Fasahar AI: Tsarin “Artificial Intelligence” a Fagen Kere-Kere

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 21 ga watan Agusta, 2020.

412

Fasahar “AI” a Fagen Kere-Kere

Bayan fagen sadarwa da kwamfuta, wannan tsari na “Artificial Intelligence” ya fara maye fannin kere-kere.  Mafi shahara daga cikin na’urorin da aka girka wa wannan fasaha dai ita ce na’urar mutum-mutumi, wato: “Robot”.  Wannan na’ura dai an kera ta ne a siffa da surar dan adam, ko wasu halittu; suna motsi, suna daukan kaya, suna karban kaya, suna aika sako kuma suna karban sako, suna tafiya, suna hawa kuma suna sauka.  A manyan kamfanoni kera motoci ko injina ko jiragen sama, wadannan na’urori na mutum-mutumi suna da girma.  Galibi ma cikin surar babban inji ko wani abin daukan kaya aka yi su, ba a surar dan adam ba.  A manyan shagunan sayar da kayayyaki kuma dake galibin kasashen da suka ci gaba, an kera ire-iren wadannan na’urori ne a siffa da surar dan adam, ko wasu halittu masu ban sha’awa.  Wannan ita ce siffarsu ta asali.  Kuma ana amfani da inji ne wajen sarrafa ayyukansu.

Na’ura Mai Fasaha (AI Robot)

Amma a halin yanzu da bayyanar wannan fasaha ta “AI”, an kintsa musu tunani da dabi’un dan adam, don basu damar gudanar da ayyukan da suke yi ba tare da wata inji dake jujjuya su ba.  Kawai sai dai su rika amfani da ka’ida da dabi’un da aka girka musu cikin kwakwalwarsu.  Na’urori masu wannan siffa da dabi’a su ake kira: “AI Robots” ko “AI Powered Robots” – wato “Na’ura mai fasaha” kenan. A fagen likitanci ma an samu ci gaba a wannan fanni sosai.  Na’ura mai fasaha ta farko da ta fara aiwatar da aikin tiyata a jikin wata halitta a duniya ita ce wacce aka kera a shekarar 2012.  An wakilta wannan na’ura ce don dinke cikin wata dabba da aka bude saboda wata cuta dake damunta a tumbinta.  Nan take ta dinke wurin sarai.  Masana suka ce ta dinke wurin da kyau, fiye da yadda dan adam ke dinke ciwo a jikin mara lafiya.

- Adv -

Daga bayyanar wannan cuta ta “COVID-19”, an samu karuwar kamfanoni da shaguna masu amfani da ire-iren wadannan na’urori masu fasaha don sawwake ayyuka da kara tabbatar da kariya.  Misali, a wani kantin cin abinci dake kasar Jafan, idan ka ba da odar abin da za a kawo maka na abinci, da zarar an gama hadawa, irin wannan na’urar ce za ta dauko abincin, tiryan-tiryan, ta kawo maka inda kake zaune, ta ajiye maka a kan tebur, sannan ta juya ta tafi.  Idan wani ma ya bukata, haka za a masa.  An tanade ta ne don tabbatar da kariya daga kamuwa da cutar korona.  A shagunan sayar da kayayyakin masarufi kuwa, ana amfani dasu wajen dauko kayayyaki masu nauyi, ko taimaka wa masu sayan kaya daukan abin da suka saya wurin da suka dauko su zuwa inda za su biya kudi, kafin su wuce.  Wannan kadan ne cikin dubunnan misalai da ake dasu a aikace, a warwatse a sanannin duniya.

Mota Mai Tuka Kanta (Driverless Car)

Bayan wadannan na’urori masu fasaha, wannan fanni na “AI” ya sawwake hanyar samar da motoci masu tuka kansu, ba tare da direba ba.  Sai dai ka shiga ka tayar da ita, ka zauna kana kallon ikon Allah; za ta kaika inda kake.  Wannan nau’in mota ita ake kira: “Driverless Car” – mota mai tuka kanta, ba wai mota mara direba ba.  Wannan nau’in mota, duk da cewa har yanzu ana ta gwaji ne kansu, amma akwai wadanda suka fara amfani dasu a wasu kebantattun wurare.  Kamfanin Tesla, babban kamfanin kera motoci da na’urorin zamani dake kasar Amurka, wanda shahararren mai kudin nan dan kasar Afirka ta Kudu mai suna Elon Musk ya mallaka, tuni ya fara kera motoci masu tuka kansu.  Bayan kamfanin Tesla, kamfanin Google ma, wanda muke amfani da manhajarsa wajen neman bayanai, shi ma tuni yayi nisa wajen kera mota mai tuka kanta.

Wannan nau’in mota dai ana dora mata dabi’un dan adam ne, wajen fahimtar titi, da masu tsallaka titi, da tazarar da za ta iya baiwa motar dake gaba da ita ko baya da ita, da yanayin mahalli, da yadda za ta dakata idan tazo bakin danja, da yadda itan danja ta ba da hannu, za ta iya ganewa kuma taci gaba da tafiya, da yadda za ta iya sarrafa kanta idan tazo shataletale (Roundabout), duk yawan motocin dake wurin kuwa.  Tirkashi!  Wani aikin sai ilimi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.