Fasahar 5G: Madaukan Titin Sadarwar 5G

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 31 ga watan Yuli, 2020.

175

Babban Titin Sadarwa (High-Band 5G)

Wannan shi ne nau’in titin sadarwa na kololuwa, a tsarin fasahar “5G”, kuma shi ne na karshe. Wannan titin sadarwa na gudanuwa ne a zangon sadarwa dake matakin Giga Hertz 25 zuwa 39. Tirkashi! Babban goro sai magogin karshe. A duk gwaje-gwajen da aka yi kan fasahar “5G” a duniya, har yanzu ba a fara aiwatar da sadarwa a wannan titi ba, a aikace. Galibin abubuwan al’ajabi da mamaki a fagen sadarwar fasahar “5G”, duk suna wannan marhala ne ko titi.

A takaice dai, wannan titin sadarwa mafi girma na iya karba da aika sakonnin da mizaninsu ya kama daga tiriliyon daya (1GB) zuwa tiriliyon ashirin (20GB) cikin dakika guda. Sannan, kamar sauran nau’ukan titunan sadarwa da bayaninsu ya gabata, wannan titi na da dan karen sauri wajen aikawa ko karban sakonni, ba wai yawan mizanin sakonnin ne kadai ba.
Sai dai da ingancinsa, wannan titi ba shi da kadadar sadarwa mai fadi ko girma. Ma’ana, yana iya karba da aika sakonni masu yawa ne cikin dan gajeren zangon sadarwa. Amma yana iya daukan na’urorin sadarwa masu dimbin yawa, wanda sauran titunan ba su iya dauka. Sannan yana iya aiwatar da sadarwa tsakanin wadannan na’urori, a iya zangon da suke, cikin gaggawa kuma da inganci. Shi yasa ake amfani da zangon sadarwa masu yawa a wuri guda, don taimakawa wajen aiwatar da sadarwa ga dimbin masu amfani da na’urorin sadarwa a inda suke.

A aikace, wannan tsarin fasahar “5G” ana amfani dashi a wuraren da ke da cunkoson jama’a dake son aiwatar da sadarwa a tsakaninsu da juna ko tsakaninsu da wasu na’urorin sadarwa dake wasu wurare daban. Misali, a manyan birane masu dimbin jama’a. Ko manyan kasuwanni masu cunkoson jama’a. Ko filayen saukan jirgin sama masu girma da ake dasu a duniya. Ko filayen wasanni musamman na kwallon kafa. Ko manyan dakunan taro inda dubunnan jama’a ke taruwa a lokaci guda, kuma suke da bukatar da aiwatar da sadarwa. A ire-iren wadannan wurare dai babu tsarin da yafi dacewa dasu illa Babban titin sadarwa na fasahar “5G”, wato: “High-band 5G”.

Daga cikin dalilan da suka sa ake girke eriyan sadarwa masu yawa a dan gajeren wurin da wannan tsari ke gudanuwa shi ne, don tsarin ba ya iya huda wasu nau’ukan bangon dakuna masu kauri, don shigar da siginar sadarwa. Ko wasu nau’ukan tagogi na zamani. Wannan yasa ake amfani da zangon sadarwa mai dauke da eriyan sadarwa (Cell Tower Antenna), don taimaka ma tsarin.

Ta la’akari da karfin sadarwa da yawan mizanin bayanan da wannan titi ke iya ta’ammali dasu, idan kana bukatar saukar da bidiyo da mizaninsa ya kai 20GB a misali, a tsarin fasahar “5G” karkashin Karamin titin sadarwa, cikin kasa da dakiku 20 ka gama saukar dashi. Duk da cewa hakan zai dogara ne ga karfin yanayin sadarwar kamfanin wayar da kake amfani da layinsu.

- Adv -

Madaukan Titin Sadarwa

Wadannan nau’ukan tituna da bayaninsu ya gabata a sama, suna dauke ne da wasu madaukai – wato abubuwa ko tsarin dake daukan bayanan da ake son aikawa. Misali, kamar babban titi ce, wacce take da fadi ko girma, kuma babbar mota na bi ta kanta. Sabanin sauran tsare-tsaren baya dake dauke da madauki guda a titin sadarwarsu, wannan tsari na fasahar “5G” na dauke ne da madaukai da yawa.

A tsarin fasahar “5G”, kowane titi na amfani da tsarin: “Multi-input and Multi-output” ne, wato: “MIMO”, wanda nayi ishara gareshi a makonni biyu da suka gabata. Wannan tsari ne na sadarwa dake amfani da hanyoyi masu yawa a lokaci guda, wajen dauka da aikawa da sakonni ko karbarsu. Ka dauka kamar babbar titi ce wacce ke dauke da manyan motoci masu dauke da kayayyaki masu dimbin yawa. Wannan kwatankwacin tsarin fasahar “5G” kenan. Su kuma sauran tsarin da suka gabata kamar titi ne babba wanda mota daya rak ke bi, dauke da kaya. Ka ga wancan titin farko za ta fi sauran aikawa da kayayyaki masu yawa a lokaci guda, fiye da titin dake dauke da babbar mota daya rak.

Na’urorin Sadarwa

Galibin jama’a sun dauka tsarin fasahar “5G” ya ta’allaka ne ga wayoyin salula kadai, kamar sauran tsare-tsaren sadarwa da suka gabata. Wannan ba haka yake ba. Bayan wayoyin salula da kamfanonin sadarwar wayar salula na duniya ke kerawa da kuma amfani dasu wajen bai wa mutane damar aiwatar da sadarwa ta siginar rediyo, tsarin fasahar “5G” na da kudurar taimaka wa sauran kayayyaki da na’urorin sadarwa na zamani irin su: motocin zamani masu amfani da makamashin lantarki (Electric cars), da na’urar dumama abinci (Microwaves), da gidajen zamani masu amfani da tsarin sadarwa (Smart Homes), da na’urorin adana bayanai, da kwamfutoci, da na’urorin mu’amala da bayanai, da na’urorin jin sauti ko kallon bayanan bidiyo, da na’urorin daukan hoto na gida da na asibiti, da na’urorin sawwara bayanai da dai dukkan wata na’ura ta zamani da ake amfani da ita a gida, ko ofis, ko makarantu, ko asibiti, ko masana’antu, duk wannan tsarin sadarwa na iya taimaka musu wajen aiwatar da sadarwa ba tare da taimakon wani dan adam ba. Wannan tsari shi ake kira: “The Internet of Things”, ko “IoT” a gajarce.

Kamar yadda na sanar a farkon wadannan kasidu da suke zuwa mana tun farko, ire-iren abubuwan da wannan tsari na sadarwa zai iya gudanarwa a fagen sadarwa abubuwa ne na mamaki wadanda idan ba mutum ya gansu bane a aikace, musamman ga mu da muke wannan bangare na duniya, sai ya dauka zuki-ta-malli ce, ba gaskiya ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.