Tasirin Dakatar da Shafin “Twitter” a Najeriya

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 11 ga watan Yuni, 2021.

288

Ranar Laraba, 2 ga watan Yuni ne kamfanin Twitter ta cire wani bangare na sakon mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari – inda yake gargadi ga masu baraza ga hadewar kasar nan a matsayin al’umma daya, da su daina ko kuma su fuskanci fushin hukuma – da cewa sakon ya saba wa ka’idojin da dandalin ya tanada wajen yada sakonni.  Sakamakon haka aka rufe shafin Shugaban kasa har na tsawon sa’o’i 12.  Kwanaki biyu bayan faruwar wannan lamari, sai gwamnatin tarayya, ta hanyar Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ta ba da sanarwar dakatar da amfani da wannan dandali na Twitter a Najeriya gaba daya.  Wannan ya faru ne ranar Jumma’a, 4 ga watan Yuni.  Daga nan hukuma ta umarci dukkan kamfanonin wayar salula da dakile kafar dake baiwa masu wayoyin salula damar isa ga dandali ko manhajar Twitter.  Tun daga wannan rana, idan ba masu amfani da hanyar “Virtual Private Network” (VPN) ba, babu mai iya amfani da manhaja ko shafin Twitter a Najeriya.

Faruwar wannan lamari dai ya haifar da cecekuce a tsakanin jama’a, musamman masana a harkar sadarwa da shari’a da kuma hakkin jama’a wajen fadin albarkacin baki.  Haka kungiyoyin kasashen waje da dama sunyi korafi kan wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka.  Haka ma hukumar Twitter ta nuna rashin jin dadinta da yadda abin ya kasance, ta kuma yi alkawarin cewa nan kadan za ta nemo hanyar warware wannan matsala.  A nata bangare, cikin sanarwa na karshe da ta fitar, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa akwai tattaunawa dake gudana tsakanin bangarorin biyu.  Ta kuma kara jaddada cewa wannan mataki da ta dauka ba shi da alaka na kai tsaye da cire sakon Shugaban Kasa da dandalin yayi, illa don ganin yadda kamfanin bai gushe ba yana bai wa masu kokarin hargitsa hadin kan wannan kasa goyon baya, musamman a zanga-zangar “#ENDSARS” da ya gudana a shekarar da ta gabata.  Sai dai kuma, mene ne tasirin wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka ga al’ummar kasar baki daya?

A bangare daya, ta la’akari da sharhin galibin wadanda ke wajen Najeriya musamman, wannan mataki zai jawo galibin kamfanonin sadarwa na zamani masu yunkurin zuba jari a Najeriya, su fasa.  Wannan kuma ba karamin nakasa bane ga tattalin arzikin kasarmu, musamman a cikin halin da kasar ciki yanzu.  Bayan haka, hatta masu zuba jari a wasu bangarorin zasu ji tsoron shigowa saboda tsoron rashin ‘yancin fadin albarkacin baki.  Musamman ganin cewa tuni gwamnatin tarayya ta kafa hukuma da zata daidaita tsarin alaka tsakanin gwamnati da kafofin sada zumunta mai suna: “National Council on Information” (NCI), tare da umartan kafofin sadarwa irin su Zoom, da Netflix, da Skype, da Whatsapp, da suyi rajista da hukumar Yaba Labaru ta Kasa (National Broadcasting Commission) kafin ci gaba da gudanar da harkokinsu a Najeriya.  Wannan mataki, a cewar masharhanta, wata dabara ce ta kayyade hakkin fadin albarkacin baki.  Kuma wannan zai sa masu zuba jari su kaura zuwa kasashe makota ko su tsorata da shigowa Najeriya ma.  Domin hatta kamfanin Twitter da ya tashi bude ofishi a Afirka bai zo Najeriya ba, sai ya bude a kasar Gana.  Wannan kamar wani hannunka mai sanda ne, biyo bayan abin da ya faru lokacin zanga-zangar “#ENDSARS” da ya gudana.

- Adv -

Har wa yau, kamfanin Twitter zai ci gaba da hasarar kudaden tallace-tallace da yake samu daga kamfanonin Najeriya, musamman bankuna, da masana’antu da sauransu.  A halin yanzu akwai masu amfani da dandalin kusan miliyan 40 a Najeriya.  Wannan adadi ya dara adadin masu amfani da shafin a kasar Amurka, wanda bai shige miliyan 38 ba.  Haka wadanda ke amfani da shafin don tallata sana’ar da suke yi ko ayyukan da suke gudanarwa ta wannan kafa, su ma sun rasa wannan dama kenan.  Sannan galibin bankuna da kafafen talabijin na tauraron dan adam, suna amfani da Twitter wajen ta’ammali da abokan huldarsu, musamman wadanda ke da korafi tsakaninsu da kamfanin.  Yanzu duk wadannan damammaki sun rasa su kenan.  Haka galibin masu amfani da Twitter wajen karanta labarai musamman kan Najeriya, wannan damar ta tafi.

