Facebook Gidan Rudu: “Maigida, Ina Matarka?”

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

452

“Maigida, Ina Matarka?”

Daga cikin abin da yafi tayar da hankali cikin munanan tasirin hanyoyin sada zumunta na zamani sanadiyyar rashin tarbiya, akwai irin matsalar da matanmu na aure, Hausawa musamman suka samu kansu a ciki, musamman a dandalin Facebook. Tabbas akwai matan aure da yawa a Facebook masu mutunci, masu yada ilimi na addini a zauruka da dama, masu nasiha ga ‘yan mata ‘yan bana-bakwai don kar su fada cikin tarkon shedan a wannan dandali. Wannan abu yana burgeni matuka, domin suna rage wa malaman addini aiki ne a zahirin rayuwa musamman a arewacin Najeriya. Ayyukansu na tasiri sosai, domin suna amfani da irin lafazin da ‘yan matan ke iya fahimta ne, cikin sauki kuma. Ina rokon Allah ya kara musu karfin gwiwa, da karin hakuri da juriya, wajen kara inganta wannan aiki nasu mai tasiri.

A daya bangaren kuma, akwai watsattsu, marasa mutunci, wadanda suka fitsara har suka fitsare wasu; tsakanin matan aure da zawarawa. A yau an wayi gari yadda saurayi da buduwa ke kulla alaka ta soyayya, ayi ta abubuwa marasa tsafta, haka matan aure ke kulla alakar soyayya irin na madigo wanda ke farawa tun daga Facebook. Galibi sukan hadu ne a zaurukansu (Groups), inda ake tattaunawa. Akwai kawalai mata masu hada waya. Idan ke Hajiya ce kina son wata mace da za ku rika haduwa kuna soyayya irin ta madigo, akwai mai hadawa, duk ta wadannan zauruka. Abin mamaki shi ne, asalin ire-iren wadannan zauruka an bude su ne don kulla zumunci tsakanin mata; za ka ga sakonni na wa’azi da nasiha, amma a cikin zauren ake samun juna. Daga nan sai a koma Inbox a ta hiran shashanci. Daga nan a rika hira a waya musamman idan maigida ba ya gari. Wata kan yi “chat” har zuwa karfe biyun dare da “masoyiyarta.” Idan abin ya kasaita, suna ziyartar juna, ko da ba gari daya suke ba. A wajen ziyarar ma a kwanta tare, a daki daya, a kan gado daya, ana ta shashanci, musamman idan maigida ba mazaunin gari bane.

Wasu matan auren kuma suna neman ‘yan mata ne, ‘yan makaranta, musamman ‘yan jami’a, su rika shashanci dasu ta kafar Facebook, a karshe a kulla alakar ziyara, musamman lokacin da Uba ke tsammanin ‘yarsa na makaranta. Akwai wacce ta shaku da wata bazawara tun a Facebook, suna gaisawa, aka fara shashanci a Inbox. A karshe dai wannan budurwa ta kai mata ziyara, sai da tayi makonni shida a gidan wannan bazawara mai hali suna shashanci. Akwai matan auren dake abin a waya da Facebook kadai, amma a zahiri ba su haduwa. Akwai wacce ba ta da sana’a sai neman ‘yan mata, kuma matar aure ce. Idan ta samu wacce take so ta kafar Facebook, sai ta bukaci budurwar ta kawo mata ziyara, ita kuma ta kama Otal su kwana suna shashanci. Idan ma ta bukaci abokiyar shashanci amma tace ba ta da kudin mota, tana iya tura mata kudi ta banki, ita dai bukatarta a hadu; kudi ba damuwarta bane. Mijinta ba mazaunin gida bane, a kudu yake aiki ita kuma ya barta nan Arewa da yara.

Akwai matar auren da ta rantse wa abokiyar shashancinta cewa, wallahi tallahi tunda take da mijinta, bata taba sanin meye sha’awa ba, kuma (mijin) ba ya burgeta, ba ta ma sha’awarsa. Bata san dadin sha’awa ba sai da ta hadu da abokiyar shashancinta. Akwai matan auren da saboda shakuwa da irin wannan shashanci ya haddasa musu, idan daya tayi fushi da daya, to, komai na gidanta na iya shiriricewa. Ta gwammace mijinta yayi fushi da ita da ace masoyiyarta ce. Akwai wacce take gaya wa wata kawarta cewa mijinta ya taba kama ta da wata masoyiyarta, a kan gadonta, a dakinta, suna shashanci; a tube zindir dukkansu. Da ya leka ya gansu, sai kawai ya koma falo, yace idan sun gama ta sanar dashi. Da kawar ta tambayeta: “To yaya aka kare?” Sai tace wallahi ba abin da ya faru. Kawai ce masa tayi wai suna gwajin sabbin dinki ne!

- Adv -

Ire-iren wadannan mata asharararru sukan tona asiran mazajensu wajen kwanciya ga kawayensu na shashanci. Akwai wacce da zarar mijinta ya gama saduwa da ita nan take za ta hau Facebook ta sanar da masoyiyarta, da irin tsarin da aka bi wajen aiwatar da abin. Wadannan masu shashanci da mata ‘yan uwansu kenan; ko dai zawarawa ko ‘yan mata ‘yan jami’a ko kuma kawayensu matan aure.
A daya bangaren kuma, akwai matan aure dake haduwa da mazaje ta wadannan kafafe na sadarwa; ko dai tsofaffin samarinsu lokacin samartaka, ko kuma wasu da suka hadu dasu. Sukan kulla alaka dasu sosai, a ta hirar batsa, da aika hotuna, idan abin ya kasaita, akan hadu a waje (Otal ko wani wuri daban) don ya sadu da ita. Wannan shi yafi komai sauki ma, wai cire wando ta ka. Akwai wanda ya hadu da wata matar aure ta Facebook, tana cikin kunci, kamar yadda ta sanar dashi, ba ta son mijinta ko kadan kuma ita tana da karfin sha’awa, shi kuma yakan fita waje shashancinsa. A karshe wannan saurayi wanda ko aure bai taba yi ba, ya gayyaceta wani gida a garin da suke, ya sadu da ita. Akwai wanda duk sadda ya bukaci kwanciya da wata tsohuwar budurwarsa da ke da aure yanzu, bayan shashancin da suke yi ta waya da Facebook, sukan hadu a wani wuri ya sadu da ita. Da aurenta har da yara.

Darasi:

1. Wadannan labarai ne masu tayar da hankali, kuma tabbatattu. Babbar manufar ita ce mu fahimci irin hadari da kuma mummunan tasirin da rashin tarbiyya ke haddasawa ga masu mu’amala da wadannan kafafen sadarwa.

2. Maigida, har wa yau kai nake tambaya: wai ina matarka take?

BABAN SADIK
08.03.2016 – 9:21am

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Abu yusuf sadiq says

    MALAM ALLAH YASA KAMA DA MAFI FICIN GIDA ALJANNAH MADAU KAKIYA AMIN MUNA FASHINTA KWARAI DA GASKE

    1. Baban Sadik says

      Ni ke da godiya. Allah saka da alheri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.