Sakonnin Masu Karatu (2020) (10)

Dalilin Da Ke Sa Wayoyi Su Nuna "Invalid IMEI" Bayan Restore

An guba wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 18 ga watan Satumba, 2020.

246

Assalamu alaikum Abban Sadiq, barka da wannan lokaci.  Tambayata ita ce: me yasa idan akayi restoring din wasu wayoyin suke nuna Invalid IMEI number? Daga Ibrahim A. Idris Jos

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ibrahim, da fatan kana lafiya.  Da farko dai, Kalmar “IMEI” na nufin: “International Mobile Equipment Identity” ne, wato: lamba ce ta musamman, wanda babu wata wayar salula mai dauke da irinsu.  Kamar dai zanen yatsun hannu ne.  Duk wayar da ba ta dauke da wadannan lambobi, to, ana daukanta a matsayin jabu ce, wacce ba ingantacciya ba.  Kuma idan waya ta shiga wannan yanayi, to, ba za ka iya aiwatar da kira ko amsa kira ba, sannan ba za ka iya aikawa ko karban sakonnin tes ba.  Kuma a daidai inda sunan kamfanin wayarka yake, ba abin da za ka gani sai: “Invalid IMEI”.  Akwai dalilai guda biyu zuwa uku manya, dake sa wayar salula ta rika nuna cewa lambobinta na IMEI ba ingantattu bane.

Dalili na farko shi ne, idan ya zama wayar sace ta aka yi.  Idan aka sace wayar salula, kuma mai wayar ya kai kara wajen hukuma, kuma – ta hanyar jami’an tsaro – suka nemi kamfanin wayar ya la’anta wayar, nan take zai mata tambari a kanta, tunda suna iya ganin wayar a na’urorinsu na sadarwa.  Idan suka yi hakan, to, duk sadda aka kunna wayar, ba za iya aiwatar da sadarwa da kowane irin yanayin sadarwa na kamfanin wayar salula ba.  Wannan tsari shi ake kira: “Blacklisting”.

Dalili na biyu shi ne, idan ya zama asalin masarrafar wayar (Processor) – idan nau’in Android ce – ya samu matsala; ko dai wajen sanadiyyar hakan ne yasa aka farke wayar (ta hanyar Rooting ko Resetting), ko kuma wajen aiwatar da aikin ne aka samu matsala.  A yanayi irin wannan, wayar na iya birkicewa, wasu daga cikin bayanan dake da alaka da wadannan lambobi ko tsarin gano yanayin sadarwar wayar salula (Network Identification Settings) su samu gurbace (Corrupted).  Hakan zai sa ta rasa gane kanta, balle gano inda yanayin sadarwa yake.

Dalili na uku mahimmi shi ne, a ka’ida idan aka tashi filashin din wayar salula, daga cikin manyan sharuddan dake sa a samu sakamako mai inganci shi ne a cire katin SIM din wayar, kafin ayi filashin.  Idan aka mance, ko cikin jahilci, aka yi wa wayar salula filashin dauke da katin SIM a jikinta, wannan na iya gurbata bayanan dake dauke da wadannan lambobi na IMEI.  Sakamakon hakan kuma sai ta fara nuna wannan sako dake nuna tsarinta na gano yanayin sadarwa ya gurbace.

Ana iya magance wannan matsala ta hanyar amfani da manhajojin kyauta dake cibiyar manhaja ta Play Store. Akwai manyan manhajoji guda biyu da za a iya amfani dasu wajen yin hakan.  Manhaja ta farko ita ce: “MTK Engineering Mode.”  Kana iya saukar da ita kai tsaye a kan wayarka idan kana amfani da waya mai nau’in Android ce.  Domin dukkan wayoyin salula na Android, suna amfani da masarrafar “Android MTK” ce, wacce ke sarrafa dukkan umarnin da mai waya ke bai wa wayar nan take.  In kuma ka kasa gane nau’in masarrafar wayar, duk ba matsala.  Kana iya amfani da manhajar “Chamelphone”.  Wannan manhaja za ta taimaka maka wajen gyara matsalar da ta samu wayar, sannan ta lakkana wa wayarka sababbin lambobin IMEI, cikin sauki.

- Adv -

Ta yiwu sadda ka tashi yin hakan wayarka ba ta iya aiwatar da komai dake da alaka da yanayin sadarwa.  Kana iya samun wani ya baka tsarin sadarwar Intanet ta hanyar “Hotspot”, wanda tsarin samun siginar Intanet ne a wayar salula ba tare da amfani da tsarin yanayin wayar salula ba.  Idan ya jona maka wayarka sai kawai ka saukar da manhajar ka gyara.  Kasancewar wannan shafi ne takaitacce, bazan iya maka cikakken bayani filla-filla ba.  Amma kana iya samun wani ya taimaka maka wajen yin hakan, ko kai wajen mai gyara, a gyara maka.  Ba abu bane da ya kamata ya ci kudi da yawa.

Wannan shi ne dan gajeren bayanin da zan iya yi.  Ina fatan ka gamsu.

Asslamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki? Allah ya kara maka basira.  Ka taimaka mini da cikakken tarihinka, da irin karatun da kayi kana dalibi.  Domin rubutun da kake yi a AMINIYA abin akwai zurfin ilhama tare da ilmantarwa.  Da fatan samun amsar nake yi ma fatan alkhairi.  Daga Rabi’u M. Minjibir: 08107017451.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Rabi’u.  Da fatan kana cikin koshin lafiya.  Wannan tambaya ce mai fadi, wacce ke bukatar tsawon lokaci ana bayani.  Da kace cikakken tarihina, a gaskiya ba abu bane mai yiwuwa a wannan shafi takaitacce.  Duk da haka, Sunana dai Abdullahi Salihu Abubakar ne, kuma an haifeni ne a garin Garki da ke nan babban birnin tarayya, Abuja.  Shekaruna 44 a halin yanzu.  Asalin kakannina ‘yan garin Sumaila ne dake Jihar Kano, amma da mu da iyayenmu duk a nan Abuja aka haifemu.  Na yi karatun Firamare da Sakandare da Jami’a, duk a nan Abuja.  Digirana na farko a fannin Tattalin Arziki ne, wato: “Economics”.  Sannan na yi digiri na biyu, wato: “Masters” a fannin Hada-hadar Kudi da Bankin Musulunci, wato: “Islamic Banking and Finance”, a cibiyar Hada-hadar Kudi da Bankin Musulunci dake Jami’ar Bayero, a Kano, wato: “International Institute of Islamic Banking and Finance” (IIIBF).

Dangane da ilimin kwamfuta da fannin sadarwar zamani kuma, na tsince shi ne, cikin dacewar Allah, sanadiyyar sha’awa da nake dashi a wannan fannin.  Ba wai makaranta naje na koya ba.  Abin da na koya a jami’a shi ne tattalin arziki da fannin hada-hadar kudade na zamani da na tsarin Musulunci.  Ina da mata da yara.  Kuma ina zaune a Garki dake nan babban birnin tarayya, Abuja.  Don neman Karin hasken han yadda na tsinci wannan ilimi na sadarwa da kwamfuta, akwai Makala guda mai bangarori 4, mai take:  “Rayuwata a Duniyar Sadarwa”, wanda za ka iya samunsa a Taskar Baban Sadik dake: https://babansadik.com/rayuwata-a-duniyar-sadarwa-1/.  Idan ka gama karanta wannan Makala, a kasa za ka ci karo da kashi na 2, haka na 3, har zuwa na 4.

Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.