Facebook Gidan Rudu: “Mu Hadu a WhatsApp, Ya Fi Sirri”

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

565

“Mu Hadu a WhatsApp, Ya Fi Sirri!”

Wannan shi ne galibin zancen samari da ‘yan mata idan suna son su fara hirar batsa ko aika wa juna hotunan batsa, yayin da suke hira ta Inbox a Facebook.  Tsakanin Facebook da Whatsapp, kashi 70 cikin 100 na hiran samari da ‘yan mata duk na batsa ne.  Bayan hirar saurayi da budurwa a killace, akwai Zauruka birjik a Whatsapp na mata zalla, ‘yan mata kenan, da na maza zalla, samari kenan, da na cakuden maza da mata marasa aure, da matan aure zalla, da na cakuden matan aure da zawarawa.

A wasu lokuta akan samu budurwa daya ko biyu a zauren matan aure zalla, idan suna da uwa a gindin murhu kenan.  Akwai wata baiwar Allah da ta sanar dani watanni biyu da suka gabata cewa, akwai wani Zaure a Whatsapp da take ciki, ita kadai ce budurwa, duk sauran matan aure ne.  Amma irin zantuka da hotuna da bidiyo da ake rabawa a zauren, a cewarta, baki ba zai iya fadansu ba.  Ba wannan kadai ba, tace hatta hirar mazajensu suna yi; labarai kala-kala.  Da yanayin kwanciyar da aka yi dasu da irin wanda suke so.  Kai, zancen sai wanda yaji.

Duk da cewa da manhajar “Whatsapp” da “Instagram” da kuma “Facebook” duk na kamfanin Facebook ne, amma ga alama manhajar Whatsapp tana rage ma sauran biyun tagomashi, wajen yawan jama’a da yawan masu hawa.  Meye dalili?  Saboda “Sirri”, kamar yadda samari da ‘yan mata ke fada.  Wannan sirri da suke kira, idan ka duba duk za ka ga akwai shi a Instagram da Facebook Chat Application ma, to amma a ma’anance suna nufin saukin mu’amala ne, wajen karban hotuna da bidiyo.  In ba haka ba, ai kashi 90 cikin 100 na mutanenmu na amfani da wadannan manhajoji ne ta wayar salula.  Tabbas in an kwatanta da Facebook, Whatsapp yafi sirri, domin idan kayi rubutu a shafinka a facebook duk abokanka na iya gani har suyi tsokaci.  Haka zaurukan Facebook ma suke. To amma in haka ne, bai ma kamata a kwatanta biyun ba wajen sirri, domin ba yanayinsu daya ba.  Wannan sharhi ni ne kawai nake yinsa, amma su a wajensu sun gane abin da suke nufi.

Galibin abin da yafi yaduwa a wayoyin salularmu musamman matasa shi ne hotuna da bidiyo na batsa.  Ina maimaita wannan zance ne saboda tabbaci; halin da muka samu kanmu a ciki kenan.  Akwai zaurukan addini da yawa, birjik, amma abin da mutane ke yi ta bayan fage yana warware abin da suke fada ko tutiyar koyi dashi a zaurukan da suke ciki na addini ne.

- Adv -

Kamar yadda ake da matan aure da zawarawa masu yada tsiya a Whatsapp, haka ake da samari da ‘yan mata (maza da mata) da matasa maza masu aure, kai har da tsoffi masu yada ashararanci ta manhajar Whatsapp.  Domin galibin zaurukan dake Whatsapp, asalinsu daga Facebook ne.  Haka ma galibin kawancen dake tsakanin jama’a a Whatsapp, duk asalinsa daga Facebook ne.  Bayan haka, da yawa cikin masu amfani da manhajar Whatsapp suna amfani da Facebook ne kawai wajen neman abokan hira a Whatsapp, ta hanyar karbar lambobin wayarsu da suke amfani da ita wajen Whatsapp din.  Sauran bayani kuma sai an hadu a can.

Darasi:

Yawan sabo da irin wannan dabi’a na kai mutum ga halaka.  Kuma mummunar sakamakonsa na iya hassada fitina a tsakanin mai yi da abokan zamansa.  Allah tsare mu baki daya, amin.

BABAN SADIK

18.03.2016 – 4:35pm

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.