Hira da BBC Hausa kan Bikin Ranar Tsaftace Intanet a Duniya (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 21 ga watan Fabrairu, 2020.

185

Na biyu kuma shi ne, yana da kyau su waye abokanansu.  Sanin abokanansu na da mahimmanci domin yanzu galibin abota ana yinta ne ta hanyar kafofin sada zumunta na Intanet, wato “Social Media”.  Ka ga a nan, da wanda ka sani, da wanda ma baka sani ba, da wanda kuke kasa daya da wanda ma ba kasa daya kuke duk a nan ake haduwa.  Don haka, yana da kyay iyaye su san da su waye ‘ya’yansu ke mu’amala kuma wasu wurare ne ko shafuka suke mu’amala dasu.  Kuma kamar yadda na fada a baya, hakan zai iya yiwuwa ne ta hanyar duba wayoyinsu lokaci-lokaci.  Idan kwamfuta suke dashi ana iya karbar kwamfutar a rika dubawa.  Sannan akwai hanyoyin kariya – domin riga-kafi ya fi magani. Idan waya ce za a baiwa yaro kuma an san akwai hanyoyin da aka san zai iya amfani dasu wadanda sun saba wa al’ada (da addini) ko kuma zai iya cutuwa daga gare su, to, ana iya toshe wadannan hanyoyin gabanin a bashi wayar.  Ko kuma idan uba ko uwa Masani ne akan harkar sadarwa, su tanadi wata hanya da zasu rika bibiyar ma’amalar da dansu yake yi. Misali, idan waya ce yake da ita, suna iya sanin lambobin sirrin shiga wayar (Passcord).  Idan kwamfuta ce, su san kalmar sirrin shiga kwamfutar (Password).  Haka ma idan yaron yana akwatin Imel, su san kalmar sirrin akwatin Imel din.  Wannan zai taimaka wajen sanin wasu irin mu’amaloli ne yara ke gudanarwa a wannan mahalli ta amfani da wadannan na’urorin sadarwa.

Abu na uku shi ne, a rika zama da yara ana tattaunawa dasu don kokarin tantance wasu irin amfanoni ne suke samu wajen ma’amala da wannan fasaha ta Intanet.  Sannan wasu shafuka suke shiga don samun wadannan amfanoni?  Idan an gano shafuka ne ko wurare ne da basu dace ba, sai a basu shawarwari kan haka.  Wato yaro yana da wani abu guda daya.  Idan yasan yana ma’amala da wasu abubuwa munana a wayarsa, yana da wahala a iya ganewa, musamman idan yasan cewa muddin aka gano abin da yake yi, za a horar dashi horo mai tsanani.  Hakan kuma zai faru ne idan ba a jawo shi a jika ba.  Amma idan yasan an sake dashi, an jawo shi a jika ana hira dashi, to zai iya fadin gaskiya.  To, idan aka san yaro bazai fadi gaskiya ba don irin wannan dalilin, hanya mafi sauki ita ce a rika bincikar wayarsa a lokacin da ba ya zato.

Wadannan kadan ne daga cikin hanyoyin.

BBC Hausa:  Ta la’akari da cewa yawancin wadanda ke mu’amala da fasahar Intanet matasa ne, wasu ma ‘yan kasa da shekaru 18, ko akwai bukatar samar da wata doka da za ta iyakance wuraren da zasu rika ziyarta a Intanet?

- Adv -

Baban Sadik:  A gaskiya batun samar da wata doka don takura yanayin ma’amalar mutane a Intanet, abu ne da hatta a kasashen da suka ci gaba bai cika samar da wata fa’ida dari-bisa-dari ba, balle a ce a kasa ko mahalli irin Najeriya, inda ba a cika dabbaka doka ba.  Hakan zai fito fili idan muka yi la’akari da cewa hatta dokokin da muke dasu ma a kasa ba wani dabbaka su ake yi ba sosai.  Sannan na biyu, mahallin Intanet ya sha bamban da zahirin rayuwa.  Kama mutumin da yayi laifi ta amfani da wayarsa (ko kwamfuta) ko wasu shafuka da ya shiga wadanda watakila ma ba a Najeriya asalinsu yake ba, abu ne mai tsauri matuka.

Ni a ganina, maimakon ayi ta kokari ko yunkurin ganin cewa an sake samar da wasu dokoki, musamman ganin cewa akwai doka da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya rattafa wa hannu a shekarar 2015 wacce ke hana ta’ammali da haramtattun bayanai ko kutse a kwamfutoci ko shafukan gwamnati, ga kuma kuduri na musamman dake gaban majalisar dattawa da aka tsara don yaki da kalaman batanci a kafafen sada zumunta, me zai hana ayi ta wayar da kan jama’a tukunna?  Domin wadannan dokokin ko an samar dasu, muddin ba a lura tare da dabbaka su ga duk wanda ya taka su, zasu zamo jeka-na-yika ne kawai.  Kamar yadda ka sani, muna da dokoki sun fi dari a Najeriya, amma ba a dabbaka su, idan ba wani ake son a kama ba don wata manufa ta siyasa.

Ni na fi ganin, in har samar da wata doka za ta samar da fa’ida, to wayar da kan jama’a ya samu a farko tukunna.  Domin idan mutum yasan hadarin abu, to, bazai afka masa ba, kuma idan ma ya afka masa, to, ya san cewa idan aka kama shi ba za a raga masa ba.  Wannan shi ne abin da yake da mahimmanci.  A yawaita wayar da kan matasa, a ilmantar dasu sosai.  Akwai hukumomin gwamnati irin su hukumar yada bayanai da al’adu ta kasa (Ministry of Information and Culture) da hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (National Orientation Agency); yana da kyau su yawaita wayar da kan jama’a musamman iyaye.  A kuma rika shirya laccoci don bayyana sakamakon munanan wadannan hanyoyi dake Intanet.  Da miyagun sakamakon aiwatar da kutse (Hacking) da aiwatar da zamba-cikin-aminci (Internet Scam), misali.  Idan hukuma ta dage kullum ana wayar da kan jama’a kan wadannan abubuwan, to, daga baya idan an samar da doka mutum yasan cewa idan ya aikata, ga abin da ke jiransa na hukunci.

Sannan wannan mahalli na Intanet fa, mahalli ne da yake bako ga galibin ‘yan Najeriya har yanzu.  Da yawa cikin mutane musamman a arewacin Najeriya sun dauka Dandalin Facebook ko manhajar Whatsapp su ne fasahar Intanet din.  Wallahi sai kana tattaunawa da mutane za ka gane da yawa cikinsu basu ma san meye Intanet din ba.  Shin, Intanet din nan, mece ce ita?  Wasu sun dauka fasahar Intanet fa wata na’ura ce kamar akwatin Talabijin da za kaje kasuwa ka sayo ka ajiye a dakinka kana kamo duk tashar da kake son gani.  Basu dauka cewa shafuka ne na bayanai da za ka iya mu’amala da su a wayar salula ko kwamfuta ba. Har yanzu da yawa ba a ma san mece ce Intanet din nan ba.  To, ka ga a yayin da ya zama ita kanta fasahar Intanet din an jahilce ta, samar da doka ba zai samar da wata fa’ida ba sai an wayar da kan jama’a tukun.  In kuwa ba haka ba, zai zama wani sabon hanyar kashe kudi ne.  Don haka, a wayar da kan jama’a.  A wayar da kan jama’a.  A wayar da kan jama’a.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.