Kimiyya da Fasaha a Kasashen Musulmi (7)

Ayyukan Cigaban Kimiyya A Qasashen Musulmai A Yau 

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 24 ga watan Disamba, 2021.

425

Kamar makonnin baya, za mu ci gaba da fassarar maqalar Farfesa Jim Al-Khalili, wanda qwararre ne a fannin nazarin kimiyyar Fiziyar Nukiliya (Theoritical Nuclear Physics) a Jami’ar Surrey dake qasar Burtaniya.  Mai fassara shi ne Malam Muddassir S. Abdullahi, kamar yadda bayani ya gabata a makonnin baya.  A sha karatu lafiya.

——–

Ayyukan Cigaban Kimiyya A Qasashen Musulmai A Yau 

Bari mu xan yi duba ga qasashen dake Yankin Gabas ta Tsakiya, wato Middle East, za mu iya ganin yadda suka samar da sababbun manya-manyan ayyukan (projects) da al’ummar yankin kullum ke karvarsu hannu bibbiyu. Da farko, mu fara da sabuwar alqarya ko birnin kimiya, wato “Science Park” da aka buxe a lokacin bazara (a can Turai) na shekarar 2009 a sabon birnin da ake kira da “Madinatul Ilm” a harshen Larabci, a wajen babban birnin qasar Qatar da ake kira da Doha.

- Adv -

Shi wannan birnin, ya gayyaci manya-manyan jami’o’i na duniya  ne dake ajin farko domin su buxe rassansu (Campus). Waxannan jami’o’I dai sun haxa da Jami’ar Carnegie Mellon, da Jami’ar Texas A&M, da kuma Jami’ar Northwestern, dukkaninsu daga qasar Amurka. Har wa yau dai, a cikin wannan birni na kimiyya na Qatar, akwai yankin da ake kira da “Qatar Science and Technology Park”, wanda maqasudin samar da wannan matattara, shi ne don qyanqyasar jiga-jigan kamfanonin fasahar kere-kere a duniya (High-tech Companies) don kawo sauyi, da kuma maraba da duk wasu kamfanoni na fasaha da mutum zai iya tunani. A taqaice dai, suna son samar da gagarumar nasarar nan da yankin nan jihar California da ake wa laqabi da “Silicon Valley” ya haifar wa duniya a fagen fasahar zamani a matakai daban-daban ne.

Sai kuma katafariyar jami’ar nan ta qasar Saudiyya dake kusa da yammacin birnin Jeddah mai suna King Abdullah University of Science and Technology (KAUST) da ta lashe miliyoyin daloli har miliyan dubu goma na dalar Amurka ($10bn). Domin qarin bayani a kan wannan katafaren aiki, za a iya duba babbar jaridar nan ta ilimin fiziyya mai suna Physics World, ta water Nuwambar 2009, shafi na 12-13.  Wani abin ban sha’awa ga wannan katafaren aikin shi ne yadda wannan katafaren jami’ar ta shiga sahun cibiyar binciken kimiyya na zamani (International Research University). Ga da xakunan gwaje-gwajen kimiyya da fasaha na kece-raini.  Bayan haka, jami’ar ta ware dala na gugar dala har dala miliyan dubu xaya da rabi ($1.5bn) kacokan tsangayoyin bincike, wato “Research Facilities” a shekaru biyar na farkon buxe makarantar.

A wani salo da ba a tava gani ba a qasar, wannan jami’ar ita ce jami’a ta farko a qasar da ta bi tsarin gudanar da koyarwa tsakanin mata da maza a haxe a xakuan karatu, ba kamar yadda aka san ana yi ba na zaman su daban-daban.   Har wa yau dai, ita wannan jami’ar, ta ci alwashin sakarwa masana da masu bincike da nazari, sakakken ‘yanci na yin duk wani bincike ko kawo nazarce-nazarce da za su kawo sauyi ga duniya. Haka kuma, ta shimfixa tsarin gudanar da ayyukan bincike kacokan ne kan tsarin da zai tabbatar da qasar Saudiyya ta dogara da kanta, a lokacin da farashin albarkatun man fetur ke ja baya a duniya.

Har wa yau, akasarin binciken da za a rika gudanarwa a jami’ar sun qunshi yadda qasar za ta amfana ne xari bisa xari, musamman vangaren hasken ranar da Allah ya azurta ta da shi, da kuma samar da irin shuka, da za su iya rayuwa da yaxo a yankin nasu mai cike da tsananin zafin rana da kuma qarancin ruwa.   Shi yasa jami’o’i da yawa dake Yankin Turai da kuma Amurka ke ta qoqarin yadda za su samu damar qulla alaqa da wannan jami’a ta Sarki Abdullah – fatan dai ya zamanto domin bunqasa ilimi da bincike suke ta hanqoron ba domin ximbin dukiya da arziqi da qasar ke da ita ba.

Misali na qarshe kan irin waxannan manya-manyan ayyukan domin farfaxowa daga koma baya da qasashen Musulmai da Larabawa ke ciki a vangaren binciken kimiyya da fasaha da sauran qere-qere, shi ne wani katafaren aiki da ake wa laqabi da “SESAME” a gajarce, ko kace: “Synchrotron-light for Experimental Science and Applications in the Middle East” (Dubi sananniyar jaridar nan ta fiziyya ta qasar Amurka mai suna “Physics World”, na watan Afrailu, 2008 shafi: 16-17).   Ana hasashen wannan aiki zai zamanto sanadin samuwar qasaitacciyar cibiyar bincike da nazari ta duniya, (International Research Center), ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.