Fasahar 5G: Jita-Jita da Karerayi Kan 5G (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 18 ga watan Disamba, 2020.

694

Jita-Jita kan Fasahar 5G

Duk sadda aka samu wata sabuwar fasaha ta ci gaban rayuwa, to, tabbas sai an samu jita-jita dake biye da ita. Wannan al’ada ce ta rayuwa. Wannan fasaha ta 5G ma, kamar sauran nau’ukan fasahohin sadarwa na zaman da wadanda suka gabace su, an samu jita-jita dake ta yaduwa kan cutarwar da ake cewa fasahar na dauke dashi. Wanda idan aka dabbaka wannan fasaha, a cewar masu wannan jita-jita, to, nan gaba za a samu yaduwar cututtuka cikin al’umma. Saboda yawaitan makamashin hasken sadarwa mai guba, wato: “Ionizing Radiation”, kamar yadda nayi ishara gare shi a bayanin da ya gabata. Sai kuma wasu dalilai marasa kan gado, wadanda asalinsu ko dai manufofi ne na kasuwanci, ko siyasa, ko kuma siyasar diflomasiyya.

Wadannan jita-jita dai sun kasu kashi biyu ne. Akwai wadanda ke da kamshin gaskiya a cikinsu, wadanda kuma aka gudanar da bincike (kuma ake ci gaba da yi) don gano samuwar tasiri ko rashinsa, ko kuma gaskiyar abin da ake fada. Sannan akwai jita-jitar da tsagwaron karya ce. Hankali da tunani na lafiyayyen mutum bazai dauka ba. Bari mu fara da nau’in jita-jitan dake dauke da kamshin gaskiya:

Jita-Jita Mai Kamshin Gaskiya

Yaduwar jita-jita kan hasashen illolin fasahar 5G dai ya faro ne tun shekaru biyu da suka gabata. Sadda aka samu masu adawa da wannan fasaha da ake kira da suna: “Anti-5G Group”, suka fara yada cewa wannan fasaha na dauke ne da mummunar illa ga lafiyar dan adam da mahalli. Nan take ire-iren wadannan bayanai suka watsu kamar wutar daji a Intanet, musamman shafukan sada zumunta – Facebook, da Twitter, da Instagram, da Youtube. Ganin kimar masu yada wannan jita-jita yasa wasu daga cikin shugabanni da ‘yan siyasa a manyan kasashen Turai da ma kasar Amurka, suka fara shakka kan inganci da dacewar wannan fasaha a cikin al’umma. Wannan jita-jita ya jawo cecekuce sosai.

William Board daya ne daga cikin marubuta a jaridar The New York Times na kasar Amurka. A cikin makalarsa da ya rubuta a shekarar 2019, ya nakalto cewa tashar talabijin din Amurka mai suna: “RT America” ce ta fara yada shirye-shirye masu alakanta fasahar 5G da cututtuka irin su cutar sankara ta kwakwalwa (Brain Cancer), da rashin haihuwa, da cutar rashin daidaituwar tunani (Autism), da kumburin zuciya (Heart tumor) da sauransu. Yace tashar ta fara watsa wadannan shirye-shirye ne a shekarar 2018, wanda ya zuwa shekarar 2019 kadai ta yi shirye-shirye wajen bakwai. Duk a kan wannan maudu’i. Wadannan shirye-shirye ne suka watsu zuwa shafukan Intanet, musamman shafukan Mudawwanai da na sadar da zumunta. Amma, a cewar marubucin, dukkan wadannan zantuka ba su da wani tushe a kimiyyance, balle makama.

- Adv -

Bayan haka, a shekarar 2019 dai har wa yau, sai wani gungun malaman kimiyya su 180 daga kasashe 30 suka rubuta wa hukumar tarayyar Turai (European Union) wasika ta musamman don umartanta da dakatar da yunkurinta na dabbaka wannan sabuwar fasaha ta 5G, saboda hasashen cututtukan da fasahar za ta iya haifarwa a nahiyar, a cewarsu. A cikin watan Afrailu na shekarar kuma, hukumar babbar birnin Brussels dake kasar Belguim ta dakatar da wani gwaji na fasahar 5G da wani kamfani ya nemi gudanarwa, don saba wa dokokin da suka danganci makamashin hasken sadarwa. Haka ma a kasar Suwizaland an hana gudanar da gwaji makamancin wannan, saboda irin wancan dalili. Hujjar hukumar sadarwa ta kasar ita ce, har zuwa wancan lokaci, babu wani bincike da ya nuna cewa wannan fasaha ta 5G ba za haifar da wata cutarwa ga lafiyar jama’a ba.

