Yawaitar Motoci Masu Makamashin Lantarki a Duniya: Ina Muka Dosa? (2)

Kasar Sin ta ba da sanarwar daina amfani da motoci masu amfani da makamashin man fetur da dizil a kasarta zuwa shekarar 2040.  A makon jiya mun fara yin nazari kan sakon dake dunkule cikin wannan sanarwa nata, da kasashen da suka yi wanann kuduri kanfinta, da sakamakon hakan ga kudaden shigarmu a Najeriya, sannan a karshe muji bayani kan motoci masu amfani da makamashin lantarki da yanayinsu.  Ga kashi na biyu cikin wannan nazari namu nan.  A sha karatu lafiya.

526

Wannan yunkuri na kasar Sin, wanda shi ne na baya-bayan nan, ya kara jaddada abin da aka dade ana rade-radinsa, na ko dai karewar man fetur din da wasu kabilu a Najeriya suke ta tinkaho dashi, ko kuma yin kwantansa a kasuwar duniya, saboda daina amfani dashi da ake tunanin nan gaba wasu kasashe na iya yi.

Shi yasa a wannan mako da sauran makonni biyu dake tafe, naga dacewar kawo mana wani nazari mai zurfi da Steve Dent yayi, masani kan harkar kere-kere a duniya, kan motoci masu amfani da makamashin lantarki, musamman a kasar Amurka.

A cikin wannan sharhi nashi, wanda na fassara kuma na kawo mana, yayi dogon bayani kan wadannan nau’ukan motoci.  Me yasa kasashe masu arziki ke kokarin neman wani makamashin daban ba fetur da dizil ba?  Shin, yaya ake kera wadannan motoci a fasahance?  Suna da tsada?  In eh, to yaya lura dasu yake kasancewa?  Meye amfaninsu wajen rage dumamar yanayi a duniya ko cikin al’umma?  Duk wadannan tambayoyi, da ma wasu makamantansu, na cikin abin da Steve ya amsa a gamshe, cikin wannan sharhi.

- Adv -

Kasancewar a baya an buga wannan sharhi a wannan shafi, ana iya isa ga kasidun ta adireshin dake kasa:

  1. Me Ka Sani Kan Motoci Masu Amfani da Makamashin Lantarki? (1)
  2. Me Ka Sani Kan Motoci Masu Amfani da Makamashin Lantarki? (2)
  3. Me Ka Sani Kan Motoci Masu Amfani da Makamashin Lantarki? (3)

A sha karatu lafiya.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muhammadu Auwal Umar says

    Allah ya saka da Alkhairi

Leave A Reply

Your email address will not be published.