Facebook Gidan Rudu: Kowa “Malam” Ne

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

237

Kowa “Malam” Ne

Daga cikin rudu mafi girma dake dandalin Facebook, wanda fahimtarsa kan zama da wahala idan ba wanda ke kusa da abin ba, akwai da’awar malanta da galibin mutane ke yi, wanda ko kadan, idan aka same su a zahirin rayuwa sai a ga abin ba haka yake ba. Bayan wadannan kuma, akwai masu kururuta inuwar wasu, da cewa su ne kadai malamai, idan ba su ba, kowa jahili ne. Suna hakan ne da zimmar yada shaharar malaminsu, ko don su baiwa wasu haushi, ko kuma su boye nakasarsa bayyananniya ga wadanda ke kusa dashi amma suka saba masa.

Kasancewar a Dandalin facebook rubutu ake karantawa, ko hotuna ake iya gani, ko bidiyo, yasa wasu kanyi amfani da wannan kafa don hada cuwa-cuwa a fagen ilimin addini. Amma mun mance duk wadannan hanyoyin ana iya jirkita su. Ni har yanzu ban ga wani shafi ko wani zaure inda jama’a ke ta jayayya da juna a wani fanni na ilimi irin su Likitanci ko Injiniyanci ko Sadarwar zamani ko Kere-kere ba. Idan kaji muna kururuwa da tinkahon ilimi, to na addini ne, ko fagen siyasa, wanda har yanzu bamu iya shi ba. Daga cikin matsaloli mafi girma akwai masu zagin malamai na Allah, wadanda sun shahara da ilimi, don kawai su cinma wata manufarsu. Alhali su ko digon “ba” basu ajiye da sunan littafi don amfanin al’ummar musulmi ba.

Na hangi wani ya makala hoton daya daga cikin malaman kungiyoyin addini, na bangarensa, yana ta yabonsa, amma da baitukan wake wadanda Al-Mutanabbi ya rubuta don yabon wani Sarki. Abin mamaki, me ya hanashi kirkirar baitukansa daga kwakwalwarsa? A Facebook ne za ka ga mutane na rubutu suna aibanta kansu, da sunan yabo. A Facebook ne za ka ga mutane suna rubutu suna aibanta gwanayensu na bogi, da sunan yabo. Kuma abin mamaki, ana samun masu yarda har yanzu. Meye dalili?

Babbar matsalar ita ce, gane waye malami ta kafar Facebook abu ne mai wahala, muddin ba sanin mutum kayi a zahirin rayuwa ba. Don me? Saboda akwai da yawa cikin mutane dake zuwa shafukan ilimin addini a Intanet, su kwaso rubutu, su kwaso kasidu, su kwaso makaloli na ilimi, su kwaso baituka na wake, su kwaso shirgin littattafai, su zuba a shafinsu, duk da sunan su suka rubuta. Abin mamaki ma wasu ko iya jirkita bayanan ba su iyawa. Wannan “wankiya ne” kuma shi ne abin da ake kira “Satar fasaha,” wato: “Copyright Infringement” ko “Copyright Theft,” a takaice. Hatta a musulunci wannan haramun ne. Don me za ka siffata kanka da abin da baka cancance shi ba? Akwai wanda na ganshi WALLAHI, wani ya titsiyeshi a “inbox” ya rarakoshi da tambaya mai zafi, wallahi sai da yaje ya kwaso rubutun wani malaminsu tukun, ko jirkitawa bai yi ba, ya aiko masa. Da aka sake danno masa wata tambayar sai yace ayi hakuri yana cin abinci. Amsar da bai bayar ba kenan har yau.

- Adv -

Darasi:

1. Ka sani, ilimin addini kogi ne, ba ka iya kaiwa karshensa. In kuwa haka ne, ka tsaya matsayinka, kada ka kai kanka inda Allah bai kaika ba;

2. Yawan jayayya da musu mara kan-gado ba naka bane, a addini. Duk zafin kanka, duk karatunka, duk jajircewarka, WALLAHI baka kai ba, kuma ba za ka iya kai magabata ba. Me ka tanada wa al’ummar Manzon Allah, na fa’ida a addini ko a rayuwa? Al-Imam Ahmad bin Ali, Bin Hajar, shekaru 5 ya dauka yana rubuta mukaddimar littafin “Fat’hul Baaree” kadai, wato “Hadyus Saaree.” Sannan ya dauki shekaru 25 yana rubuta littafin “Fat’hul Baaree.” Ina Abu ‘Umar, Ibn Abdul-barr, An-Numari, wanda yayi wa littafin Muwadda sharhi har mujalladi 25, yasa masa suna: “At-Tamheed, Limaa Fil Muwadda Minal Ma’aanee wal Asaaneed.” Za ka iya wannan? Ko ka kai matsayin Ibnul Atheer, wanda ya rubuta littafin “An-Nihaaya Fee Ghareebil Hadeeth Wal Athar”? Ya rubuta littafin ne a kurkuku, sadda yake zaman kaso. Ina kake da Imaamu Maalik, wanda bayan ya rubuta littafin Muwadda, sai da hamshakan Malamai wajen 70 suka duba suka tabbatar sannan ya fitar? Kai wanda ka rubuta, malamai nawa suka duba littafin, in ma ka rubuta din? Ina kake da Ibnul Qayyim Al-Jawziyya, wanda ya rubuta littafin “Zaadul Ma’aad Fee Hadyi Khairil Ibaad,” da ka? Ina su Imam Az-Zahabi, marubucin littafin “Siyaru A’alaamun Nubala,” mujalladi sama da 30. Sannan ga littafin “Taareekhul Islam” mai mujalladi sama da 40?

Ina kake da Imamu Ahmad bin Hambal, wanda ya haddace hadisan Manzon Allah (SAW) sama da miliyan daya, sannan ya rubuta littafin “Al-Musnad” mai mujalladi wajen 30 mai tahqiqi? Kokarinka ya kai na malaman hadisi masu binciken halayyan maruwaita hadisai, wato: “Rijaal”? Ina Imam An-Nawawi, wanda shekarunsa gaba daya a duniya basu shige 46 ba, amma abin da ya rubuta na ilimi, idan aka ce mu kwafa kadai, da biro da takarda, ko da kwamfuta ma, ba alkalami da tawada ba, sai mu kusan kwashe shekarunsa bamu gama ba. Ina Imam At-Tahaawee, marubucin littafin “Sharhu Mushkilil Aathaar,” da littafin “Sharhu Ma’aanil Aathaar,” wanda idan ka hada su kadai, sun kai mujalladi 55? Ina kake da Ahmad bin Abdil-Haleem, bin Taimiyyah, Al-Harraanee, wanda fatawowinsa kadai wajen mujalladi 30 ne? Kai fatawowinka mujalladi nawa ne, idan ma an tara su?
Wai don Allah me kayi wa Musulunci ne da Musulmi, a wannan zamanin da kake da kwamfuta da biro mai sarrafa kansa, da sauran kayan aikin rubutu? Ba komai? Sai jayayya? Tir da rayuwar mai dabi’a irin wannan!

BABAN SADIK
19.02.2016 – 10:40AM

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.