Fasahar ChatGPT na farko da aka ƙaddamar ita ce zubi na 3.5 – ChatGPT 3.5 – cikin watan Nuwamba, 2022 kamar yadda bayani ya gabata a sama. - Jaridar AMINIYA, Jumma'a, 26 ga watan Janairu, 2024.
Fasahar samar da bayanai na AI tana iya ƙirƙirowa tare da kwaikwayon muryar mutane kala-kala. Kana iya ɗaukan muryarka a waya ko a makirfon, ka loda mata, ka samar da rubutu, kuma ta karanto maka rubutun da muryarka cikin sauƙi, kai tsaye.…
Bayan samuwar wannan fasaha a gine cikin na’urori da hanyoyin sadarwar zamani, a halin yanzu manyan kamfanonin sadarwar zamani sun ƙirƙira tare da gina manhaja ta musamman dake iya fahimtar umarnin da za ka bata – rubutu ne, ko hoto ko…