Sakonnin Masu Karatu (2022) (4)

Manhajar Binance da Yadda Ake Amfani da Ita

Wanda ya samar da wannan kamfani ko shafi shi ne: Changpeng Zhao, wanda dan asalin kasar Sin ne.  Ya yi hakan ne a shekarar 2017, wato shekaru 5 da suka gabata kenan.  Wannan mutum, wanda ake wa lakabi da “CZ”, kwararren maginin manhajar kwamfuta ne.  Zuwa yanzu dai, wannan cibiya ta hada-hadar kudaden zamani ta Binance, ita ce cibiya mafi girma a duniya, cikin cibiyoyin hada-hadar kasuwanci guda 500 da ake dasu a yanzu. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 2 ga watan Satumba, 2022.

188

Kamar yadda muka saba lokaci zuwa lokaci, daga wannan mako zuwa makonni biyu dake tafe, za mu amsa wasu daga cikin tambayoyinku ne.  Kuma kamar yadda muka sha maimaitawa a baya, idan an tashi aiko sakonni a rika kyautata rubutu, sannan a sanya adireshi, don tantance wanda ke aiko sako.  A karshe, a kiyaye wajen maimaita tambaya kan abin da muka sha maimaita shi a baya.

———————–

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka.  Da fatan kana lafiya tare da iyalinka.  Ina son karin bayani ne kan manhaja ko shafin “Binance”.  Shin, mene ne ake yi a wannan shafi, kuma mene ne amfaninsa a bangaren sadarwa na zamani?  A karshe, a matsayina na mai son ta’ammali da kafafen sadarwa na zamani, ta wace hanya zan iya amfana da wannan shafi?  Da fatan zan samu gamsasshen bayani.  Na gode. – Abubakar Dan Isa, Hayin Rigasa, Kaduna, Najeriya: danisa2000@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Abubakar.  Ina godiya matuka da addu’a.  Allah saka da alheri, amin.  Wannan tambaya taka tana dauke ne da bangarori guda uku mahimmai, kuma zan yi iya kokarina wajen ganin na amsa su gwargwadon fahimta, ba tare da tsawaitawa mai gimsarwa ba.

Binance.com

Wannan kalma ta “Binance” dai na ishara ne ga abubuwa guda uku, kowanne daga cikinsu na da alaka da dan uwansa ne.  Da farko dai, kamfani ne, sannan kuma gidan yanar sadarwa ne, wato: “Website”, kuma manhaja ce da ake amfani da ita wajen gudanar da hada-hadar kudaden zamani ta hanyar Intanet, wato: “Cryptocurrency”.  A baya munyi bayani gamsasshe kan ire-iren wadannan na’ukan kudade na zamani, a doguwar makalarmu mai take: “Fasahar Digital Currency, da Virtual Currency, da Cryptocurrency”.  A takaice dai, wannan shafi, cibiyar hada-hadar kudaden zamani ne, wato: “Cryptocurrency Exchange”.  Yadda ake hada-hadar hannayen jari a cibiyar “Nigerian Stock Exchange”, misali, haka ake hada-hadar wadannan kudade na zamani a wannan kafa ta Binance.

- Adv -

Wanda ya samar da wannan kamfani ko shafi shi ne: Changpeng Zhao, wanda dan asalin kasar Sin ne.  Ya yi hakan ne a shekarar 2017, wato shekaru 5 da suka gabata kenan.  Wannan mutum, wanda ake wa lakabi da “CZ”, kwararren maginin manhajar kwamfuta ne.  Zuwa yanzu dai, wannan cibiya ta hada-hadar kudaden zamani ta Binance, ita ce cibiya mafi girma a duniya, cikin cibiyoyin hada-hadar kasuwanci guda 500 da ake dasu a yanzu.  Sannan akwai nau’ukan kudaden zamani sama da 387 da ake hada-hadarsu.  A duk mako wannan cibiya ta Binance tana samu maziyarta shafin guda miliyan 17 a takaice.

Me Ake Yi a Binance?

Kamar yadda na bayyana a sama, wannan cibiya ta Binance ana gudanar da hada-hadar kudaden zamani a ciki.  Akwai nau’ukan kudaden zamani da ake kira “Kiripto”, a gurbatacciyar Hausar zamani, irin su: “Bitcoin”, da “Etha”, da “XRP”  da sauransu.  Mutane kan yi rajista a shafin Binance da sauran makamantanta,  irin su Coinbase, da FTX, da Kraken. Bayan rajista, kana iya zuwa kudi a lalitarka, sannan ka sayi nau’in kudin da kake son saya.  Bayan wasu lokuta idan farashin kudin ya tashi sama, sai ka sayar don samun riba.  Ba wannan kadai ba, cibiyar Binance na da na’ukan fasahohin aiwatar da kasuwancin Kiripto kala-kala.  Hatta bashi kana iya ci, don sayan kiripto, idan ka sayar sai ka biya.  Wannan shi suke kira: “Margin Trading”.  Bayan shi ma, kana iya cin bashin nau’in kudin kiripto don rikewa idan farashinsa ya tashi ka sayar don samun riba. Wannan shi ake kira: “Cryptocurrency Lending”.  Sai dai wannan nau’i na bashi ko aron kudi, yana dauke ne da kudin ruwa, wato riba (Interest).  Wanda kuma a musulunci haramun ne.

Har wa yau, wannan cibiya ta Binance na dauke da hanyoyin ajiyan kudade daban-daban ne.  Kana iya amfani da taskarka na banki,  ko katin ATM dinka, kai tsaye don zuba kudi a lalitarka ta Binance.  Ko kuma, kayi amfani da taskar ajiyarka ta dala ko fam na Ingila; duk cibiyar na dauke da wadannan damammaki.  Haka idan ka tashi sayayya, kana iya aika kudi ta amfani da katinka na ATM na Naira, ko na dala, ko kuma, kayi amfani da tsarin P2P (Peer-to-Peer), wanda ke bai wa masu cinikayya daman ciniki da juna kai tsaye, ba tare da amfani da manhajar Binance ba wajen biya ko karban kudade.  Musamman ga wadanda suke Najeriya, inda Babban Bankin Kasa (CBN) ya haramta wa bankuna aiwatar da hada-hadan kudaden zamani, saboda hadarin dake tattare dasu.

Me Zan Samu na Fa’ida?

Ya danganci bukatarka.  Idan kana da sha’awar aitawar da kasuwanci irin wannan, akwai riba sosai, sannan kuma akwai hasara; ya danganci manufarka, da iya jajircewarka wajen fuskantar hadari ko hasara a kasuwanci.  Abin da ya kamata ka fahimta shi ne, kasuwancin kiripto hanya ce ta samun kudi sosai, sannan kuma hanya ce ta hasara mai girma.  Hakan ya faru ne saboda saurin hauhawa da saukan farashin wadannan kudade, musamman ma Bitcoin.  A halin yanzu kasuwar kiripto ta yi kasa sosai, tun daga watan Nuwamba na shekarar 2021.  Ya zuwa yanzu, farashin Bitcoin ya rushe da kashi 68.  Haka ma sauran kudade irin su Etha da XRP.  Kananan kudade masu kawo riba a baya irin su Shiba Inu (SHIB), sun yi kasa sosai.  Wasu na’ukan kudaden ma sun rushe baki daya, saboda tabarbarewar kasuwar baki daya.  Hakan kuwa ya biyo bayan daga farashin kudaden ruwa ne a kasashen Amurka da sauran kasashen Turai, da yakin Rasha da Yukirain da ake ta fafatawa yanzu.

Wannan, a takaice, shi ne dan abin da ya sawwake daga bayani.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.