Haka abin ya faru a kasar Nedaland (Holland), inda ‘yan majalisar kasar suka yi kira ga gwamnati a wancan lokaci, cewa dole ne tayi nazari mai zurfi kafin gwajin wannan fasaha. A kasar Amurka kuwa, ‘yan majalisar kasar, wato: “Congress” sun rubuta wa hukumar sadarwa ta kasar Amurka, wato: “Federal Communications Commission” (FCC), inda suke nuna mata damuwarsu kan hasashen illolin da ake tunanin aiwatar da wannan fasaha zai haifar. Cikin wannan lokaci dai har wa yau, hukumar birnin Mill Valley dake jihar Kalfoniya na kasar Amurka ta hana yunkurin da wani kamfani yayi na kafa turakun na’urar yada yanayin sadarwar fasahar 5G. Haka abin ya kasance a jihar Vermont da New Hampshire na kasar Amurka, duk da yunkurin kwantar da hankali da hukumar Abinci da Magunguna na kasar, wato: “Food and Drug Administration”, ta ci gaba da yi, cewa har yanzu babu wani abu a cikin tsarin dokar hukuma kan na’urorin sadarwa, dake barazana lafiyar al’ummar kasar.
Bayan kungiyoyi masu adawa da fasahar 5G a kasar Burtaniya sun ta gudanar da kamfe kan wannan lamari, an samu kananan gundumomi irin su: Totnes, da Brighton, da Hove, da Glanstonbury, da kuma Frome sun ci gaba da samar da dokoki masu tsauri don hana gudanar da gwaji ko dabbaka wannan sabuwar fasaha ta 5G a gundumominsu. Wannan ke nuna yadda wannan jita-jita ya yadu kuma yayi tasiri kenan.

Mafi shahara daga cikin wadanda ke adawa da dabbaka wannan tsari na fasahar 5G sun hada da Dr. Davies da kuma Dr. Sasha. Dr. Davies dai wata masaniyar kimiyya ce dake kasar Amurka. Mai bincike ne sosai kuma ta yi suna wajen shugabanni. Domin tana daya daga cikin mataimakan tsohon Shugaba Bill Clinton na kasar Amurka, a matsayin mai bashi shawara kan harkokin da suka danganci lafiya. Shi kuma Dr. Sasha wani kwararre ne a fannin kimiyyar Fiziya, kuma dan kasar Burtaniya ne. Yana cikin wadanda suka ta shirya tarurruka don ‘wayar da kan’ jama’a kan abin da ya kira: “hadarin dake tattare da wannan fasaha ta 5G.”

A nata bangare, Dr. Davies tace tabbas akwai alaka mai karfi tsakanin cututtuka irin su karancin maniyyi ga maza, wanda ke haddasa karancin haihuwa, da kuma makamashin hasken rediyo mai cutarwa (ionizing radiation), wanda kuma wayoyin salula ke yadawa a yayin da ake amfani dasu, ko wanda na’urorin “Wi-Fi” ke fitarwa yayin da ake amfani dasu wajen karban siginar Intanet a makarantu, da asibitoci, da filayen jiragen sama, da bas-bas dake manyan birane, da gidajen jama’a da wuraren tarurruka ko shagunan sayar da kayayyaki. Daga cikin cututtukan da Dr. Davies tace suna da sila mai karfi da wannan fasaha ta 5G dai akwai cutar rashin bacci, da cutar karancin tuno abubuwa, da cutar karancin haddace abubuwa, da cutar karancin fahimtar yanayi, da kuma cutar sankara ta kwakwalwa (Brain cancer). Shi kuma Dr. Sasha ya kara da cewa, wannan fasaha ta 5G na iya haddasa cutar karancin natsuwa ga yara (Autism), ko yaduwarsa.

Zantukan wadannan masana dai sun yadu sosai a Intanet, a tsarin bidiyo, ko sauti, ko kuma rubutattun bayanai da wasu suka rubuta, ko wadanda suka rubuta aka ta yadawa. Kuma hakan yayi tasiri wajen jefa tsoro a zukatan jama’a, musamman ma shugabannin siyasa a galibin kasashen duniya, ciki har da Najeriya. Inda aka ta cecekuce hatta a Majalisar kasa ta Najeriya, da umartan gwannatin tararraya ta dakatar da wannan tsari har sai an samu tabbacin gaskiya ko rashin gaskiyar dake tattare da wadannan zantuka. Wannan yasa aka ta kokarin aiwatar da gwaje-gwaje don kokarin gano gaskiyar wadannan jita-jita.

Wannan kan jita-jitar dake da kamshin gaskiya kenan.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.