Sakonnin Masu Karatu (2012) (1)

Saboda wasu dalilai da suka sha karfina ba zan samu ci gaba da kasidar da muka faro makonni uku da suka gabata ba a yau, sai dai mako  mai zuwa in Allah yaso.  A bi ni bashi don Allah. A yau ga wasu daga cikin sakonnin da kuka aiko a baya.  Da fatan za a gafarce ni. A sha karatu lafiya.

71

Salamun Alaikum Baban Sadeeq, yaya jama’a?  Allah yasa mu dace, amin.  Don Allah yaya ake yi a fim a mayar da mutum tagwaye (‘yan biyu)?  Daga Alhassan  

Wa alaikumus salam, Malam Alhassan da fatan kana lafiya.  Hakan kan kasance ne ta hanyar amfani da na’urar daukan hoto na zamani, wacce ke da ire-iren wadannan hanyoyin dabaru masu ban mamaki.  Bayan na’urar daukan hoto, akwai masarrafa ko manhajar kwamfuta mai iya aiwatar da wannan aiki cikin sauki.  Idan ka kalli fina-finai irin su Matrix misali, za ka ci karo da abubuwa masu ban al’ajabi wadanda wasu ma kana iya rantsewa ba za su iya faruwa ba, amma a fim suna faruwa.  Shi yasa ake kiran fim a hausance da suna “Shiri.”  Ma’ana wani abu ne aka shirya, ba wai hakika bane; kawalwalwaniya ce kawai.  Da fatan ka gamsu.


Salamun Alaikum Baban Sadiq, da fatan kana lafiya da dukkan ma’abota wannan shafi mai albarka. Ina son saka kalmomin izinin shiga (Password) na Facebook, amma ban san yadda ake yi ba.  Daga Abubakar Aminu mai Cingam, Legas: 07031105049

Wa alaikumus salam Malam Abubakar, akwai sarkakiya kadan cikin tambayarka.  Shin, daman can kana da shafi ne a Facebook?  In eh, kenan ka mance kalmominka kenan.  Idan kuma a a, to, ai daman babu yadda za ayi ka iya shigar da kalmomin shiga tunda baka bude shafi ba.  Idan ka mance ne, akwai shafi da zasu kaika inda za a maka tambayoyi, da zarar ka amsa tambayoyin sai a aiko maka da fam din da za ka cika don canza wata sabuwar kalmar shiga.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum, Allah ya saka maka da alheri.  Ina son ka aiko mini da kasidar “Tsibirin Bamuda” da wacce ake tsara “Facebook” ta wannan adireshin Imel: aliyusadis@gmail.com.  Daga Aliyu Sadis, Minna, Neja: 08064022965

Wa alaikumus salam, Malam Aliyu ka gafarce ni saboda jinkirin amsa maka bukatunka.  Ka duba jakar Imel dinka, tuni na tura maka. Allah amfanar da mu baki daya, amin.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, don Allah a taimaka a mana cikakken bayani kan yadda ake canza kalmomin izinin shiga a shafin Facebook.  Daga Nura Sahabi, Pangamu, Gangare, Suleja: 08034145643

Wa alaikumus salaam, Malam Nura, bayani kan yadda ake canza kalmomin shiga shi ne: ka je “Settings” a shafinka, ka gangara inda ake canza kalmomin shiga, wato Password, sai ka canza.  Wannan ba wani abu bane mai wahala.  A waya kake ko a kwamfuta.  Allah sa a dace.


- Adv -

Salaamun alaikum Baban Sadiq, Allah ya taimake ka.  Wai me ake nufi da shafin musayar hoto na Pinterest, da kuma shafin Microsoft?  Kuma yaya ake amfani dasu ne?  Daga Aminu Sadauki, Unguwar Dosa, Kaduna: 07032958029

Wa alaikumus salam, Malam Aminu barka ka dai. Shafin Pinterest dai shafi ne da ake musayar hotuna, kamar yadda ka fada.  Amma kafin ka fara amfana da hotunan wasu, sai ka yi rajista, sannan ka nemi abokai wadanda za ka iya musayar hotuna dasu.  Kana da damar loda hotunanka, ka kuma killace wadanda kake son musayar wadannan hotuna da su daga cikin mambobin wannan Dandali.  Shafin Pinterest na daga cikin shafuka ko Dandalin Abota da suke tashe a wannan zamani, bayan dandalin Facebook.

