Tsaunuka Masu Aman Wuta (3)

Ga kashi na uku na binciken da muke ta faman yi kan tsaunuka masu aman wuta, wato: Volcanic Moutains.

444

Abu na farko da ke makare a karkashin tsaunin dai, kamar yadda muka sanar, shi ne damamme, kuma tafasasshen “kunun dutse”.  Na kira shi da kalmar “kunu” ne saboda a dame yake, da kaurinsa, kamar kunun gari (ko “jaguda”, ga wadanda suka santa).  Na kira shi “tafasasshe” ne saboda yana da matukar zafi.  Saboda tsananin zafinsa ma, launinsa ja ne, zur!  A karo na karshe, na danganta shi da “dutse” ne (na ce “kunun dutse”) saboda asalinsa kenan.  Dutse ne aka rababbaka shi, ya zama damammen kunu, mai kauri, kuma ja zur.  Mai karatu ba zai fahimci yadda abin yake ba sai ya ganshi a fili, ko kuma ya kwatanta shi da “damammen kunun karfe”, wanda masana’antar karafa ke narkawa kafin su sandarar da shi zuwa ga abin da suke son kerawa. Hakan ma a babin kwatance ne, ba wai daidai zafinsu daya ba.

Wannan kunun dutse da ke makare a karkashin tsaunin dai yana da matukar zafi.  Masu bincike sun sanar da cewa mafi karancin zafinsa shi ne dari bakwai, a ma’aunin zafi na santigireti (700c).  A can sama kuma, ya kai dubu daya da dari uku, a wannan ma’auni (1,300c)!  Yana cakude ne da sinadaran kimiyya da dama.  Daga cikinsu akwai sinadarin gilas, kuma a dauke yake da wata masifaffiyar iska mai kumfa a samansa.  Da zarar zafi ya kai zafi, sai wannan masifaffiyar iska ta fetso shi waje, da zafinsa, da kuma kaurinsa. Wannan kunun dutse shi ne ake kira Molten Magma, a Kimiyyance.  Kuma shi ne asalin dautse nau’in Igneous da muka sani; wato dunkulalle kuma tsantsar dutse kenan.

Wannan shi ne abu na farko da ke fitowa daga karkashin tsauni mai amai, tare da wannan iska, da zafi da kuma sinadaran da ke tattare da shi. Da zarar ya fito, sai ya sake suna, da kuma yanayi.

- Adv -

Wannan ya kawo mu ga nau’in abin da ke samuwa na biyu, a yayin aman tsauni.  Fitowar wannan kunun dutse ke da wuya sai ya kasu kashi biyu.  Kafin bayanin nau’insa, duk sadda wannan kunun dutse ya fito waje, sunansa ya tashi daga Molten Magma ko Magma, ya koma Lava, ko Lava Flows.  Shi wannan Lava ko kace Sandararren Kunun Dutse, shi ne ke yin ambaliya daga saman tsaunin, ya fara gangarowa, kafin ya sandare ya zama dutse curarre.  A yayin gangarowarsa ne yake yin iya barnar da yake yi, musamman idan tsaunin a kusa yake da wani kauye, kuma cikin dare aman ya faru.  Wanda ke gangarowa ko yin ambaliya, shi ake kira Active Lava, kuma shi ne mai haddasa wuta da ke ci balbal a duk sadda aman ya faru.  Wannan ke nuna mana cewa shi tsaunin ba wai wutar yake amanta ba, a a, sinadaran wutar yake amayowa.  Wannan nau’i na sandararren kunun dutse mai ambaliya, shi yafi komai barna a lokacin da yake fitowa.

A tarihin tsaunuka masu amai, akwai garuruwa ko kauyuka masu yawa da suka kone ko suka tashi karfi da yaji, sanadiyyar wannan ambaliya mai hadari.  Misali, akwai wani kauye da ke Jumhuriyar Kwango, ko tsohuwar Zayar ta da, wanda tsaunin Nyiragongo ya kona sanadiyyar aman da yayi cikin dare, lokacin da ‘yan kauyen ke bacci.  Haka ma kauyukan Kaimu, da Kalapana, da Kapoho, da Kewaiki, duk kauyuka ne da tsaunin Kilauea da ke Tsibirin Hawaii na kasar Amurka ya kona, sanadiyyar aman da yake yi a-kai-a-kai.  Haka ma akwai kauyen San Sebastiano al-Vesuvio da ke kasar Italiya, wanda tsaunin Vesuvius ya kona a shekarar 1944.  A kasar Filifins ma akwai wani kauye da Tsaunin Cagsawa ya kona.  Wadannan su ne garuruwa ko kauyukan da wannan sandararren kunun dutse mai malala a farfajiyar tsauni ya kora ko kona, tare da salwantar da rayuwan mazauna cikinsu.

A daya bangaren kuma, akwai kauyuka ko garuruwan da yayi musu mummunan ta’asa. Wadannan kauyuka sun hada da: kauyen Catamina da ke kasar Italiya, wanda Tsaunin Etna yayi wa ta’asa a shekarar 1669, sai garin Goma da ke Jumhuriyar Kwango Kinshasa, a shekarar 2002, da garin Haiwaey da ke Tsibirin Iceland, wanda tsaunin Eldfell ya raunata a shekarar 1973.  Har wa yau akwai kauyen Royal Gardens da ke Tsibirin Hawaii na kasar Amurka da ya sha lugude a shekarar 1986-87, sai kuma wani kauyen San Juan na kasar Meziko mai suna Paricutin.  Wannan shi ne galibin ta’adin da wannan sandararren kunun dutse mai gangarowa daga saman tsauni ke yi a daidai lokacin da tsaunin ke amai.  Nau’i na biyu kuma shi ne wanda ya riga ya kame, sanadiyyar hucewar da yayi bayan ya gangara, ko ya samu wani kududdufi ya kwanta.  Wannan nau’i shi ake kira Passive Lava, wato nau’i mara illa kenan.  Idan ya riga ya kame, to nan take yake zama wani nau’in taki mai matukar alfanu wajen harkar noma.  Ka ji wata hikimar Ubangiji kuma!

Don haka wasu lokuta ake samun wasu kauyuka da ke kusa da tsauni mai aman wuta, wadanda ko an ce su tashi sai su ki.  Ko da ya musu ta’adi sanadiyyar aman da yayi, za su sake dawowa inda suke a da.  Wannan ma ya sa a Tsibirin Hawaii na kasar Amurka akwai kauyukan da sun kone sanadiyyar wannan ta’adi, amma daga baya sai hukuma ta sake gina su.  Mazauna wurin na yin hakan ne sanadiyyar albarkar noma da suke samu.  Domin duk kasar da wannan sinadari na Lava yayi ambaliya a kanta, to za ta zamo mai matukar albarka ta fuskar noma.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.