake yi na rubutu, ko zane, ko gabatar da bayanai ta amfani da “PowerPoint”, manhajar na tantance ayyukanka, kuma dasu za ta yi amfani wajen baka shawarwari.  Abin kamar maita, amma ilimi ne tsantsa.

A bangaren kamfanin Google, akwai manhajar “Google Assistant” ko “Google Voice Search”, wacce ita ma ke da ire-iren wadancan dabi’u, har ma da kari.  Wannan manhaja mai fasaha na Google, kasancewar kamfanin Google uwa ce a fannin zakulo bayanai da sarrafa su, dabi’unta suna da ban mamaki.  Tana iya tambayarka abin da kake son yi, cikin sautin mace ko namiji. Idan kace mata so kake ka karanta jaridu, nan take za ta nemo maka wadanda ke kasarku, ko inda kake ko duk inda kake so, ta baje maka su.  Sannan ma ta taya ka karanta su.  A bangaren neman bayanai kuma, manhajar “Google Search” gaba dayanta tana dogaro ne da wannan tsari.  Idan kai dan Najeriya ne, sai ka budo shafin Google daga https://www.google.com, misali, da zarar ka fara rubuta Kalma ko jumlar da kake son neman bayanai a kai, nan take manhajar za ta hankalci abin da kake rubutawa, tana hada alaka tsakaninsa da abin da wasu ko kai, a baya, ka taba rubutawa.  Idan sun dace, kafin ka gama rubutawa ta aiko maka cikakken jumlar ko Kalmar da kake son tambayowa, tare da wasu kalmomi ko jumloli masu kama dasu.  Wannan duk aikin fasahar “AI” ne.

- Adv -

Kamfanin Amazon, babban shagon sayar da kayayyaki mafi girma a Intanet a duniya, yana da nau’in manhaja mai fasaha mai suna: “Alexa”.  Wannan manhaja tana dauke ne a shafinsa na Intanet, sannan a wasu na’urorin sadarwa da yake dashi masu suna: “Amazon Kindle”.  Kwanakin baya na yi odar littafi, sai naga an yi jinkirin aiko mini bayanin rana da lokacin da za a kawo mini.  Nan take na hau shafinsu don jin bahasi, aka hada da ita.  Haka nayi ta mata tambayoyi tana bani amsa, a karshe ta sanar dani cewa inyi hakuri, zuwa gobe zan samu cikakken bayanin ranar da littafina zai zo.  Hakan kuwa aka yi; gari na wayewa sai ga sako.  Kana iya amfani da muryarka wajen bata umarni, ka saurari labarai, da bayani kan yanayi da sauransu.  Wannan manhaja, da shi kanshi gidan yanar sadarwar na Amazon, a makare suke da wannan fasaha ta “AI”.

A bangaren kamfanin Facebook kuwa, an zo gidan “Artificial Intelligence.”  Dandalin Facebook an gina shi ne, daga farko har karshensa, da wannan fasaha na “AI”.  Wannan tsari na girke ne a cikin babban injin da ke sarrafa Dandalin Facebook, wato: “Facebook Algorithm.”  Shi yasa, da zarar ka gama rajista, a matsayinka na sabon mamba, nan take sai kaga ana nuna maka hotuna da sunayen mutanen da ka sansu a zahirin rayuwa; watakila ma anguwarku daya, ko kunyi makaranta daya, da dai sauransu.  Ba maita bane, injin yayi amfani da bayanan da ka bayar ne, sai ya gina hasashe a kan cewa, “Tunda makaranta kaza kayi, kuma a gari ko kasa kaza aka haifeka, to, ba makawa dole ka san wane da wance da suke kasa kaza da makaranta kaza.”  Kashi 90 cikin 100 na abubuwan da kake gani a dandalin facebook na bayanai, duk wannan inji mai suna: “Facebook Algorigthm” ne ke sarrafa su.  Tun daga tallace-tallace da za ka gani, da wasu zauruka da za a bijiro maka (Suggested Groups) don kwadaitar da kai ka shiga, har zuwa irin labaran da kake gani idan ka hau shafinka na Facebook, duk wannan tsari ne dake girke cikin injin Facebook ke aiwatar dasu.

A karshe, galibin wayoyin salula da kwamfuta yanzu suna zuwa ne fasahar tambarin yatsu (Biometric Lock/Fingerprint), wanda da zarar ka shafa dan yatsanka sai kawai ta bude, ba sai ka yi ta hankorin shigar da Kalmar sirri ba.  Haka akwai masu zuwa fasahar bude kwamfuta ko wayar salula ta amfani da fuska (Facial Lock/Unlock).  Wayar salular da nake amfani da ita – Huawei Y9 (2019) – tana dauke da wannan tsari na fasahar “AI”. Duk wanda na taba kiranshi da wayar, ko ya taba kirana, na amsa muka yi Magana – ko bayan shekara ne – da zarar na budo lambarsa don sake kira, nan take zan ga rubutu a gefen sunansa cewa mun taba Magana da juna ta hanyar kira.  Idan layukansu biyu ne a wayata, wacce muka yi waya dashi ta karshe, ita ce za a sanya wa alama.  An dabi’antar da wayar ne tun wurin kera ta, da irin wannan siffa, ta amfani da wani tsari mai suna: “Supervised Learning”, karkashin fannin “Machine Learning” da bayaninsa ya gabata a baya.  Dukkan wadannan tsare-tsare sun samu ne ta hanyar wannan fasaha ta “Artificial Intelligence”, wato: “AI”.

Masana harkar sadarwa da dabi’un dan adam suka ce a yanzu dai, babu wanda yafi kowa sanin dan adam irin wayar salularsa, da kwamfutarsa, da kuma shafukan Intanet din da yake ziyarta.  Wayarka tafi matarka, da dan uwanka, da abokanka sanin hakikanin sirrinka.  Wannan zance yafi gaskatuwa a kasashen da kusan dukkan jama’a na gabatar da rayuwarsu ne ta hanyar wadannan na’urori da kafafen sadarwa.  Domin wayarka ce kadai ta san wa da wa kake kira ko suke kiranka.  Wayarka ce kadai tasan wasu shafukan Intanet ne kake ziyarta; a bayyane ko a boye.  Gidajen yanar sadarwa ne kadai suka san wani shafi ka hau, kuma me da me ka aiwatar a shafin.  Wayarka ce ta san ina kaje yau, ta wani titi ka bar gidanka, ta wani titi ka dawo gidanka.  Wayarka ce kadai ke sanin hotuna nawa ka dauka, sannan wa da wa ka aika musu.  Wayarka ce kadai ke sanin mutum nawa ka rubuta wa sakon tes, kuma mutum nawa ne suka rubuto ko aiko maka.  Ita ce har wa yau ta san, cikin sakonnin da kake aikawa ko aka aiko maka, guda nawa ne ka goge, sannan guda nawa ne ka boye su a wayarka.  Shafin Youtube, da Dandalin Facebook, da manhajar TikTok, da WhatsApp, da SnapChat, duk sun fi kowa sanin abokan huldarka, da jujjuyawarka.  A takaice dai, wadannan na’urori da kafofin sadarwa sun samu wannan kudura ne ta hanyar wannan fasaha ta “Artificial Intelligence”.  Bayan su, ba wanda ya san abin da suka sani kanka, sai Allah Mahaliccinka.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.