Fasahar AI: Tsarin “Artificial Intelligence” a Fagen Na’ura Mai Fasaha (Robot)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 28 ga watan Agusta, 2020.

639

Dan Adam, Ko Na’ura Mai Fasaha?

Ganin wannan ci gaba babu kakkautawa da ake samu a fagen kere-kere da kimiyyar fasahar sadarwa yasa wasu suka fara tunanin, “Anya, nan gaba kuwa na’urori masu fasaha (AI Robots) baza su maye gurbin dan adam a masana’antu da shagunan saye da sayarwa ba kuwa?”  Wannan tambaya ce babban taron Kungiyar Masana’antu da Kere-Kere na duniya mai suna: “Global Manufacturing and Industrialization Summit” (GMIS2020) yayi nazari kansa don samun hakikanin makomar dan adam a masana’antu da shagunan da ake amfanin da na’urori masu sarrafa kansu, saboda dabi’un dan adam da aka girka musu.  Wannan taro dai ya gudana ne a ranar 28 ga watan Yuli da ya gataba, a birnin Hannover dake kasar Jamus.  Masana daga manyan kamfanonin kere-kere da binciken kimiyya da fasahar sadarwa ne suka tofa albarkacin bakinsu kan wannan al’amari.  Taron ya gano abubuwa biyar masu mahimmanci kan wannan maudu’i.

Abu na farko shi ne, amfani da fasahar “AI” cikin ayyukan kamfanoni da masana’antu zai taimaka wajen sawwake ayyuka ne, da kuma kara habbaka kokarin mutanen dake aiki a masana’antun. Hakan zai taimaka wajen rage ayyuka masu maimaituwa da kuma samar da kariya ga ma’aikata.  Domin akwai wasu ayyuka a masana’antu masu hadari ga lafiyar mutane, idan aka yi amfani da na’urori masu fasaha (AI Robots) wajen gudanar da wadannan ayyukan, wannan zai zama kariya ga ma’aikata kuma ya dada inganta aikin.

Abu na biyu da taron ya lura dashi shi ne, kashi 60 cikin 100 na kamfanoni da masana’antun dake amfani da na’urori masu fasaha suna yin hakan ne wajen karfafa ma’aikatansu da rage musu aiki, ba wai sun samar da tsarin ne don korar ma’aikata ba.  Domin abu ne sananne cewa, akwai abubuwa da dama na fahimta da tunani, wanda har yanzu idan ba dan adam ba, babu wata na’ura da za ta iya yinsu.  Musamman abin da ya shafi sanin ya-kamata, kamar yadda bahaushe ke fada.

Abu na uku, taron ya tabbatar da cewa, ta la’akari da kudurar wadannan na’urori masu fasaha, amfanin samar dasu shi ne don su yi wa dan adam hidima, ba wai su maye gurbinsa ba.  Wannan shi ne abin da shugaban bangaren fasaha da kere-kere na kamfanin BMW Group, Mista Mattias Schindler ya tabbatar a wajen taron.  Schindler ya tabbatar da cewa dole ne kamfanoni su san kima da kudurar kowanne; Tsakanin na’ura mai fasaha da kuma dan adam da ya samar da ita.  Nau’in aikin da yafi kamata da dacewa da na’ura mai fasaha – saboda hadarin dake tattare dashi – a gabatar da ita tayi.  Wannan kuma dan adam ne yafi cancanta ya aiwatar, dan adam yayi.

Abu na hudu mai mahimmanci da taron ya tabbatar shi ne, hadakar na’urori masu fasaha da kudurar dan adam a masana’antu, shi ke samar da mafi ingancin sakamako wajen kere-kere.  Domin da yawa daga cikin wadannan na’urori dole ne dan adam ya sarrafa su.  Idan kuma inda su ne kadai ke yanke hukunci, saboda dacewar yanayinsu da yanayin aikin, sai suyi.  Wannan zai sa a samu ingancin aiki a dukkan bangarorin ayyukan kamfani ko masana’anta.

Abu na biyar kuma na karshe da taron ya lura dashi shi ne, masana’antu da dama sun yi amfani da na’ura mai fasaha a ma’aikatunsu a lokacin da ma’aikata ke halin zaman gida sanadiyyar cutar korona.  Kamar yadda yake sananne, tun daga watan Fabrairu na wannan shekara galibin kasashe suka saka dokar hana fita.  Galibin masana’antu da kamfanoni duk sun rufe, sai kadan.  Wadanda suka ci gaba da gudanar da ayyuka saboda yanayinsu, galibi sunyi amfani da wadannan na’urori masu fasaha ne wajen gudanar da wasu ayyuka.  Misali, wasu kamfanoni sunyi amfani da na’ura mai fasaha wajen gwajin dumin jikin ma’aikata yayin da suka zo shiga ma’aikatar.  Wasu sunyi amfani dasu wajen gano ingancin tsare-tsare da bayanai.  Wasu sunyi amfani dasu wajen gano kusancin dake tsakanin ma’aikata, saboda tabbatar da nisantar juna don kada a kamu da cuta, da dai sauransu.

