Kimiyyar Sandar Gora Wajen Kera Kekuna

Hikimar dan adam ba ta taba karewa. Ga yadda wasu bayin Allah ke amfani da sandar bishir gora, don kere kwarangwal din keken hawa a Africa. Wannan ke nuna irin basirar da Allah yayi wa dan adam.

255

A kullum kwakwalwar dan Adam kara fadi take yi, iya gwargwadon kalubalen da yake cin karo da su a tafarkin rayuwa.  Wannan dabi’a na cikin tsarin halittar da ta bambanta dan Adam da sauran dabbobi.  Cikin itatuwan da Allah ya hore mana akwai itaciyar gora, wacce ke yin sanduna masu tsawo, da karfi, da kuma tsawon rayuwa.  Wannan nau’i na bishiya da galibi ke rayuwa a wuraren da ruwa ke gudanuwa da’iman a duniya, na cikin bishiyoyin da muke da su a kasashen Afirka tun fil azal.  To amma saboda rashin ci gaban tattalin arziki da kimiyyar zamani, a galibin wurare hura wuta ake yi da sanduwan wannan bishiya, ko yin dannin gidaje da su, ko yin rufin gidaje da su, da sauran abubuwa.  Wannan a gargajiyance kenan.

A halin yanzu mai karatu zai yi mamakin jin cewa sandunan itacen gora sun zaman kayan gabas, inda aka wayi gari ana sarrafa su don yin kwarangwal din kekunan zamani a wasu daga cikin kasashen duniya, har da kasashen Afirka a yau.  Wannan sabuwar fasahar kere-kere da ke bayar da daman amfani da sandunan gora ta samu karbuwa sosai a halin yanzu. Domin ana kera kwarangwal (wato Frame) na dukkan nau’ukan kekunan zamani, irinsu kekunan hawa na shakatawa, da kekunan tseren motsa jiki, wato Racing Bicycles, da kekunan yara, da na manya, da nau’ukan kekunan gajiyayyu ko nakasassu, da dai sauransu. Bangarorin da wannan sabuwar fasaha ta kunsa dai su ne: sandan mazauni ko siddin keken, wato Seat Tube, da dokin keken, wanda ke hada sandan siddi da sandan da ke rike da hannun keken, wato Top Tube.  Sai kuma sandan yatsun keken, wanda ke dauke da yatsun da ke rike da tayar gaba, wato Head Tube.  Bayan wadannan bangarori, har wa yau akwai yatsun da ke rike da tayar gaba, wato Fork, da sandar da ke hada marikin kan keke da mazaunin kaca daga can kasa kenan.

- Adv -

A bangare baya kuma, akwai sandar da ke hada mazaunin siddi (wato Seat Tube) da sandar yatsun da ke rike da tayar baya, wato Seat Stays.  Sai bangaren karshe, wato sandar yatsun kafar baya, wanda a turance ake kira Chain Stays.  Wannan sanda mai rike da yatsun tayar baya, tare da mahadar mazaunin siddi da sandar da ta hada kan keken a sama, su ne ke rike da injinan da ke juya kacan keken baki dayansu.  Dukkan wadannan bangarori da bayaninsu ya gabata, da gyararrun sandunan gora ake yinsu.  Ba su kadai ba ma, hatta murfin kacan keken, wato kurumbo, da kuma siddin keken, duk da wannan makamashi na sandunan gora ake yinsu.  Yadda ake sarrafa wadannan sanduna kuwa shi ne, bayan an ciro su, an feke su tsaf, sai a kankare su, a shafe su da wasu sinadarai, sannan a dumama su a wuta, don kara musu juriya da hana su karyewa.  Bayan haka, sai a yanka su zuwa iya tsawon da ake bukata don hada kwarangwal din keken.  Duk inda mahadi tsakanin sanda da sanda ya zo, sai a yabe mahadin ko inda za a jona sandunan biyu (misali, mahadin mazaunin siddi, da mahadin kurumbo inda injinan kaca suke, da kuma mahadin kan keken, wanda ke saman yatsun marikin tayar gaba da na baya) da bawon itaciyar ganyen wiwi, wato Hemp Fiber.  Wannan bawo na itaciyar tabar wiwi tana da matukar karfi, da jure wahala. Wannan yabe shi ne ke tsayawa a matsayin walda.

A wasu lokuta kuma akan yi amfani da bawon sinadarin kabon (wato Carbon Fiber), don wannan yabe a matsayin walda.  Cikin wani shiri na musamman da tashar BBC World Satellite Channel ke yi a duk shekara mai suna World Challenge, wanda shiri ne na musamman kan sababbin hanyoyin kere-kere a duniya, an sanya wannan sabuwar fasaha a sahun sauran hanyoyin kere-kere masu tasiri da kayatarwa a duniya a shekarar 2010.

A halin yanzu dai ana kera ire-iren wadannan kekuna ta amfani da wannan sabuwar fasahar sandar gora a kasar Indonesiya, domin suna noma wannan itaciya sosai.  Bayan haka, akwai kasashen Afrika guda uku da ke da arzikin wannan itaciya ta gora, kuma an samu wani kamfani da ya bude wata masana’anta inda ake ta kera ire-iren wadannan kekuna.  Wadannan kasashe dai su ne: kasar Zambiya, da kasar Senegal, da kuma kasar Suwaziland.  Kamfanin Calfee Design, wanda ya assasa kamfanin kera wadannan kekuna a kasashen Afirka ya bayar da tabbaci kan ingancin abin da yake kerawa, inda yake bayar da garanti na tsawon shekaru goma bayan saye.  A halin yanzu dai kasuwar kekunan hawa masu kwarangwal din sandar gora ta bude a wadannan kasashe, domin bayan ‘yan kasa da suke saye suna hawa don shakatawa ko zuwa gonakinsu, ana kuma fitar da su zuwa kasashe irinsu Faransa da sauran kasashen Turai.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.