A daya bangaren kuma, shafin Microsoft dai gidan yanar sadarwar kamfanin Microsoft Inc. ne da ke kasar Amurka, wanda Bill Gates da abokinsa Paul Allen suka kafa tun shekarar 1975.  A halin yanzu wannan shafi na dauke ne da bayanai kan dukkan hajojin wannan kamfani da ke gina manhajar kwamfuta, babba da karami.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikium Baban Sadik, yaya aiki?  Da fatan kana lafiya.  Wai me yasa idan mutum ya kira wani, sai a nuna masa cewa: Call is being Diverted?  Na gode.  Daga Usman Muazu Funtua, Katsina: 08106067660

Wa alaikumus salam, Malam Usman, a duk sadda ka ga haka, to alama ce da ke nuna cewa lallai mai layin ya toshe layin ne, don juya dukkan masu kiransa zuwa wani layin daban; ko don saboda matsalar rashin ingancin yanayin sadarwa, ko don rashin kudi a layin, ko wasu dalilai dai da shi kadai ya sani.  Kana iya hakan me ta hanyar hadin gwiwa da kamfanin waya, wanda hakan ke samuwa a cikin kowace wayar salula na zamani.  Da fatan ka gamsu.


Gaisuwa ta musamman ga Baban Sadik.  Ina maka fatan alheri, Allah ya kara maka basira, amin.  Tambayata ita ce: wane dalili ne yake haifar da rufewar Imel (Emel Blocking or Invalidating of Email), sannan ta wace hanya za a iya budewa (Unlock), bayan kamfanin manhajar Imel (irin su Yahoo, ko Gmail, ko Hotmail) ya rufe?  Daga Kabir Ibn Usman, Abuja.

Malam Kabir Usman, barka ka dai. Ban da masaniya dangane wadannan kalmomi da kayi amfani dasu wajen bayanin tambayarka, a ilimance.  Amma na fahimci inda tambayar ta dosa.  Akwai hanyoyi biyu da kamfanin manhajar Imel ke rufe wa mai jakar Imel akwatin Imel dinsa.  Hanyar farko ita ce dadaddiyar hanya.  Hakan na faruwa ne idan mai jakar Imel yayi watanni 6 bai shiga akwatin Imel dinsa ba, sai a rufe. Wannan rufewa shi suke kira: Deactivation.  A duk sadda ka tashi shiga za a sanar da kai halin da akwatin Imel din ke ciki.  Amma za a nuna maka hanyar budewa, wato: Reactivation kenan.  Amma a yanzu ma kamfanonin manhajar Imel sun daina amfani da wannan tsari.

Sai hanya ta biyu, wacce ke samuwa sanadiyyar canza tsarin shiga Imel dinka, ko na’urar da kake amfani da ita wajen shiga.  Misali, idan ka saba shiga akwatin Imel dinta ta hanyar kwamfuta ce, sai kwatsam watarana ka bukaci shiga ta hanyar wayar salularka a karo na farko, kamfanin manhajar Imel zai dauka ba kai bane, wani ne ke kokarin shiga ba izini, don haka sai a toshe akwatin, ace sai ya fadi ranar haihuwar da ya bayar a sadda yake cike fam din bude akwatin, ko a ce ya fadi amsar tambayar sirri da aka masa sadda yake bude akwatin.  Masu Dandalin Facebook ma kanyi amfani da wannan tsari wajen tantance hakikanin mai shafi idan ya shiga ta hanyar da bai saba ba.

Abin da wannen ke nufi shi ne, a duk sadda kake shiga akwatin Imel dinka, ko shafinka da ke Dandalin Facebook, akwai masarrafa ta musamman da ke haddace hanyoyin da kake shiga shafin ko akwatin dasu.  Duk sadda aka samu sauyi, to za a tuhumi wannan sauyi ta hanyar neman tantancewa.  Idan shafinka ne, sai ka bayar da bayanan da aka tambayeka, muddin ka kasa kuma, to ba za a taba bari ka shiga shafin ba.  Don haka, zaman lafiyarka daya ne; ka fadi amsar tambayar da aka maka.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.