- Adv -

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, a tabbace yake cewa lallai wannan fasaha ta “Artificial Intelligence” ko “AI”, za ta ci gaba da yaduwa a duniya, kuma kamfanoni da masana’antu za su ci gaba da mallakar na’urori masu dauke da wannan fasaha, don sawwake ayyuka da ci gabansu.  Sannan a bangaren fasahar sadarwa kuma, kayayyakin sadarwar da muke dasu za su kara zama masu “hankali”, masu “tunani”, masu iya “kirdado” ko “hasashe” kuma masu karfin hadda wajen taskance abubuwan da muke yi akansu.  Wannan dama ce, amma tana iya zama matsala a gare mu, saboda dalilan tsaro.  Shi yasa ma, a halin yanzu masana a wannan fanni na “Artificial Intelligence” suke yi wa kansu wasu tambayoyi guda uku da har yanzu, basu samu amsarsu ba, watakila sai nan gaba.

Tambayar farko ita ce: “Shin, na’urori masu fasaha, wadanda aka girka musu dabi’u da wasu daga cikin halayyar dan adam, suna iya warware dukkan matsalar dan adam don sawwake masa rayuwa?”  Amsar, a yanzu dai, ita ce: “A a”.

Tambaya ta biyu, suka ce: “Shin, ta la’akari da aka samar dasu, ire-iren wadannan na’urori masu fasaha suna da hatsari. Don basu san ya kamata ba.  Basu san adalci ba.  Basu san tausayi ba.  Basu san kunya da kara ba.  Basu san hakuri da juriya irin ta dabi’a ba.  Shin, ta wace hanya za a iya kintsa musu ire-iren wadannan kebantanttun siffofi da dabi’u?”  Har yanzu babu amsa kan haka, sai dai abin da Allah Yayi nan gaba.

Tambaya ta uku kuma ta karshe, suka ce: “Shin, idan nan gaba aka iya cusa wa wadannan na’urori wadancan kebantattun dabi’u na dan adam – tausayi, kunya, kara, adalci, sanin ya-kamata – zai iya yiwuwa a samar musu da hakkoki su ma, kamar yadda kowane dan adam ke da hakki a dokokin duniya a yau?”  Amsar, kamar tambayar da ta gabace ta, bata samu ba.  Watakila sai nan gaba.

A karshe dai, da yawa cikin masu karatun wannan Makala zasu ga abin kamar almara, ko wani yunkuri na karar da dan adam a bayan kasa.  Ba haka lamarin yake ba.  Dole ne mu dauki ire-iren wadannan abubuwa a matsayin wani abu ne na hakika, wanda ko ba-dade-ko-ba-jima, yana iya riskarmu kai tsaye, kuma har yayi tasiri a rayuwarmu.  In kuwa haka ne, to abin da ya rage mana a yanzu shi ne kokarin fahimtar wannan tsari, da karantarsa, da kuma kwarewa a fannin, don gano hanyoyin da tasirinsa zai iya zama alfamu gare mu, mu karfafe shi, ko wanda zai iya zama tsantsar cutarwa ga al’ada da addininmu, don mu kauce masa.

Dole ne mu fahimci yaren zamani, don mu’amala da mazauna cikinta.

- Adv -

You might also like
3 Comments
  1. Mustapha Sunusi Tahir says

    Slm baban sadik barka da warhaka naka sance mai bibiyar mukalarka kusan nakaranta su dayawa ina maka fatan alkairi bissalam, sunan mustapha Sunusi Tahir daga Kano state

    1. Baban Sadik says

      Wa alaikums salam, barka da Mustapha. Allah amfanar damu baki daya. Na gode matuka.

  2. Nasiru Yahaya says

    Assalamu alaika, Baban Sadik sunana Nasiru Yahaya, mutumin Kano ne ni mazaunin Abuja, Bwari area Council, gaskiya ina jin dadin karanta makalolinka domin suna matukar karamin sanayya akan abubuwa da yawa bisa wannan dalilin ya sa nima na ke yawan gawa mutane adireshinka na yanar Gizo don su ma su karu.
    Daga cikin makalolinka da na karanta kuma su ke taimaka min matuka su ne wanda ka yi a kan dabarun neman bayanai a internet, a bisa wannan kadai ma kawai ina yi maka kyakykyawan fata da kuma yi maka addu’ar samun nasara a rayuwa. 08034265344.

Leave A Reply

Your email address will not be published.