Fasahar “Digital Currency”: Nau’ukan Kudaden “Crypto” (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 14 ga watan Mayu, 2021.

302

Litecoin

An kirkiri kwandalar “Litecoin” ne cikin shekarar 2011, kuma wanda ya samar da ita shi ne: Charlie Lee.  Asalin fasahar dai daga magudanar Bitcoin ne. Don haka, da yaren gina manhaja na “C++” aka gina fasahar.  Ita ce fasahar farko da ta fara amfani da tsarin kariyar bayanai na “Scrypt” wanda ya kunshi amfani da “password”, sabanin fasahar bitcoin dake amfani da “SHA-256d”.  Kuma tana amfani da ka’idar “Proof of Work” (PoW) ne wajen tantance bayanai.  A halin yanzu farashin Litecoin ya kai dalar Amurka dari biyu da doriya ($280.95), wajen naira dubu dari da goma shabiyar kenan.  Tambarin kwandalar Litecoin a kasuwar hada-hadar kudi dai shi ne: “LTC”.

Namecoin

Kwandalar “Namecoin” ita ma dai cikin shekarar 2011 aka kirkireta.  Wanda ya samar da ita kuwa shi ne Vincent Durham.  Fasaha ce mai dauke da tsarin tsaron bayanai nau’in “SHA-256d”, tare da ka’idar tantancewa nau’in “PoW”, kamar na fasahar “Litecoin” kenan.  Farashin namecoin dai ya kai dalar Amurka $2.32, kwatankwacin naira dubu daya kenan da doriya.  Tambarin kwandalar a kasuwar hada-hadar kudade shi ne “NMC”.  Ita ma, kamar kwandalar “Litecoin”, asalin magudanarta daga fasahar Bitcoin ne.

Peercoin

Fasahar “Peercoin” ta samo asali ne a shekarar 2012, kuma Sunny King ne ya kirkirota ta amfani da tsarin tsaron bayanai nau’in “SHA-256d”.  Da yaren gina manhajar kwamfuta na “C++” aka gina wannan magudanar fasahar.  Wannan fasaha ita ce ta farko wajen fara amfani da ka’idojin tantance hada-hadar kudi guda biyu, wato: “Proof of Work” (PoW) da kuma “Proof of Stake” (PoS).  Domin asalin fasahar daga Bitcoin ne.  A halin yanzu farashin peercoin ya kai dalar Amurka $1.22, kwatankwacin naira dari shida da doriya kenan kudin Najeriya.  Tambarin kwandalar a kasuwar hada-hadar kudade shi ne: “PPC”.

Ripple

Fasahar “Ripple”, wadda ta samo asali daga sabuwar magudanar hada-hadar kudi da kamfanin Ethereum ya samar, an kirkirota ne don sawwaka hanyar aikawa da karban basuka a tsakanin mutane biyu masu ta’ammali da fasahar.  Wadanda ya kirkiri wannan fasaha su ne Christ Larsen da Jed McCaleb, a shekarar 2013, kuma sunyi hakan ne ta amfani da yaren gina manhajar kwamfuta na “C++”, kamar sauran wadanda suka gabata.  Sannan aka dora mata tsarin tsaron bayanai mai suna: “Elliptic Curve Digital Signature Algorithm” (ECDA).  A halin yanzu farashin kwandalar Ripple ya kai dalar Amurka $1.55, kwatankwacin naira dari bakwai da ‘yan kai kenan kudin Najeriya.  Tambarin kwandalar shi ne: “XRP”.

- Adv -

Auroracoin

Wannan nau’in kwandala, wacce ke da asali daga fasahar bitcoin, an kirkireta ne a shekarar 2014.  Wanda ya samar da ita shi ne: Baldur Odinsson, dan asalin kasar Iceland, ita ma duk ta amfani da yaren gina manhajar kwamfuta na “C++”.  Ka’idar tantance bayanai da take amfani dashi kuma shi ne: “Proof of Work” (PoW).  Manufar kirkirar kwandalar Auroracoin dai shi ne don ta maye gurbin kudin kasar Iceland, gaba daya.  Babu tabbacin hakan zai yiwu dai zuwa yau.  Farashin auroracoin dai yana kasa da dalar Amurka daya ne ($0.84).  Kwatankwacin kusan naira dari hudu kenan.  Tambarinta a kasuwan hada-hadar kudi shi ne: “AUR”.

Dash

An samar da kwandalar Dash ne a shekarar 2014, ta amfani da yaren gina manhajar kwamfuta na “C++”, da ka’idar tantance bayanai guda biyu, wato: “Proof of Work” (PoW) da kuma “Proof of Stake” (PoS).  Wadanda suka kirkiri wannan fasaha dai su ne: Evean Duffield da Kyle Hagan.  Asalin fasahar dai daga magudanar Bitcoin suka samar dashi.  Kuma ita fasahar farko ake iya amfani da ita wajen tsara kasafin kudi (Budget) da samar da ingantaccen tsarin shugabanci ta hanyar magudanarta.  A halin yanzu farashin kwandalar Dash dai ya kai dalar Amurka $321.56, kwatankwacin naira dubu dari da talatin daya da ‘yan kai kenan, kudin Najeriya.  Tambarinta shi ne: “DASH”.

NEO

Kwandalar NEO dai wadanda ya kirkireta su ne: Da Hangfei da Erik Zhangta amfani da yaren gina manhajar kwamfuta na “C++”, da tsarin kariyar bayanai na musamman mai suna: “dBET”.  Wannan fasaha ce ‘yar kasar Sin (China).  Asalin sunan da aka kirkireta dashi a shekarar 2014 dai shi ne: “Antcoins”, amma daga baya cikin shekarar 2017 aka canza sunan zuwa: “NEO”.  Farashin wannan kwandala dai ya kai dalar Amurka $113.39, kwatankwacin naira dubu arba’in da shida da dari biyar da ‘yan kai, kudin Najeriya. Tambarin NEO dai shi ne: “NEO”.

Ethereum

Wannan ita ce kwandalar dake gasa da bitcoin a kasuwar hada-hadar kudade na duniyar Intanet.   An samar da wannan fasaha ne a shekarar 2015, ta amfani da wani sabon salon gina magudanar fasahar, wanda ya sha bamban da na bitcoin.  Wanda ya kirkiro wannan fasaha dai shi ne: Vitalik Buterin, ta amfani da yaren gina manhajar kwamfuta na “C++” da “Go”, wato yaren gina manhaja na kamfanin Google.  Ka’idar tantance bayanansa dai “Proof of Work” (PoW) ne, kuma farashinsa a yau ya kai dalar Amurka $3,165.81, kwatankwacin naira miliyan daya da dubu dari biyu da ‘yan kai kenan, kudin Najeriya.  Tambarin Ethereum a kasuwar hada-hadar kudade dai shi ne: “ETH”.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.