A daya bangaren kuma, yunkurin gwanatin tarayya wajen daidaita sahun kafafenn sada zumunta na iya haifar da tsari da natsuwa cikin yadda mutane ke gudanar da rayuwarsu a wadannan kafafe.  A tare da cewa ita kanta hukuma ta san cewa kulle wadannan kafafe gaba daya ba shi ne zai samar da waraka ba, musamman ta la’akari da yadda duniya ta hade a tsarin sadarwa.  Ba wai Najeriya kadai ba, hatta a kasashen Turai an san cewa akwai matsala wajen yadda wadannan kafafe ke tantance abubuwan da jama’a ke zubawa a kansu.  A kasar Amurka misali, majalisar tarayyar kasar (Congress) ta sha kiran shubagannin wadannan kafafe a lokuta daban-daban, da nuna musu illolin dake cikin tsare-tsaren manhajarsu.  Haka tarayyar Turai ta sha lafta ma wasunsu tara na kudade masu dimbin yawa, sanadiyyar taka dokar nahiyar.  A kasar Indiya yanzu haka akwai takaddama tsakaninka da kamfanin Twitter.  Kasashe irin su Thailand misali, sun sha rufe kafar YouTube sanadiyyar al’amura masu alaka da siyasa da dokar kasa.  Cikin watan da ya gabata (Mayu, 2021), jihar Florida dake kasar Amurka ta samar da doka da zai rika lafta wa kafafen sada zumunta tara na musamman, idan suka cire, ko suka dakatar da wani dan siyasar jihar daga kafarsu, kan abin da bai taka kara ya karya ba.  Akwai kasashen turai da dama, irin su Jamus, da ke da dokar umartar kowace kafar sadarwa ce ta cire wani sakon da kasar ke ganin ya keta haddinta ko dokar kasarta, daga dandalin, sannan da hukunta duk wanda ya dora sakon.

Wannan ke nuna cewa lallai akwai abubuwan nazari dangane da yadda wadannan kafafe ke gudanar da al’amuransu.  Kuma tattaunawa tsakanin hukumomin kasashe don samar da matsaya kan tsarin gudanar kafafen, shi ne zai taimaka wajen warware ire-iren wadannan matsaloli.  Don haka, wannan takaddama da a halin yanzu ake yi tsakanin gwamnati tarayya da kamfanin Twitter, idan ya kai ga daidaita fahimta da samun matsaya tabbatacce, zai taimaka wajen kawo tsari kan yadda ‘yan Najeriya zasu ci gaba da amfani da wannan dandali ba tare da matsala ba.

Dandalin Twitter dai ya yi kaurin suna wajen cirewa ko gogewa ko kora ko dakatar da shafuka da sakonnin da aka dora su, sanadiyyar saba abin da yake kira ka’idojin gudanarwar kamfanin.  An kafa kamfanin ne a shekarar 2006, kuma zuwa wannan shekara (2021) yana da masu rajista miliyan 350 a duniya.  A duk yini mutane sama da miliyan 190 ne ke hawa dandalin.  Dangane da abin da ya shafi kora ko dakatarwa, kamfanin ya kori ko dakatar da shafukan mutane sama da 216 shahararru a duniya, ciki har da tsohon shugaban kasar Amurka, wato: Donald Trump, da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kafafen yada labaru irin su The New York Times, da Aljazeera Arabic.  Bayan Najeriya, daga cikin kasashen da suka (taba) toshe dandalin Twitter dai akwai kasar Sin (China), da Koriya ta Arewa (North Korea), da Iran, da Masar (Egypt) a 2011, da Turkiyya (Turkey) a 2014, da Turkmenistan, da Burtaniya (2011).

- Adv -

You might also like
3 Comments
  1. HAMISU says

    ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI.

  2. Izzuddin ShehuManzo says

    Allah Yasaka Baban Sadik Allah Yakara Basira, Mungode Da Fadakarwa

    1. Baban Sadik says

      Ni ke da godiya. Allah saka da alheri. Aci gaba da kasancewa tare damu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.