Fasahar 5G: Illolin Da Ake Hasashensu Daga Siginar 5G (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 4 ga watan Disamba, 2020.

274

Illar Makamashin Hasken Sadarwa Mai Guba (Ionizing Radiation)

Daga cikin illoli da ake ta cecekuce a kansu kuma ake jita-jitar wannan fasahar sadarwa za ta kawo cikin al’umma, akwai illar dake tattare da makamashin hasken sadarwa dake cikin magadisun lantarki.  Abin da wannan zance ke nufi a warware shi ne, wayar salula, sanadiyyar sadarwa da take aiwatarwa tsakaninta da na’urar yada yanayin sadarwa (Antenna ko Cell Tower), tana fitar da wasu sinadaran haske masu dumi, wadanda asali daman su ne ke dauke da bayanan da mai waya ke karba ko aikawa, a yanayin sauti ko bayanai na bidiyo ko hotuna, idan ta hanyar Intanet ne.

Wannan makamashin haske mai dumi dai shi ake kira: “Radiation”.  Kuma yana gudanuwa ne a duk inda haske yake a duniya.  Hasken dake bayyana a mahallinmu na dauke dashi.  Hasken rana na dauke dashi.  Hasken wutar lantarki na dauke dashi. Hasken makamashin X-Ray, wanda ake amfani dashi wajen gano cututtuka a kasusuwan jikin dan adam, yana dauke dashi.  Hasken na’urar dafa abinci mai suna: “Microwave”, ko “Oven”, tana dauke dashi.  Haka ma hasken na’urar hada makamashin nukiliya, wato: “Nuclear Reactor”, ita ma tana dauke dashi.  A takaice dai, dukkan wani abin da ke dauke a bayan kasan nan, muddin sinadarin haske na riskarsa, to, dole yana dauke da wannan makamashin “Radiation”.  Sai dai kuma, kafin mu kutsa da bayani kan shin, da gaske ne wannan fasaha ta 5G tana dauke da illolin da suka shafi wannan guba na makamashin hasken sadarwa, zai dace mu san zuwa kashi ne nawa ne makamashin haske ya karkasu, kuma a wani zango suke gudanuwa?

Darajoji da Nau’ukan Haske

Wannan makamashin haske dai ya kasu gida biyar ne, kuma yana gudanuwa ne a wani zango da Allah ya tanada a wannan duniya tamu mai dauke da tsarin gudu da maimaituwa wajen kokarin isar da bayanai cikin haske, wanda a kimiyyance ake kira: “Electromagnetic Wavelength.”  Dangane da daraja da nau’i, makamashin haske a wannan zango dai ya kasu zuwa kashi biyar ne, ko shida.  Wannan rabe-rabe ya ta’allaka ne da yanayin kima, da launi, da bayyana – ana iya gani ko a a  –  da kuma tsarin da suke samuwa.

A zangon farko akwai nau’in haske mai dumi na lantarki mai takaitaccen maimaituwa, amma mai cin dogon zango idan aka yi amfani da shi wajen aikawa da sako na sauti.  Wannan shi ake kira Radio Waves, kuma da shi ne ake iya aikawa da shirye-shiryen gidajen rediyo da talabijin – musamman a zangon “AM” da “FM” da sauransu.   A wannan zango ne har wa yau wayoyin salula suke aiki, wajen aiwatar da sadarwa a tsakaninsu da juna ko da sauran kayayyakin sadarwa.  Duk harkar Intanet, da rediyo, da talabijin, duk a wannan zango suke gudanuwa.  Tsarin hasken dake wannan zango dai, har yanzu babu wani bincike tabbatacce da ya nuna cewa yana cutarwa.

- Adv -

Sai nau’in haske mai biye masa a zango na biyu, wato tsarin haske mai tattare da dumi, mai taimakawa wajen dafe-dafe.  Da wannan tsari ake amfani wajen tsara na’urar dumama abinci da sauran kayayyakin makulashe, wato Microwaves.  Da kuma shi ne har wa yau, ake amfani wajen gina na’urar hangen nesa da ke dukkan filayen jirgin sama, wato Radars.  Yana daukan dogon zango, amma yana da takaitaccen maimaituwa.

Sai kuma nau’in haske na uku, wanda haske ne dake tattare da dumi da kuma launi, amma da shi da sauran tsarin hasken da suka gabata, dan Adam ba ya iya ganinsu da idonsa;  kasa suke da ganinsa; sai dai kawai ya ji duminsu, iya kusancin dake tsakaninsa da inda suke samuwa.  Wannan shi ne tsarin hasken da ake kira “Infra-red Light”, kuma ana amfani da shi wajen yin abubuwa da dama, ciki har da aikawa da sakonni a tsakanin kayayyakin sadarwa na zamani.  Har wa yau, da nau’in hasken Infra-red ne na’urar rimot (Remote control) na talabijin ko kwamfuta, take aiki.

Sai tsarin haske na gaba, wanda ya kunshi shahararrun launuka bakwai masu bayyana a yanayin Bakan Gizo, wato “Rainbow” (Red, Orange, Blue, Yellow, Green, Indigo & Violet).  Wannan nau’in haske shi ne hakikanin haske da muke samu daga rana amma wanda ke riskarmu a wannan duniya da muke ciki; tataccen haske kenan, wato Visible Light.  Wannan har wa yau shi ne nau’in hasken da ya keto sararin samaniya, har muke amfana da shi.  Daga cikin nau’in wannan haske har wa yau akwai hasken kwan lantarki dake gudanuwa a gidaje ko shagunanmu.  Abin da wannan ke nufi shi ne, makamashin hasken da kwan lantarki ke bazawa a mahallin da yake, ya ninka makamashin hasken da wayar salula ke fitarwa idan ana amfani da ita, ninki ba ninki. Ba a ma hada su.

Bayan wannan sai kuma nau’in haske mai tsanani dake samuwa daga rana; gundarin hasken kenan, wanda ke fitowa kai tsaye daga ranar.  Ba halittar da ke iya jure masa.  Wannan shi ake kira “Ultraviolet Light”, kuma yana da saurin maimaituwa wajen isa ga abin da ya hasko, mai cin gajeren zango.  Idan ya fito daga rana, akwai dabaka-dabaka da Allah Yai masa a sararin samaniya da ke tace shi, ya takaita mana haske da zafinsa zuwa nau’in hasken da muke iya rayuwa cikinsa.

Sai kuma hasken na’urar bincike ko hango cututtuka da ke jikin dan Adam ko halittu, wato X-Ray Light.  Wannan nau’in haske ne da e cin gajeren zango, mai saurin maimaituwa don ya darkake duk abin da aka haska shi gareshi.  Da shi ake hasko illolin da ke damunmu galibi a asibitocinmu; da shi ake hango jarirai da lura da halin da suke ciki a mahaifa.  Duk inda kaga na’urar “X-Ray” (X-Ray Machine), tana dauke ne da nau’in makamashin haske mai suna: “X-Ray Light.”

Sai zango na karshe, mai dauke da nau’in hasken dake iya dafa sinadaran makamashin nukiliya.  Wannan shi ake kira: “Gamma Rays.”  Wannan nau’in haske dai yana dauke ne da tarin makamashin da dan adam bai iya jure gani ko darsuwansa a fatar jikinsa.  Saboda masifaffen zafin da yake dauke dashi, da kuma tasirin zafin wajen mummunar illa ga rayuwar dan adam da mahalli baki daya.

Wadannan, a takaice, su ne tsarin gudun haske da maimaituwansa da muke mu’amala da su a sararin wannan duniya da muke ciki.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.