Fasahar 5G: Asali da Tarihin Samuwar 5G (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 10 ga watan Yuli, 2020.

235

Asali da Tarihin Samuwar Fasahar “5G” (1)

Bayan nazari kan amfani da fa’idojin da wannan fasaha ke dauke dasu, kuma muke sa ran su amfani bil’adama a duniya, a yau za mu dubi yadda aka yi wannan fasaha ta samu ne a duniya. Abu ne sananne cewa ba wata kasa bace ko kungiya daya ta samar da wannan fasaha, haka ma abin da ya shafi tsare-tsaren da suke da alaka da ita. Da farko dai, wadanda suka samar kuma suke tafiyar da tsare-tsaren ka’idojin sadarwar da wannan fasaha ta ginu a kai su ne: Hukumar Sadarwar Wayar Tarho ta Duniya, wato “International Telecommunications Union”, ko “ITU” a gajarce, wadda hukuma ce karkashin majalisar dinkin duniya. Sai kuma kungiyar dake lura da samar da ka’idojin sadarwar Intanet a wayar salula.

Wadannan kungiyoyi biyu, ta hadin kai da hukumomin sadarwa na kasashen duniya, su ne suka ko suke jibintar daidaita ka’idajojin sadarwa da marhalolin tsarin sadarwar wayar salula da suka gabata, da wadanda ake amfani dasu a yanzu, suke dogaro ko gudanuwa a kai. Amma abin da ya shafi aikatawa ko dabbaka wadannan ka’idoji a na’urorin sadarwa na zamani na kasashe, da kuma tashoshin sadarwa na wayar salula, nauyin kasashe ne da kungiyoyi ko kamfanonin sadarwa na wayar salula dake da sha’awar yin hakan. Ba dole bane wai don an samar da wadanann ka’idoji, ace dole sai kowace kasa ta dabbaka su. Harka ce ta kasuwanci da maslahar al’umma, ga kasa ko kamfanin da yaga cewa zai iya. Don haka, idan Najeriya tace ita baza ta dabbaka wannan tsari na “5G” ba, to, ba abin da tayi na taka doka. Kuma wayarka ko tsarin 10G take dashi misali, baza ta iya amfanuwam da shi ba, tunda babu tsarin a kan na’urorin sadarwar kasar baki daya.

A halin yanzu da muke Magana dai wannan tsari na “5G” ya fara game duniya, inda aka samu kasashe da kamfanonin sadarwar dake kasashen suka dora tsarin a kan na’urorin sadarwarsu, don dacewa da zamanin da ake ciki. Amma kafin nan, tunanin samar da wannan tsari, da yunkurin gudanar da bincike kansa, ya faro ne sama da shekaru goma da suka gabata:

Shekarar 2008

- Adv -

Yunkurin samar da wani abu mai kama da tsarin fasahar “5G” dai ya samo asali ne cikin watan Afrailu na shekarar 2008, lokacin da hukumar binciken sararin samaniya na kasar Amurka mai suna NASA, ta hadin gwiwa da Geoff Brown da wani kamfanin kimiyya da aka fi sani da suna: “M2Mi”, wato: “Machine to Machine Intelligence,” suka samar da wata yarjejeniya don gunadar da bincike na musamman kan tsarin fasahar “5G”.
A cikin wannan shekara ta 2008 dai har wa yau, kasar Koriya ta Kudu – South Korea – ita ma ta kaddamar da wani tsari na bincike da zai samar da ka’idojin sadarwa a tsarin fasahar “5G”, amma ta amfani da hanyar isar da sako nau’in “Beam-Division Multiple Access.” Wannan tsari ne dake taimakawa wajen isar da sako ta hanyar wayar iska ta amfani da hasken lantarki mai dauke da bayanai a tsarin siginar rediyo (ba rediyon da muke sauare ba), kuma ta hanyoyi masu yawa, a lokaci guda.

Shekarar 2012

A watan Agosta na shekarar 2012 sai Jami’ar New York (New York University) dake kasar Amurka ta samar da tsangayar bincike na musamman mai suna: “NYU Wireless”, wanda zallar abin da zai mayar da hankali a kai shi ne, gudanar da bincike mai zurfi a marhalar farko kan tsarin fasahar “5G”.

Bayan wata biyu, cikin watan Satumba na shekarar 2012 dai har wa yau, sai Gwamnatin Burtaniya ta hadin gwiwa da Cibiyar Tallafin Binciken Ilimin Kimiyya na kasar mai suna “UK Research Partnership Investment Fund” suka baiwa Jami’ar Surrey (University of Surrey) dake kasar Ingila tallafin zunzurutun kudi har fam miliyan talatin da biyar (£35 million), don kafa cibiyar gudanar da bincike na musamman kan tsarin sadarwa na fasahar “5G”. Daga cikin wannan adadi na kudi akwai kamfanonin sadarwar wayar salual dake kasar irin su: Samsung, da Huawei, da Fujitsu da suka ba da nasu tallafin, da sharadin zasu zaman a farko da za a fara gudanar da gwajin wannan fasaha ta amfani da na’urorinsu na sadarwa, idan har an kammala.

A ranar 1 ga watan Nuwamba na shekarar 2012 ne Hukumar Tarayyar Turai, wato: “European Union” ko “EU” a gajarce, ta kaddamar da bincike ita ma kan wannan fasaha ta “5G”, don samar da wani ingantaccen tsarin sadarwa na wayar-iska da zai saukake wa al’ummar nahiyar turai rayuwa ta kowane fanni, daga shekarar 2020 zuwa abin da Allah Yaso. Wannan bincike ya ta’allaka ne kacokam kan tsari da ka’idojin sadarwa na fasahar “5G”. Wannan shiri na EU dai shi ne daga baya ya jagoranci samar da ginannun ka’idojin sadarwar da fasahar “5G” a duniya gaba daya, ta hadin gwiwa da hukumar ITU, wato hukumar lura da tsarin sadarwar wayar salula ta duniya.

A cikin watan Nuwamban ne dai har wa yau mai suna: “iJOIN EU” a nahiyar Turai, wanda ya mayar da hankali wajen samar da fasahar sadarwa a kananan kadadar sadarwa mai suna: “Small Cell Technology”. A cewar kwamishinan lura da harkar sadarwar zamani a nahiyar turai na wancan lokaci mai suna: Gunther Oettinger ya tabbatar, cewa: “Amfani da titin sadar da bayanai mai inganci na cikin mahimman ginshikan tsari da fasahar 5G.” Wannan shiri na “iJOIN EU” dai na cikin tsare-tsaren farko nag aba-gaba da hukumar tarayyar turai, wato EU, ta samar wajen nuna wa duniya nasarar da take samu a farkon lokaci don yiwuwar samuwar wannan tsari na fasahar “5G”, a babban taron sadarwar wayar salula ta duniya da aka gabatar a birnin Baselona (Barcelona) na kasar Spain a shekarar 2015.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.